Shekara daya data gabata na tabayin rubutu mai kama da wannan inda nayi tsokaci akan yawan tafiye tafiyen shugaba Buhari.
Lalle ne tafiye tafiye ga shugaban kasa abune mai alfanu da kawo cigaba ga kasa, domin ko ba komai tafiyar tana nuna kima da kuma martabar kasa a idon duniya, saboda idan babu kima da martabawa bamai gayyatar shugaban kasar ku. Kuma da alama tafiye tafiyen suna taimakawa tattalin arzikin kasa, ta hanyar kulla kasuwanci da kuma wasu yarjejeniyoyi Na inganta tattalin arzikin kasa. Idan har da za'a aiwatar da wadannan yarjejeniyoyi.
To amma a hannu daya a maganar gaskiya tafiye tafiyen zuwa yanzu sunyi matukar yawa, bincike ya nuna a wannan zamani babu wani shugaban kasa dayakai Na najeriya yawan tafiye tafiye, domin ana hasashen cewa daga shekarar 2015 zuwa yanzu shugaba Buhari yayi tafiye tafiyen da suka kai sau dari
Saidai abin damuwa zuwa yanzu mutane basuga amfanin tafiye tafiyen ba a zahiri, tunda babu wani Abu da za'a nuna ace sakamakon tafiye tafiyen ne aka samesu. Misali a lokacin tafiye tafiyen Obasanjo an yafewa najeriya bashin da ake bin ta na miliyoyin Dalar Amuruka.
Saboda haka zaiyi kyau shugaban kasa Buhari ya hakura da tafiye tafiyen nan haka nan ya tsaya ya tabbata duk abin da aka kulla a tafiye tafiyen baya an cimmusu, kada ya bari har lokaci ya kare batare da ganin sakamakon tafiye tafiyen ba, domin yin hakan zai zama aikin baban Giwa WATO ANYI BA'AYIBA. Domin matukar mulkinka ya kare ba tare da ganin alfanun abin da ka kulla akan tafiye tafiyen nan ba to gwamnati ka zata gamu da suka ta har abada.
Musa Ibrahim Daura
29-10-2019.