AN BIZNE SHAHIDAN BAUCHI A DARUL-RAHAMA ZARIA


A ranar Talatar da ta gabata ne , yan uwa musulmi almajiran
Sayyid Zakzaky (H) na garin Bauchi , suka fito muzaharar
#RanarAshura1441 a garin bauchi kamar yanda aka saba duk
shekara, Muzaharar na cikin tafiya kamar yanda aka tsara sai
ga , jami'an tsaron Nigeria yan ina da kisa, suka bude ma
masu muzaharar wuta ba tare da sun musu laifin komai ba,
inda suka raunata da dama, suka kashe mutum hudu, wato

  • Shahid_Huzaifa_Sunusi
  • Shahid_Huzaifa_Adamu
  • Shahid_Ahamad_Shu'aibu
  • Shahid_Hussaini_Haruna


Anyi musu sallah ne a jiya Alhamis, a bauchi din a safiyar
Juma'a kuma aka bisne su a Makabartan Shahidai na Darul-
Rahama Dake kauyen Dambo A Zariya.

Amincin Allah ya tabbata a Gareku Randa aka haifeku da Ranar da aka kasheku da Ranar da za'a tasheku kuna Rayayyu.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post