Tun farko-farkon wannan makon ne dai shugabanni da manyan jami’an kasashen duniya suke ta tururuwa zuwa birnin New York na kasar Amurka don halartar taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 74 don tattauna batutuwa daban-daban da suka shafi kasashensu da kuma ma duniya baki daya, wanda aka fara shi a jiya Talata 25/09/2019 kuma ake sa ran zai dau kwanaki ana yi.
Ko shakka babu daga cikin batutuwan da ake sa ran za su fi daukan hankula a yayin wannan taron har da batun matsalar dumamar yanayi, rikici da kai ruwa ranar da ke faruwa a yankin Tekun Fasha, Yakin Yemen, takunkumi da shirin nukiliyan Iran, rikicin Indiya da Pakistan, Rikicin kasar Venezuela, fitar Birtaniyya daga Tarayyar Turai (Brexit) da kuma ‘rikicin’ Palastinawa da Isra’ila.
Duk da cewa shugabannin duniya da dama ne za su je wajen, sannan kuma shugaban kasa dai shugaban kasa ne, don haka kowane shugaba yana da irin na sa muhimmanci, to amma ko shakka babu akwai wasu shugabannin wadanda idanuwan duniya za su fi komawa kansu da kuma jiran aji me za su ce, kai ka ce ma tamkar saboda su aka yi taron.
A mafi yawan lokuta dai, musamman cikin shekarun baya-bayan nan wadannan shugabanni sun hada da shugaban Amurka, shugaban Rasha, shugaban Iran da kuma firayi ministan ‘Isra’ila’ watakila da wasu na daban. Duk da cewa a wannan karon watakila an rasa shugabanni biyu wato na Rasha da na ‘Isra’ila’ don kuwa ba za su halarci taron ba, duk da cewa Netanyahun Isra’ila din kan ma daga dukkan alamu koda ya zo da wuya ya samu irin muhimmancin da a baya ake ba shi saboda kusan an riga da an san me zai fadi, sannan kuma tasirinsa yayi kasa sosai.
To sai dai daga yadda na bibiyi wannan batu tun daga kusan shekaran jiya har zuwa yau din nan, ko shakka babu gwarzon taron shi ne shugaban kasar Iran, Dakta Hasan Rouhani.
Daya daga cikin dalilan da ke tabbatar da hakan shi ne yadda tun daga isarsa birnin New York, a ranar Litinin din da ta gabata, idanuwa suka koma kansa. Kafafen watsa labarai hatta na ‘makiya’ suna son hira/tattaunawa da shi. Shugabanni da firayi ministocin kasashe daban-daban suna ta hankoron ganawa da shi. Shugaban Amurka, Donald Trump, kan ma babban fatansa shi ne samun damar ganawa da shi a bayan fagen wannan taro.
Mene ne dalilin hakan?
Babban dalilin hakan shi ne kasar da ya ke jagoranta, wato Iran.
Hakan kuwa ya biyo bayan irin matsayin da kasar ta kai ne na zama daya daga cikin kasashe masu fadi a ji, ko kuma ma ta farko a wannan bangaren, alal akalla a yankin da take.
Ba don komai Shugaba Rouhani ya sami wannan matsayin ba sai saboda: Yana jagorantar kasar da ta mallaki karfi na zahiri na duniya, a duniyar da karfi din shi ne hajar da ke ci.
Saboda yana jagorantar kasar da ta mallaki makaman da babu wani da ya isa ya ce mata ‘kule’ ba ta ce masa ‘cas’ ba.
Saboda yana jagorantar kasar da ke jagorantar sansanonin ‘yan tsayin daka (Mihwar al-Muqawamah da larabci ko Axis of Resistance a turance) da suke da karfin sauya yanayi na siyasa da karfin soji a yankin nan musamman a kasashen Yemen, Labanon, Palastinu, Siriya, Iraki da sauransu.
Yana jagorantar kasar da ta mallaki karfi da fasahar dogaro da kai; wacce ta mallaki ilimi da tunani da idan aka yi riko da su duniya za ta amfana; wacce ta riki siyasar gaskiya da cika alkawari da girmama yarjejeniyoyi na kasa da kasa; wacce ta dogara da al’ummarta wajen cimma duk wani abin da ta sa a gaba; haka nan kuwa wacce uwa-uba, ta sa Allah a gaba take neman taimakonsa a dukkanin fagage.
Wadannan siffofi kuwa su ne, abin bakin ciki, shugabannin larabawa, wadanda ya dace su yi tarayya da shugaba Rouhanin cikin wannan yanayi, suka rasa. Don haka suka zamanto zuwansu da rashin zuwansu wannan taron, kusan duk daya ne, watakila ma gara ma ba su je; don kuwa babu ma mai sauraransu. Alhali shi kuwa shugaban na Iran (kowane ne shi kuwa, kama daga Sayyid Khamenei, lokacin yana shugaban kasa, har zuwa ga Rouhani na yanzu) kowa na jiran dakon ya ji me zai ce ne duk kuwa da cewa ‘yan tawagar wasu kasashe irin su Amurka, ‘Isra’ila’, Saudiyya da sauransu musamman na kasashen larabawa, su kan fice daga babban zauren majalisar yayin da wani shugaban Iran ke jawabi, amma ko shakka babu su kan koma dakunansu su saurari abin da zai ce don kuwa sun san maganarsa tana da muhimmanci kuma za ta ma iya shafar makomarsu.
Muhammad Awwal Bauchi.
IRIB Hausa - Tehran, Iran.
Tags:
Labaran Duniya