*RA'AYOYIN AL'UMMA AKAN AKAN HARIN DA JAMI'AN TSARO SUKA KAWO A MARKAZIN YAN'UWA MUSULMI A KATSINA*

MALAM YAKUBU YAHYA KATSINA NA ZAUNE LAFIYA DA
MAKWABTANSA,

Tawagar ma’aikatan lafiya na 'yan-uwa Musulmi almajiran
Shaikh Zakzaky (H) watau ISMA, sun kwashe kwanaki biyu
Alhamis da Juma’a da su ka gabata, su na zagayen gidajen
makwabtan Markazin ‘yan'uwa da ke unguwar Kofar Marusa
Sauri da wurin zuwa domin jajantawa wadanda harin ranar
Ashura da Mahukuntan Nijeriya su ka kaddamar ga unguwar da
mutanen unguwar.

Zagayen ya hada da kokarin kara tantance wadanda su ka
samu cutuwa sosai sakamakon wannan hari na Teargas da
harsasan bindiga.

Akwai makwabcin Markaz dattijo dan sama da shekara saba’in (70)
Shaheed Mallam Muhammad Adamu da wannan hayaki ya
turnuke gidansa ya zamo ajalinsa, ’yan sanda su ka yi masa
kisan gilla da hayaki mai guba a cikin gidansa.

Yayin wadannan ziyarori an binciki yanayin lafiyar makwabta da aka ziyarta, akwai masu matsaloli sakamakon shakar hayaki mai guba da yanayin da aka shiga na tsoratarwar masu kawo hari da sauransu, an gayyaci mutane da dama zuwa Sickbay
‘yar karamar asibiti a cikin muhallin Markaz aka ba su
magunguna da shawarwari. An kuma jajantawa wadanda sun
sami sauki sakamakon wannan ta’asa.

Ra’ayin mazauna wannan unguwa duka ya zo daya akan cewa
lalle su na zaune lafiya da ‘yan'uwa musamman Mallam Yakubu Yahya, kuma zasu cigaba da kasancewa tare da wannan Harka.

Alhaji Mansur Ya'u (Babba) wanda wani makwabcin Mallam ne ya sheda mana cewa a lokacin da abin ke faruwa ya kawo kudi
ya baiwa matansa domin su hau abin hawa su bar unguwar
amma su duka suka ce sai dai a nike su tare da Malam, babu
inda za su tafi.

Hajiya ‘Yar Fara dattijuwa yar shekara saba’in (70) makwabciyar Markaz, tace babu inda za mu mu bari diyan banza su cimma
Malam, mun shirya su kashe mu tare da shi da ‘ya’yan mu da
jikoki, tace ban taba jin karatu mai dadi irin na Malam Yakubu
ba, tace, mun sheda yana layya da sadakoki saboda da Allah.

Sanata Alhaji Abdu Yandoma, yace ku gaida mani Malam,
babu wani hakuri ko jaje da Mallam zai aiko mana, an zo cutar da shine aka cuce mu, Allah Ya saka mana baki daya,

Alhaji Tukur dattijo ne sosai sama da shekara chasa’in (90) ya ce mun sha azabar Teargas daga ‘yan-sanda, amma Allah Ya isa
tsakanin mu da su, ba laifin Malam ba ne ko almajiransa, na
tafi gidan dan'uwa na, na sami labarin sun zagaye mana
unguwa na dawo, yarana na cewa mu bar unguwar na ce
masu babu inda zani, na ratso ta gaban ‘yan sanda na wuce
har wani daga cikinsu na tambayar dattijo ina zaka? Nace
masa gida na, nan ba Batsari ba ce ko Kankara me ya kawo
ku?

Akwai wani bawan Allah A Mukhtar Suleiman wanda Teargas ta fada a tsakar gidansa, abin ya cutar da mu, shima ya dora
laifin wannan ga wadannan ‘yan ta’adda da ya kamata su tafi
dajin Batsari inda aka fi bukatar su.

Wata mata 'yar kabilar Igbo da mijinta wadanda makwabtan
Mallam ne, sun yi Allah wadai da Buhari da gwamnatin sa
wadanda suka kira da ‘yan ta’adda masu takura ‘yancin addinin mutanen kasa.

Zuwa yanzu an sami gidaje da dama wadanda kwanon rufin su
ya farfashe da bangwayen su sakamakon duwatsu da Teargas,
yanzu haka ‘yan'uwa almajiran Malam na cigaba da gyarawa
wadannan makwabta muhallan su da aka lalata da duwatsu da
kwafsar Teargas da harsasan ‘yan-sanda.

Daga: Sashen Lafiya na Yan'uwa Musulmi, Yankin Katsina,

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post