BAZA MUYI YAKI DA IRAN BA, INJI YARIMAN SAUDIA !!!!

Yaki da Iran zai durkusar da tattalin arzikin duniya - Yarima MBS,

Yariman kasar Saudiyya mai jiran gado, Muhammad bin Salman, a hirar da ya gabatar ranar Lahadi ya bayyana cewa fito na fito da kasar Iran zai illanta tattalin arzikin duniya. Ya bayyana cewa ya gwammace a yi zaman sulhu da siyasa maimakon yaki. Yarima Mohammed bin Salman ya kara da cewa idan aka shiga yaki a yanzu, farashin danyen mai zai iya tashin da ba'a taba tunani ba. Yace: "Wannan yankin na da arzikin man kashi 30 cikin 100 na duniya, kashi 20 cikin 100 na hanyoyin kasuwanci, kimanin kashi 4 na tattalin arzikin duniya." "Yanzu me kake tunani idan dukkan wannan ya tsaya. Hakan na nufin durkushewar tattalin arzikin duniya, ba Saudiyya ko kasashen larabawa kadai ba." Ya yi kira ga shugabannin duniya da a dauki matakin dakile Iran da kuma samar da zaman lafiya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post