A Gaskiya ba Shi'a ce matsalar Nigeria da talakawan Nigeria ba,!!!

Yau ko yaro karami ya San matsalar Nigeria ba zaman juyayin ashura,Tattaki ko Mauludin da yan shi'a suke yi bane.
  • Matsalar Nigeria ba Muzaharar free Zakzaky da Almajiransa suke Yi bane.....



Yunkurin da shugaban 'Yansanda Yake burin yi na Afka ma yan Shi'a a fadin Nigeria da sunan bin umurnin Kotun da ta haramta harkah Islamiyya ba zai taba haifarwa Nigeria da Mai Ido ba..



Domin suma fa 'yan-nigeria ne Kuma a cikinta aka haife su,ba daga sama suka fado ba,Kuna tsammani zasu daina Addini kenan saboda kun haramta su.....?



Me yasa kuke son boye gazawar ku ta hanyar amfani da zubar da jinin Almajiran Malam Zakzaky(H)....?




Yaushe zaku magance matsalar tsaro da kuka yi wa talakawan Nigeria alkawari....?


Wanene ya tsira daga sharrin Barayin Shanu da Kidnappers da suka hana talakawan da suka zabe ku da Miliyoyin kuri'a barci da Ido biyu....?


Kafin ka Zama Inspector General Of Police a Nigeria wadansu sun Zama yanzu suna Ina....?


Akwai wadanda suka yi yunkurin ganin bayan yan Shi'a da da'awar su ka tambaya sun ci nasara....?


Wadansu ma wurin da aka tsare Malam Zakzaky(H) can aka Kai su.


Malam Zakzaky(H) da Allahu Ta'ala ya dogara kuma shine zai kare shi daga sharrin ku insha Allahu,mu daku shege ka fasa......
ZAINILABIDINA AHMAD SULEIMAN

My Name is Zainilabidina Ahmad Suleiman Chief Executive Officer CEO Bz News 24/7. Famous Blogger| Developer | Programmer| Journalist| Consultant |Publisher |. Contact bzglobalservice@post.com Whatsapp+2348133888333

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post