Bayan sun kai su Malam Zakzaky sun tsare su a Hedikwatan
‘Yan sandan kwantar da tarzoma a Kaduna, sun rika musu
tambayoyi kala-kala, ciki har da cewa me Malam ya je yi
kwanan baya a London? Suka ce ya rubuta amsar. Nan ya basu
cewa ya je ta’aziyyar wani dan uwa Musulmi ne da ya rasu a
can.
Haka ma su Malam Abubakar Almizan ‘yan sandan sun ta
musu tambayoyi akan wai suna gudanar da gidan rediyon FM
ba tare da izini ba. Daga karshe dai duk abin ya zama kame-
kame ne. Don haka binciken ya kare ba tare da sun samu wani
bakon abu tabbatacce ba.
Ko da yake masu tsare su din a lokacin sun dan saki jiki da su
Malam daga zuwansu wajen a ranar Alhamis zuwa safiyar
Juma’a. Amma zuwa yammaci bayan da aka yi waki’ar Kofar
Doka, sai yanayin ya canza, suka tsaurara dukkan matakai da
mu’amala ga su Malam, har zuwa safiyar Asabar, wanda ba
wani shiri suka yanke hukuncin su daukesu su yi Kudu da su.
Ranar Asabar 14/9/1996 aka zo da motoci aka kwashi su
Malam Zakzaky, Alhaji Danlami, Malam Abubakar da Malam
Shittu, ba tare da wani bayani ba, a ka bar Kaduna da su, akai
Kudu, yayin da aka kai Malam Shittu kukukun Benin, aka kai
Malam Abubakar Almizan na Kalaba, aka kai Alhaji Danlami na
Inugu, shi kuma Malam Zakzaky aka kai shi kurkukun Fatakwal.
Muzaharorin kira a saki Shaikh Zakzaky sun cigaba da gudana
akai-akai a tsawon akalla shekaru biyu da wata uku na tsare
Malam, wanda ya fara tun daga Satumbar 1996 har zuwa
Disambar 1998, kimanin shekaru biyu da wata uku. A yayin da
Muzaharar da aka samu waki’amafi tsanani bayan ta kofar
Doka, ita ce wacce ta gudana a ranar Laraba 19 ga Satumbar
1996 din a garin Kaduna, wanda aka samu Shahidai mutum
shida, wadanda aka iya tabbatarwa, ko da yake sun ta kasha
wasu ‘yan'uwa da ma mutanen gari sun tafi da gawarwakinsu
da ba a iya tabbatarwa ba, tare da masu rauni.
Daga wannan waki’ar ce kuma suka fara aiwatar da shirin
Abacha na uku, wanda shine farautan ‘yan'uwa a garuruwansu
ta hanyar amfani da sarakuna, hakimai da masu unguwanni,
aka rika kama ‘yan'uwa ana daurewa a kurkuku da cel din ‘yan sanda, ana azabtar da su, da dira Fudiyoyi da wuraren
Ta’alimomi, a bude wuta da harsashi masu rai da tiyagas
kamar yadda ya sha aukuwa a wajen Ta’alimi a Kaduna da
sauran gurare.
Wani lokaci insha Allah za mu waiwayi yadda aka rika wasan
kwaikwayo da sunan yiwa Shaikh Zakzaky shari’a a Kaduna,
mutuwar Abacha wacce ta auku a ranar 8 ga watan June, 1998
zuwa sakin su Malam Zakzaky da yadda aka tarbe su. Muna
rokon Allah kamar yadda ya kawo karshen waccan waki’ar da
mutuwar Abacha, ya kawo mana karshen wannan waki’ar da
abin da yake ganin shine maslaha kuma kubuta da aminci gare mu.
Waki’ar Abacha da yunkurinsa na ganin bayan Harkar
Musulunci kamar yadda Shaikh Zakzaky yake fada: “Shine ya
kawo tumbatsa da habakar al’amarin Harkar Musulunci wanda
aka ji duriyarta a duniya, har duniya ta san a kasar nan akwai
wasu mutane masu wata da’awar komawa addinin Musulunci.”
Ko ba komai daga karshe tuhumar da ake wa Shaikh Zakzaky
ya tashi daga yin gidan rediyo ko tafiya London, ya koma
zargin wai yace “Babu hukuma sai ta Allah.” Kamar dai yadda
yanzu zargin da ake masa ya tashi daga sanyawa a tare hanya,
ko rashin bin dokar kasa, suka koma suna kokarin cewa yana
yunkurin Musuluntar da Nijeriya ne.
Muna rokon Allah ya gaggauta kawo mana karshen zalunci da
azzalumai. Ya daukaka Musulunci da ma’abotan yunkurin
tabbatar da shi. Ya kaskanta kafirci da masu aiwatar da shi. Ya
karbi shahadar Shahidanmu, Ya girmama matsayinsu, Ya bamu
I tasu, Ya tsinewa makasansu albarka. Ya gaggauta kubutar
Jagoranmu da dukkan ‘yan'uwa.
Tags:
Munasabobi
