YANDA MUZAHARAR ASHURA TA GUDANA A GARIN SHADOW

YADDA MUZAHARAR ASHURA TA GUDANA A GARIN SHADOW.


Almajiran sayyeed zakzaky ne suka fito kwansu da kwarkwata suka fito domin nuna juyayin su da kisan da akayima jikan manzan Allah (s. w.) wato imam husaini wanda yazidu (L)  ya jagoranta  a filin karbala.


Da wannan dalili masoya ga jikan manzon Allah wato imam husaini suka fito suka nuna alhininsu ga wannan mummunan aiki na na yazidu (L).

Abun ya bada natija sosai duba da yadda Al'amari yaketa habbaka a garin na shado.  Ina nufin mabiya Alllama sayyeed zakzaky a kullum yawa suke karawa.


Gomnati tana kisa amma Al'amari a kullum yana bada abunda ake bukata wato karin mabiya na Ahlil baiti (As)


Lallai (IG)  kaji kunya a garin shado suma sun gudanar da muzahara ta Ashura. Dahaka zaka gane ita wannan harka kayan Allah ce kuma babu yadda zakayi da kayan da Allah ya tanada.

Daga karshe ina kara mika jinjina ga shafin nan mai farin jini wato( MA'ASUMA NIGERIA NEWS UPDATES.)

shi wannan shafi yana da matukar mahimmanci gake dan uwa ka daure ka rika ziyartar wannan shafin domin sanin meke faruwa a cikin duniyarmu a yau.

Allah ka kwato mana jagoranmu wato sayyeed zakzaky H daga hannun azzaluman mahukuntan kasarnan bihaqqi sayyeeda Ma'asuma.

Tareda wakilinmu.
Ammar Abubakar shadow.

20/9/2019

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post