SHUGABAN ÝAN SANDAN SRILINKA, YA FI NA NAJERIYA KISHIN ALÚMMA, YA AJIYE AIKINSA, SABODA HARE HAREN DA AKA KAI KASARSA.

Ranar Easter aka kai wadansu hare hare a kasar Srilinka, wanda yayi sanadiyyar mutuwar ýan kasar da dama.

Shugaban Ýan sanda na kasar, JAYASUNDARA, ya ajiye aikinsa, saboda abin da ya kira gazawarsa wajen dakile hare haren da aka kaiwa  ýan kasarsa haka siddan, Kafin shi ma, wadansu manyan Jamián tsaro sun yi ritaya saboda irin wannan dalili.

Wannan ya isa Ýan Najeriya su yi kuka da takaicin irin Shugabannin da muke da su, da Jamián tsaro marasa tausayi da kishin kasarsu.

A Nigeriya kuwa Buratai shugaban hafsan sojoji kasar kashe 'yan Shi'a yayi amma aka karamai mukami tare da mukarrabansa.


Mu, anan Najeriya, sau da yawa, Jamián tsaron ne ke kaiwa ýan kasarsu wadanda ba su ji ba, ba su gani ba hari. Su harbe su, ku karkashe, su, ba tare da wani dalili ba. Watakila saboda su cimma burin wadansu.

Wannan babban darasi ne ga Jamián tsaron Najeriya. Tambaya ga Insfekta Janaral na Ýan sandan Najeriya. Ga shi ana ta kashe bayin Allah a arewa, ana sace su ana garkuwa da su.

Yaushe za ka yi koyi da JAYASUNDARA na kasar Srilinka ka yi ritaya?

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post