ME YASA MUTUM KE KISA (MURDER)?

✍️
 Aliyu Dahiru Aliyu
Ba iya mace kawai ba, dukkaninmu, maza
YADDA MUTANE KE KISAN KAI
da mata, acikin kwakwalwarmu akwai wani sashi da yake sanya kisa! Abune na mamaki kwarai acikin ilimin "Psychology"! Ta yaya wannan abin mamaki yake faruwa? Ta yaya muke kisa? Meyasa muke kisa?  Ta yaya muke iya kashe na kusa damu? Daya daga cikin manyan malaman kimiyyar tadawwuri (Evolution) wato David M. Buss ya rubuta littafi mai suna "The Murderer Next Door : Why Mind Is Designed to Kill", ya bayyana cewa acikin kwakwalwarmu akwai gurin da aka saita don yayi kisa! Acikin kwakwalwarmu akwai gurin da tsarin halittar mutum ne kawai yayi kisa. Tun asali (bisa tsarin evolution) mutum ya gano cewa hanyar gamawa da wata matsalar tasa itace ya kashe dan uwansa. A haka Qabilu ya kashe Habilu don biyan bukatarsa. Daga nan kwakwalwar mutum ta dinga girma har ta tsirar da wata hanya (paths) da aikinta kawai shine ingiza mutum ya yi kisa ko ya batar da wani daga doron kasa.

Farfesa Carol Holden, daya daga cikin manyan malaman ilimin shari'ar halayyar masu laifuka (Forensic Psychology) yar asalin Amurika, bayan ta yi shekara goma sha biyar tana bincike akan halayyar masu kisa ta bayyana wani bincike mai tsoratarwa! Ta fada cewa ba mu da banbanci da waxanda suke kisa! Tana ganin mutanene dai-dai da kowa. Wannan ba zai zamo babban abin mamaki ga wanda yake bincike sosai ba. Mu yayan Qabilu ne da ya kashe dan uwansa! Kafin Qabilu da Habilu kuma dangin "Neanderthelensis". An tabbatar da cewa dangin "Neanderthelensis" har cin naman yan uwansu suke! Kada ka dauka ba'a yi su ba! Binciken ilimi ya tabbatar da rayuwarsu kuma an tabbatar su ma idan dayansu ya mutu to binneshi suke. Duk ta nan dan adam ya gado kisa da zubar da jini ta cikin jinin jikinsa da kwayoyin halittarsa (genes). Bayanin cewa wai kisa yana faruwa ne agun waxanda ba su waye ba ko masu qarancin ilimi ba shi da tabbataccen tushe domin binciken ilimin zamani da na taxawwuri sun tabbatar da kuskuren haka.

Ta fuskar addini da ma rai mai umarni ga mummunan aiki ce. Tun kafin nan da ma mala'iku sun bayyana mutum (mace da namiji) a matsayin masu zubar da jini da barna aban kasa. Lokacin da Allah yace da malaiku zai halicci mutum daga tabo, sai suka ce ta yaya Allah zai sanya wanda zai zubar da jini kuma yayi kisa aban kasa! Shi yasa a tsawon tarihi ake samun masu kashe-kashe acikin mutane, mata masu kashe mazajensu da kuma maza masu kashe matansu, maqoci mai kashe maqocinsa, malami mai kashe xalibinsa, mai kuxin da yake kashe talaka. Bincike ya nuna mutum shi ne mafi kashe xan uwansa a duk cikin yan uwansa dabbobi! Zaki, kura, miciji, kada, kifi da sauran halittu; babu wanda ya kai mutum kashe xan uwansa acikinsu! Zubar da jini acikin kwakwalwar dan Adam yake daga Ghenghiz Khan, Adolf Hitler har zuwa Benito Mussolini. 

David M Buss yana cewa idan aka duba kwakwalwar mai kisa za'a gano wani abu na halittarsa da yake ingizashi don kisan. Kuma abin mamakin ba iya mai kisan ba, a duka halittunmu akwai wannan halittar sai dai wani yafi wani iya riqe kansa! Binciken kimiyya, musamman ilimin Psychology ya tabbatar da cewa a kaso 100 bai fi kaso 5 ne suke kisa saboda akwai matsala a qwaqwalrsu ba! Mafi yawan wadanda suke kisa lafiyarsu kalau sai dai lauyoyi su lanqwasa magana su dinga ganin kamar hakan haukane. Nawa muka gani daga malaman addinin sun yi kisa? Nawa muka gani daga masana Falsafa sun yi kisa? Nawa muka gani daga shugabanni suna zubar da jini? Maganar kisa ko zubar da jini bai ware jinsi ko al'ada ba. Kisa yana faruwa a ko'ina kuma a kowane hali. Ba sai mun tsawaita a tarihi ba, nawa Ghenghiz Khan ya kashe? Dubunnan miliyoyi shi kadai! Shi kadai ya sanya aka kashe mutanen Naishapur baki dayansu maza da mata da yara da dabbobi saboda sun kashe sirikinsa guda daya kacal! Nawa Adolf Hitler ya kashe? Shi kadai ya kashe yahudawa sama da miliyan shida! Mutane nawa aka kashe tsakanin yakin duniya na daya da na biyu? Sama da miliyan dari! Wannna ban ja ka zuwa tsohon tarihi ba da mutum cike yake da kisa da zubar da jini da barna a ban kasa.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post