LABARI NA (part 7) ABIN DA YA JA HANKALINA NA ZAMA DAN SHI'A


Kayi Shere domin wasu Amfana.
Cewar Abdurazak Sani
Kashi na bakwai.

_Da fari zamu so muba da hakuri ga yan uwa bisa kwana biyu na rashin ciga ba da wannan rubutu, sakamakon wasu dalilai da fatan za'a gafarcemu_

_Baya ga haka muna godiya da sakonnin Ku, musamman wadanda suka turomana sakunan su ta Email, ko Comments  kamar su TIJJANI ISYAKU, HABIB YA'U, MUSA HASSAN KD d.s da wadan da bamusami damar kawowaba sakamakon karancin lokaci muna godiya sosai Allah yasa ka da Alkhairi ya kuma bar zumin ci, bihakki sayyidil anbiyya, da iyalan gidan sa, da sahabban sa tsarkaka Ilahy/amin._
______________CI GABA_______________
A rubutun mu na baya mun tsaya gun da Abdul ya ke kokarin barin gidan su a yayin da mahaifina su ya ce da shi ya barmasa gidan sa za mu Dora....

A dai dai wannan lokaci haka na shiga dakin Maman mu, idona na cike da kwallah, Maman haka ta dube ne sa'annan ta da da fashewa da kuka ta ce da ni, yanzu Abdul tafiya zakayi kabar ni? Fadar haka ke dawuya ban San lokacin da hawaye suka gangaro daga idanuna ba, haka na yi karfin hali, na ce mama ki yafeni sannan ki Yimin addu'a... Ban gama karsawa ba bansan lokacin da na fashe dakuka ba. ita ko Maman ba'acewa komai, kannena kuwa kowa yayi ta gumi, hawaye na zubuwa daga idanuna su, duk da irin wannan hali da ake ciki, kukan mahaifiyata yayi tsanani, kan warmu ita ta ke rarrashin mahaifiyar mu.
Duk da cewar nasan bakomai bai ne ya tayarwa da mahaifiyata HANKALIba face yau gashi zan bar gidan mahaifiyana, batasan wanna hali zan shiga ba, musamman yadda nashiga halin haula'i baya, ta yadda mahaifiyata, tasha wahala akai na, duk da cewar shima Abban mu yasha wahala akaina Amman shi baba daga baya tunanin hakan.
Haka na je na durkusa sa agabanta hannuna na kan gwuwowinta na ce mama Dan Allah ki yi hakuri, sannan komai me wucewa ne mama, ki ya femin, sannan ki cigaba da sani adduoin ki mama inshaAllah bazan baki kun yaba... Kafin na karasa bansan lokacin da na Dada fashewa kuka ba, Maman mu ta dubeni fuskarta hawaye na gangarowa da ga idanuna ta, ta ce babu komai Abdul na yaba femaka sannan ka kula Abdul, ina yimaka wasiya da kaji tsoran Allah a duk Inda ka ke, ka kula da salloli.

Haka ta Yimin nasihohi masu ratsa jiki ta ce dani tashi katafi abdul Allah ya yimaka Albarka.
Duba da yadda halin da mahaifiyata ta ciki haka na fito cikin sauri, da fitowata mahaifiyata ta Dada fashe da kuka, suka kanne ne suka fashe da kuka, ni kuwa ba'acewa komai, haka na sakko daga bene kafin nagama sauka daga benen gidan mu, kan wata ta biyoni da gudu ta na kuka ta ce baya yaya Abdul Dan Allah kar katafi, haka ta fashe da kuka ta na kama akwati ta na ja Ina ja, sanna na dube ta na ce ki yi hakuri baby inshaAllah kamar yau zan dawo, ban gama rufe baki ba, sai ga Abban mu ya Tito ya daka mata tsawa haka ta naji ta nagani,bada San ran taba tasakar min jakar, haka na daga kai na nakalli mahaifina idanuna suka Dade cika da kwallah haka na jawad da kaina cikin sauri, haka na cigaba da sakkowa daga bene, a dai dai wannan lokacin haka Abban mu ya rufe baby da duka, duk da irin San da ya ke mata, haka ta tafi da gudu ta nufi falon Maman mu, haka nasakko daga saman bene ina jin kukan baby tare da daga muryar Abban mu a yiyin da ya ke fada, kafin na karaso bakin get din gidan mu gun a farfajiya na hango me gadin gidan mu, ya fito daga dakin sa, ya na kallona ya ce Abdul LAFIYA? Mekefaruwa? Haka na dube shi, idanuna na cike da kwallah nace babu komai kafin ya na rufe baki tuni Abban mu ya leko ta window ya na fada yana yiwa me gadi magana, ya yi hanzari ya budemin get domin baya bukatar ya sake ganina.

Ana cikin wanna hali Ashe sauran kannena suma sun leko ta taba suka kallona, kamar ance na daga kaina haka na Hangi sauran yan uwan kowannan su ya na kuka.
Dajin yadda Abban mu ya balbale megadin gidan mu da fada yasan cewar lallai balafiya haka ya dubeni cikin tausayawar sa gareni, jikin sa sanyaye haka ya budemin get sauran yan uwana suna kuka ita ko Maman mu, sakamakon Bacin rai, bata iya lekowa ba, ta na dakin ta na kuKa haka nasa kafata na fito, tun ma kafin naga ma fitowata DA sauran kayayyakina tuni a Abban mu ya rufe megadaiin gidan mu da fada ya yi sauri ya rufe kasa get.

Haka nafito na rasa ina ma zan nufa? Shakka babu da ace kamar da ne bazan yi tunanin inazan nufaba, Amman sakamakon yadda zuciyata ta samu tsoran Allah, bazan iya komowa gidan jiyaba.

Sabo DA nasan in dadene,kama tun daga abin da zanci nasha na kuma yi shittura nasan duk baza su Yimin wahala ba domin abokan mu Wanda na rabu da su, mata da maza sabo da shiryiwar ubangiji, yasan duk na rabu da su.

Tabbas nasan da cewar haka rayiwa ta ke domin yayan manzan Allah (sawa) anjarab ce su to wane ni. Haka a baro gidan mu ina tunanin ina zan nufa, wata zuciyar ta sauwalima me zai hana nakoma gidan jiya, sabo da yadda mahaifina ya nuna min gwara shiga ta duniya da sauran munanan ajiyuka da na aikata Abaya gwara shi, da ace na zama Dan shia, domin kun San Bacin rai babu abin da baya sawa, Amman sai dai na godewa Allah domin duk da irin sake_shaken zuciya take cikin ikon Allah nasami nutsuwa Wanda da ace nakoma ruwa gwara ace na shiga duk wahalar da zan shiga na shiga domin nasan da cewar jarrabawace.

Haka na taho ina tun tuni, domin ina tunanin ina zan je? Ana haka na yan ke shawarar bari na tafi dangin Maman mu ina haka kazaham sai naji wayata ta na ringing dubawar da zan yi sai naga Ashe jawad ne ke kirana, na yi sauri na danna abaddalin amsa kira ,jawad ya yi min sallama kafin na amsa ya ce dani ABDUL INA KASHIGA TUNJIYA IYAN KIRAN WAYAR KA AKASHE MEKE FARUWA HAKA? HAKA NACE DA SHI. BAKOMAI KO DA JIN YANYIN DA NA AMSA YASAN BA LAFIYA, YA CE KA NA INA YANZU NACE INA KAN HANYA
KAFIN NA KARASA YA CE DA ZUWA INA? NA CE DA SHI JAWAD ABBAN MU YA KORENI DA GA GIDA.
CIKIN SAURI YA CE DANI ME KACE........ ? YANZU KANA INA TO KAJIRANI INA ZUWA.
Zamu cigaba inshaAllah.

Ko yayq
Daga Shafin Ma'asumiya Nigeria news Updates
Daga Dan uwan Ku har kullum
®Habib Rabiu Nasrallah

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post