KAMANCECENIYAR IMAN ALI (A.S) DA SAYYID ZAKZAKY (H) !

Kayi Shere domin wasu su Amfana


Bayin Allah nagartattu na kowanne zamani za kaga an sami irinsu cikin zamanin da zai biyo su. To, anan za mu kawo wasu kamanni ne na wadannan bayin Allah salihai.

(1)- JARUNTA:- A zamanin Manzon Allah (S.A.W W) kakaf ba a sami wani jarumi cikin kowanne abu kamar Imam Ali (A.S) ba in ka cire Manzo (S). Hakama a wannan zamani, Sayyid (H) shi yafi kowa, domin babu wanda ke iya fadar gaskiya ga azzaluman mahukunta kamarsa ba.

(2)- ILIMI:- Idan ka cire Manzo (S), ba a sami wani mai ilimi cikin Sahabbansa kamar Imam Ali (A.S) ba. Haka zalika Sayyid (H) shi ya kasance zakara a wannan fanni, domin ilimi shine sanin haqiqanin hukunci tare da aiki da shi.

KARANTA SABBIN LABARAI:SHIN WAI YAUSHE UMAR YASAN DARAJAR YAR MACE NE??

(3)- KWARJINI:- A tarihin larabawan Makkah da Madinah, idan aka kira sunan Imam Ali (A.S) ga kafirai da azzalumai za kaga cikinsu ya duri ruwa. To, a wannan zamani Sayyid (H) shi ya zama barazana ga kafircin duniya, domin duk lokacin da aka ambaci sunansa sukan fada cikin firgici. Shi yasa ma suke qoqarin bin dukkan wata hanya don ganin bayansa.
(4)- QIYAYYARSU CIKIN ZUKATA:- Imam Ali (A.S) na cewa;
" Wata rana Manzon Allah (S) ya riqe hannuna muna tafiya cikin unguwannin Madinah, sai muka iso zuwa ga wani lambu, sai nace; yaa Ma'aikin Allah, wanne abu ne yafi kyau cikin wannan lambu? Sai yce;
" ABINDA YA FI KYAU CIKIN SA KANA DA ABINDA YA FI SHI CIKIN ALJANNAH."
Har dai muka wuce lambuna bakwai, kowannensu ina cewa;
" Me ya fi kyau cikin sa?" Yana cewa;
" KANA DA ABINDA YA FI SHI KYAU CIKIN ALJANNAH."

To, a lokacin da muka kebe hanya sai ya rungume ni,sannan ya fashe da kuka. Sai nace; Yaa Ma'aikin Allah, me yasa ka kuka? Yace;
" QIYAYYARKA CE KAWAI CIKIN ZUKATAN MUTANE (Sahabbai), AMMA BA ZA SU NUNA SHI GARE KA BA SAI BAYAN MUTUWATA."
(Nurul-Absar, Sh:129)
Kuma abinda ya faru kenan. Shi ma Sayyid (H) ya zama maqiyi cikin zukatan Hussadu, Fussaqu da Azzalumai na wannan al'umma.

Daga Ma'asumiya Nigeria news Updates
Tare da wakilinmu Ado Isah guda

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post