NA DADE INA ADDU'AH AKAN ALLAH YA HADANI DA MALAM ZAKZAKY(H) SABODA YADDA NAKE JIN LABARINSA


—Cewar Muhammad Awwal Udawa.

Daga shafin Ma'asumah Nigeria News Updated afirar mu da mom Muhammad acikin satinnan, tare dani Ammar Umar udawa.


Ma'asumah: Zamuso muji cikakken sunanka?

Muhammad Awwal: Sunana Muhammad Awwal ina da shekaru @52yr a duniya.

Ma'asumah: Zamuso jin ya rayuwarka ta kasance kafin ka fahimci 'Harka'?

Muhammad Awwal: Rayuwata ta farone daga dalibi (Almajiri) ni dalibine a wajen wani Malami danayi kartu wajensa a Panbeguwa, gaskiyar Magana na tashi ne da ibada. Malamin mu baya mana da wasa wajen ibada da karatu.

Ma'asumah: Ko me Nene Asalin abinda ya haska maka har ka fahimci Harkar Musulunci?

Muhammad Awwal: To, a zahirin gaskiya 'Ni dai na Dade inajin labarin Malam Zakzaky(H), kuma tun lokacin da nakoma Mahaifata (Ingade) karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna, kafin inzo Udawa. Na kuma dade ina Addu'ah akan Allah ya hadani da Malam Zakzaky ko sau daya ne, in ganshi domin yadda nakejin labarinsa. Kawai sai nahadu da wasu (Yan Shi'a), Dariya! Lokacin ban mantawa munje Zariya tare dasu Makon hadin kaine lokacin ana yinshi a Fudiyya Center (FIC), da nayi niyyar kwana 1, idan naga Malam(H) indawo sai kawai akamin abinda ya burgeni sai da mukayi kwanaki(3) tabbas! Zantukan Malam(H) sun kara shaja'antani, tunda muka dawo a ka tsunduma cikin Harka har zuwa yanzu.

Ma'asumah: Bayan ka fahimci 'Harka' ko a kwai wata jarabawa daka fuskanta kodaga Iyaye mutanen Gari ko 'Yan Uwa?

Muhammad Awwal: Alhamdulillah Jarabawa an fuskanta, amma ta janibin mutanen gari, domin a lokacin Sarkin garinmu yakan rika harzika matasa domin su afkamana a lokuta daban-daban Amma Allah ya kiyaye 'yan Uwa, kuma dama ni iyayena sun Dade da barin cubits(Rasuwa) kuma banda matsala da 'yan Uwa insha Allah.

Ma'asumah: zuwa lokacin daka fahimci Harka ko a kwai wani canji da kakeji?

Muhammad Awwal: Banbancin Dana keji -ita Harka Abu gudace, kafin in fahimci Harka, zuciyata tanamin sake-sake amma bayan na fahimta sai najin ba abunda ke damuna, insha Allah.

Ma'asumah: Mun gode.

Muhammad Awwal: Nima ngd

Rubutawa: Ammar Umar udawa

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post