Kar kace sai kowa yayi Abunda Kai kake iya yi..Kuma Kar ka ce duk Wanda baiyi Abunda Kai kakeyi ba Bazai Samu Tsira ba .


Inji Jagoran Gaskiya -Sheikh Zakzaky (H)

Tun farkon tarihin addinin musulunci, bayan bayyanar Manzo mai tsira da aminci zaka ga cewa haka tarihi din ya gada, akwai wadannan matsaloli guda biyu (Matsalolin cikin da kuma na waje). Akwai matsaloli na wadanda yadda suke kallon Manzo da kuma wadanda su kayi imani da shi ta waje, suna da na su matsaloli daban daban, akwai kuma matsaloli na cikin gida, wadanda suke su kuma suna tsakankanin wadanda sukayi imani din, lafima' ma a zaman Madina, yayin da al'amarin ya fadada ya zama mutane sun shigo daga wurare daban-daban, a Makka ba a samu irin wadannan matsalolin ba, saboda su Muminai din Kalilan ne suna gwagwagwa da mushirikai.
A wannan lokacin ba'a samu wani abu wanda yayi kama da Munafurci ba, sai dai ma a samu wani abu wanda ya ke akasin Munafurci shine mutum yana da lmani ya bayyana akasin hakanan, ya nuna cewa shi ba ma musulmi bane, domin gudun fitina.
Amma yayin da aka zo Madina ya zama anyi ma addinin Musulunci shigan duuu' wasu anfi karfin sune, ba yadda suka iya suka shiga, sannan kuma aka zo 'Amalwufud' mutane su ka zo 'Afuwajan' suka shisshigo, to duk sai suka shigo da matsalolin su. To sai ya zama ainihin an samu matsalolin cikin gida masu yawan gaske wanda yake zama yanzun na waje ma kalilan, ainihin na cikin gidan ne ma yafi yawa wannan kuma har ya zuwa lokacin da Manzo ya bar duniya matsalolin cikin gidan ya bari, sune kuma suka dinga karuwa har suka kai ga Yake-yaken da akayi da rarrabe-rarraben da akayi da kuma Kashe-kashen fahimta da ire-iren su, wanda har aka gadar mana da addinin.
Saboda haka idan dai akwai matsala, muna iya cewa muna da matsalan gado, ko ba a lura ba! Bamu da yadda zamu yi, dama dole ya zama akwai matsala din, saboda ita matsalan gadonta akayi, amma abinda ya kamace mu muyi shine, idan mutum ya fahimci inda ya sa gaba ya ga inda za shi, ga kuma hanyar da zai bi, to ina ganin ya kamata ya zama shi yai ta tafiyar sa ne duk da kuma akwai matsala din, inko har yace to yanzu zai zauna sai ya magance matsala din gaba daya sannan yayi tafiyansa to ba inda zaya, domin ita matsalar ba mai magantuwa ba ce.
Idan da kana da hankali, in ka ga matsalan da baza ta magantu ba, to abinda ya kamata ka manta da ita kawai ka ci gaba da Harkar ka, wato idan ko matsalan mai magantuwa ne, to shikenan ana iya zuwa ayi maganinta sannan ayi gaba.
To wasu matsalolin da al'umma take da shi in mutum ya dube su da kyau zai ga ce matsaloli ne wadanda suke sunyo asali tun farko, kuma anzo mana da su ne, mun gaje su ne, saboda haka in muka ce sai mun warware su to mai yiwuwa ba za muyi tafiyan ba. Amma tunda na farko suma tare da matsalolin sun yi tafiya din, to muma abinda ya kamace mu kenan. To, wato muna da matsalan ganin mutane ga al'amari, kamar yadda yadda jiya nake batun fadi da tsukewa, nayi kokari jiya in nuna mana cewa, babu shakka mutum zai iya yin addini da dan dai-dai abin ya zo masa komai Kankantar sa, ya kuma gama lafiya lau, ya samu tsira gobe kiyama, kamar misalin da na ke bayarwa na wani wanda ke cewa *"WAL ASRI"* ta wadaci al'ummar nan, da wanda aka karanta masa *"IZAZUL"* ya ce to karatun ya ishe shi hakanan, da wanda aka gaya masa *FARILLAI* da *NAFILOLI,* yace shiko ba zaiyi *NAFILOLIN* ba da sauransu, wanda suke duka kuma sun rabauta akan sun aikata abinda suka aikata. Da za ace mutum dan abinda ya zo masa, ya rike shi da *IMANI* da *IKHLASI,* ya kuma aikata abinsa, to Masha Allahu! Saboda za'ayi masa hisabi ne da daidai da gwargwardon iliminsa da Ayyukansa gobe kiyama, za'ayi masa hisabi ne da daidai da abinda ya sani da abinda ya aikata, domin ilimi dama hujja ne ga mutun ko akan shi.
Amma inda matsalan take, shine na inda mutun ya dauki kadan, ya kuma ce kowa ma sai ya dauki kadan, to anan kam' akwai matsala babba, in ka wadatu da dan abinda ya zo maka na ilimi ka aikata shi, to kai ba tsoro gareka ba razani, amma in kace to kowa ma komai yawan yalwan abinda ya sani ya bar wanda ya sani azo ayi wanan (naka), mu kaddara ka san *AHALARI* kuma ka aikata *AHALARIN,* ya wadace ka, ba sai kuma ka ce to duk wanda ya san *MUKTASAR* ya aje *MUKTASAR* din *AHALARI* ne yanzu ba za a wuce nan ba, to ina ganin ka jawo rigima, da abinda ya kamata ka ce ni dai *AHALARIN* nan na tsare, in ana magana mai tsaurin na *MUKTASAR* kace ku je cen, ku ne Malamai, ga iyakan nawa nan, to da ace mutun zai hakan, to kuma har wala yau mai *MUKTASAR* zai ce kai don Allah gafara can Jahilin kawai, sai kayi *MUKTASAR* kake da ilimi, ko kuma sai kayi *MUKTASAR* za ka samu tsira, to da shi kuma ainihin ya kawo wata fitina din, saboda mai yiwuwa ba zai iya daga ilimin mai *AHALARIN* ba ya kai shi ga mustawa din *MUKTASAR* din ba, ko da zai iya yiwuwa sai a hankali, amma ba dare daya ba, to ko wannen daga cikin wayanan janibobin biyu yana iya yin laifi, wato wanda yake yana da ilimin da yafi yalwa, yana iyayin laifin in ya tilasa ma mai dan kadan cewa sai yazo ga mutasawan shi, hakan kuma mai ilimi dan kadan din sai yace mai Yalwan Ilimi din sai ya dawo ya sauko ga nasa mustawan, to ina ganin duka wannan za a samu rigingimu.
*-Allama Sayyid Zakzaky a wani jawabinsa da yayi a garin BIRNIN KEBBI a wani taron MUUTAMAR, a lokacin da Da'irar take fama da jarabawar fitinar cikin gida, a shekarun baya can.*

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post