ZALUNCI DA DANNIYA

ZALUNCI DA DANNIYA:

Nigeria Ina Mafita Na Sheikh Zakzaky
Ma'asumah Nigeria News update
Ishaq Muh'd Suleiman


To, na farko zalunci. Zalunci kamar yadda na riga na fa]i ma’anarsa na lugga shi ne mutum ya ci haƙƙin wani. Haƙƙin nan na iya zama kayan wani, ko kuma yana iya zama wani haƙƙi ba na kaya ba, ko da na damar ya faɗi ra’ayinsa ne ko kuma haƙƙin ya san wani abu. To in ya zamana 
an hana shi wannan haƙƙin, to za mu iya cewa an zalunce shi.
Zalunci yana iya zama har wala yau ta fuskar yin shisshigi a kan 

  • haƙƙin wani. Wato ko da ba a danne shi ba, an kutsa masa, an tauye masa ko yaya ne. Saboda haka muna iya cewa kishiyan zalunci shi ne adalci.

 Adalci yana iya zama daidaita mutane da kuma daidaita su a wajen rabo. Alal misali da za'a ce mun ha]u za a raba wani abu da yake duk namu ne, to a raba shi daidai wa daida zai zama adalci. Koda yake wani lokaci adalci ba ya nufin daidaito. Alal misali inda zamu ci abinci  ne aka ce to kowane mutum a ba shi daidai yawan kada yafi na kowa, to zamu ga cewa mai babban ciki an ƙware shi, kuma an yi wasa da yaro. 
Kamar ga yaro ɗan ƙarami sai a kifa masa ƙaton malmala. Mai babban ciki kuma zai iya cinye wannan malmala din, shi kuma ƙarami zai tsakura ne ya zubar da sauran, to ba zai zama an yi adalci ba. Adalci ba lalai yana nufin daidaito ba ne.
Har wala yau muna iya cewa, shisshigi shi ma kishiyan adalci ne. 
Wato kamar mutum ya kutsa cikin abinda yake haƙƙin wani ne. Na 
wani ne ba nasa ba. Saboda haka zamu ga a isɗilahin Alƙur'ani wannan kalma ‘Zulm’ ta zo a wurare da yawan gaske a Alƙur’ani. Kai kace Kamal ‘Zulm’ ɗin nan, zalunci wani abu ne wanda yake a wurin Allah Ta'ala yana da muhimmanci, tunda a wurare daban-daban a Alƙur'ani zaka ji kalmar Zulm ta ɓullo, ko da sunan Zulm ɗin ko da sunan su 
azzalumai ɗin, ko wane ya fi zalunci, “Waman azlamu mimman” kaza 
da kaza. Zaka ga a wurare da dama Allah yace wa yafi zalunci fiye da wanda yayi kaza, yayi kaza. Zan dawo kan wannan in nazo kan nau’o’in zalunci.
Sannan kuma zaka ga wurare inda ya ambaci zulm ]in da sunan 
zaluncin. Kamar inda yake cewa “Innas shirka lazulmun azim.” Kuma  akwai hadisi ƙudsi inda Allah (T) yake cewa “Ya ku bayina na haramta  wa kaina zalunci, kuma na ajiye zalunci ya zama a tsakanin ku haram. 
Saboda haka kar ku zalunci junanku.” To, ‘Zulm’, ‘Zulm’, gashi nan  birjik a cikin Alƙur’ani, kuma birjik a cikin hadisin Manzo.
Kazalika kuma abinda ke kishiyantar zuluncin nan, su ma zaka gan su kalmomi ne da suka zo a wurare daban-daban a Alƙur’ani. Su ne 
‘Adal’, adalci ke nan. Shi ma za ka gan shi a wurare daban-daban a 
Alƙur’ani, inda Allah (T) ke umurni da ‘aiki ko ‘Adal’; duk dai abu 
guda ne. Hakki kamar ana nufin a yi abu daidai, ya yi ‘balance’ kenan. 
Adal shi ma kazalika, abin da yake nufi kenan. Kamar inda Allah (T) 
yake cewa ‘Innallaha yuhibbul muhsiɗin.” da kuma “Wala ta’atadu innallah la yuhibbul mu’utadin.” Wato zaka ga yana ta kawo Adal, adal a wurare daban-daban.
Yana umurni da yin ƙisɗ’ da hani ga barin zalunci.

Zamu cigaba Insha Allah

Ma'asumah Nigeria News update
Tare Da Ishaq Muh'd Suleiman
08132933333
09/07/2019

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post