ARBA, IN RANAR CIKA ALQAWARI

ARBA, IN RANAR CIKA ALQAWARI -

بسمه تعالى.

الذين يبلغون رسالات الله ويخشونه ولايخشون احد الاالله وكفى بالله حسيبا.

Idan da ace dukka Al'umma zasuyi aiki irin na manzan Allah (s. w.a)  da aminci da zaman lafiya ya cika ko ina da Al'umma tasamu natsuwar da babu wani me zaman dardar acikinta Amma idan hakan baisamuba acikinta to zasu zamanto ne suna rayuwar bala'i da tsiya da tashin hankali da musifa iri iri.
Rashin dabbaka addinin Allah yanda yace ayi shine babban abunda yajefamu cikin halin da muke aciki yau shine yasama muka manta hadafin zuwanmu wannann duniyar shine yasa muka manta da Allah Allah ya manta damu idan duk wannann halin da muke ciki sanadiyyar rashin aikata abunda Allah yacene to meye mafita????
Mafitar kwara dayace mudawo mubi tsarin Allah kamar yanda Allah keso ba yanda mukesoba muyi iya iyawarmu wajan bautama Allah gwargwadon yanda ya umarta.
Bayan haka da ace dukkan Al'umma zasuyi sadaukarwa irin wacce Imam Husain yayi ga wannann Addinin to da har abada baza'a sake samun wani dagutu da zai jagoranci musulmaiba da babu sauran wani ZALUNCI da zai zamana yana da iko acikin duniya da babu wata sauran fargaba ga al'ummar musulumai.

GAREMU MABIYA JAGORA NA HAKIKA.

Meyasa mu bazamu zamanto kwatankwacin sahabban Imam Husain (A. S)  A filin karbalaba munsani sun tsayune kyam albarkacin tsayuwar shugabansu Imam Husain gaban duk ZALUNCI duniya baki daya wanda dukkan mu a yanzu albarkacin wannann tsayuwar mukeci har suka cinma nasara wato suka kai zuwaga shahada wanda wannann matsayin shine burin duk wani mumini na hakika.

Tsayuwar jagoranmu ga dukkan zaluncin duniya ne yasa yasamu kansa acikin halin da yake ciki meyasa ne muma bazamu tsaya mu jajirce kamar yanda ya tsaya ya jajirce  badan komiba saidan ya isar da sakon Allah ga Al'umma kamar yanda kakansa mazon Allah yayi da Imam Husain  sukayi.

Dole ne idan munason yancin jagoran mu sai mun motsa kamar yanda yan'uwanmu suka tsaya har suka cika Alkwarinda suka dauka muma bamuda lokacin zura idanu👀👀👀akan wannann zalunci da akema jagoran
mu.


LABBAIKA YA ALZAKZAKY
LABBAIKA YA ALZAKZAKY
HAIHATA MINNAZILLAH.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post