gwamnatin Katsina ta roki da a nadi hukunci mai tsanani ga wadanda basuyi rijistar layukan wayar su ba

GWAMNATIN KATSINA TA ROKI DA A TANADI HUKUNCI MAI TSANANI GA WANDANDA BASUYI RIJISTAR LAYUKAN WAYARSU BA

 🇳🇬 MAASUMA NIGERIA NEWS UPDATE 🇳🇬

Gwamnan Bihar Katsina aminu bello masari




TARE DA SHARHABIL USMAN PANDOSS

Gwamnatin jihar Katsina ta bukaci gwamnatin tarayya da ta tanadi hukunci mai tsanani ga kamfanonin layukan wayar hannu da suka gaza cika umurninta na rufe duk layin wayar da ba ya da rajista.

Mataimakin gwamnan jihar Alh Mannir Yakubu ya yi wannan roko a lokacin kaddamar sa cibiyar kai daukin gaggawa ta zamani da ma’aikatar sadarwa ta kasa ta kafa a Katsina.

Mataimakin gwamnan ya yi yabo ga
 ma’aikatar sadarwa ta kasa da ta yanke wannan shawarar. Ya ce hakan zai taimaka gaya wajen raguwar ayyukan assha a cikin al’umma.

Ya ce jihar Katsina ta yi na’am da wannan sabon tsari na neman daukin gaggawa da mutum zai buga lambar 112 don kawo ma sa agaji a sassa daban-daban da ya ke bukata.

Idan za a iya tunawa dai, ma’aikatar sadarwa ta kasa ta kafa tare da kaddamar da wata cibiya ta zamani da za a rika kiran waya domin neman agajin gaggawa ga wadansu bala’o’i da suka ko suke neman tasowa.

Ministan sadarwa na Nijeriya Dr. Ali Isah Pantami ya ce ma’aikatar ta bullo da shirin ne domin mutane su nemi agajin gaggawa daga ‘yan sanda, jami’an kwana-kwana, na hukumar kiyaye hadurra da sauran sassa daban-daban.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post