YADDA AKE BOYE FILE,KO VIDEO, PHOTO,APK,PDF A WAYAR ANDROIDS


Yan uwa barka da kasancewa acikin wannan Sabon darasi na Ma'asumiyya Nigeria News Updates tazo muku dashi,

Darasinmu na farko yadda ake amfani da android wajenyin aiki irin na computer manhajar android (androi operating system) takasance mafi farin jini azamaninnan fiye da sauran manhajoji kamar windows da blackberry da apple da sauransu wannankuwa yabiyo baya ne sakamakon budadden lasisin (open source licences) datazo dashi, wannan yananufin masu amfani da ita na iyasamun damar sarrafa ta fiye da yadda manufactura dinta suka bada dama ayau zamu tattauna akan hanyoyin da zakabi wajen boye abubuwa masu muhimmanci acikin wayarka ta android ta yadda kaikadai ne zaka samu damar budasu alokacin da kaga dama ba tare dasun lalace (corrupt) ba 1 zaka iya boye filoli na rubutu misali word document, pdf, text document, dasauran document din da suka kunshi rubutu ta hanyar canza musu extension dinsu zuwa extension da android bata dagawa misali .bat, .bvs, .pid.Wannan dika extensions ne da android bata dagawa sai computer. minene file extestion? file extension wani karine na digo da haruffa biyu ko fiye da haka agaban kowani irin file na waya ko computer dake taimakamusa wajen rarrabe ko wane file zuwa rukuninsa, haka kuma file extension yake taimakawa ko wane software ko application wajen gane irin nau'in file dinda zazu iya budewa misali kowa naganin.mp4, .3gp, .dat, .avi, dasauransu akarshen sunayen vidio file da garemu acikin wayoyin mu na android wannan shi ke taimakawa waya ta iya gane cewa wannan files din arukunin vidio suke dan haka daka taba su sai ta bijiro maka dukan wata manhaja da zata iya budemaka su kokuma sai kaga daka turo sabon vidio in kashiga vidio player kamar vlc ko mx player sai kaga sabon vidion a ciki ba tare da kasanyashi da hannun kaba wannan kuwa yafaru ne sakamakon file extension, haka abun yake aban garen audio player, da pdf reader da document reader da foto viewer da sauransu. Tunda yanzu munfahimci yadda wayar android take iya gane filoli ta kuma rarrabasu to sai muyi amfani da wannan damar wajen boye abubuwan mu na sirri daga gareta ta yadda bazata budesuba da kowane application kamar haka idan kana so kaboye takardu kamar cv da certificate da littafai da makaman tan su acikin wayarka ta android ta yadda koda antabasu wayar zatace baza iyabude wannan file din ba(can't open this file). >ka shiga 'file manager' >ka gano abinda ka ke so ka boye >ka danne shi tsawon second biyar za ka ga ya yi duhu alamun ka yi making dinsa
>daga nan ka danna option ko wasu digguna uku da za ka iya gani a kusurwar wayarka >daga jerin zabukan da za su bijiro sai ka za bi "RENAME" >zai kai ka inda za ka iya canza wa file din suna idan pdf ne zaka ga .pdf a kashen sunan >sai ka goge .pdf din kawai ka maye gurbinsa da .bat ko .pid ko .bvs da sauransu >sai ka danna "SAVE" zai bijiro maka da sako yana cewa za ka canza wa wannan file din yanayi wannan zai iya taba file din ka
kar ka damu kawai ka danna ok za ka ga file din ya zana kamar haka ka jarraba tabashi da nufin ya bude wayar za ta ce maka ba zata iya bude wannan file din ba(cannot open this file) ko kuma wani error message din shi kenan yanzu ba wanda zai iya ganin abin da ke kunshe a ciki kuma ba sai rubutuba ko hoto ko bidiyo ko audio guk in ka musu haka abun daya ne. YADDA ZAKA MAIDO DA FILES DIN DA KA BOYE TA HANYAR DABARARMU TA FARKO Bayan ka boye file dinka wata rana za ka iya bukatar maido da shi domin wa amfani yo ga hanyar da za ka bi kamar haka: >ka gano file din da ka ke so ka maido a cikin "FILE MANAGER" dinka >ka danne file din kamar yadda muka yi a baya >ka danna option ko digguna uku a kusurwar wayarka >daga zabukan da suka bijiro zabi "RENAME" sai ka cire .bat ko .bvs ko kuma .abunda ka sanya sai ka maida masa extension dinsa na asali >danna save ka danna ok shi kenan. SHAWARA Za ka iya manta asalin extension din file idan ka aje shi na tsawon lokaci to amma ta yaya zaka tuna? Ga amsar tambayar nan, idan ka zo wajen canza extension din misali my cv.pdf maimakon ka cire .pdf din sai ka barshi kawai ka kara wani extension din a gaba, misali "MY CV.pdf.bat" to duk lokacin da za ka maido shi sai kawai ka cire karin kawai shikenan. 2 HANYA TA BIYU
A nan zamu tattauna wasu muhimman hanyoyi da za mu iya boye files kamar bidiyo idan kana so ka boye shi a cikin wayayar ka ta android da wani applicacion mai suna "Private,Photo,Vedio Locker" shi wannan application din yana da abubuwa da yawa a cikinsa za ka iya sanyawa hoto ko video password kai kadai ne kasan abinda ka sanya dan haka kai kadai za ka iya bude abunka budu da kari ba iya nan abun ya tsaya ba shi wannan applicatin din ya na kulle saonni (messages) da kuma sauran applications da zarar ka sanya password dinka sai kawai ka zabi iya abubuwan da ka ke so ka kulle duk sai ka yi musu tick ka danna ok shi kenan ka boye abubuwanka .Wannan hanya ta fi waccan ta sama sauki sakamakon bata bukatar ka bata lokacinka wajen wasu rubucu rubuce.Domin saukarda wannan manhajar dannaNan YADDA ZA KA BUDE FILES DINKA A DUK LOKACIN DA KA GA DAMA Kamar yadda mu ka yi bayanin yadda za mu boye files dinmu a cikin wayar mu ta android ta hanyar amfani da PRIVATE PHOTO, VEDIO LOCKER to yanzu kuma ya kamata musan yadda za mu maido da su a duk lokacin da muka shirya. Domin yin hakan kuwa idan ka shiga application din sai ka sanya password dinka zai nuna maka files din da ka kulle sai kacire duk wani tick din da ka yi musu a lokacin da za ka kullesu sai kuma ka yi saving ka fito za ka ga files dinka sun dawo yadda suke a da. 3 HANYA TA UKU
Za ka iya biye files dinka ta hanyar sanya musu zi wannan da bara ita ce zipping da turanci, anan za ka yi amfani da wata manhaja mai suna File zip, unzip tool wanda za ka iya down loding dinsa a playstore kaitsaye. Shi wannan apllication din ko manhajar na dauke da zabi biyu na farko shi ne ZIPMAKER anan za ka danna kan zip maker sai ka zabi files din da ka ke so ka sanya cikin zip din daga nan sai ka danna OK shiknan za su tattaru cikin zipfile dada nan ba za su ganu ba har sai ka cire musu zip din.
Sannan kuma shi wannan application din yana da zabi na biyu mai suna ZIPETRACT
idan kana so ka cire wa files dinka wannan zip din sai ka danna kan ZIPEXTRACT daga nan sai ka zabi file dinka da ka ke so ka cirewa zip sai kadanna OK ka jira ya gama aikinsa shikenan ka kammala.Domin saukar da wannan manhajar dannaNan
Wannan shi ne abinda ya sawwaka a yau sai dai nan gaba kadan za mu kawo muku wani sabon Android tutorial din idan kana da tambaya ko karin bayani kayi comment a kasa sannan kuyi download din Application dinmu dake gefen Dakar wannan shafin, 

SANARWA----Muna koyar da Darussa da dama ga masu bukata daga ciki Akwai , Yadda zaka kirkirar Application da kanka da wayar Android, yadda zaka Gina wapsite ko wab desing da kanka, yadda zakayi Haccing din Facebook Account DSS yadda zakaga kiran da skayiwa budurwarka ko sakunan da skatura mata ko WhatsApp chart ko Facebook chart DSS.. Duka muna koyarwa gamai bukata sai yayi mana magana ta WhatsApp ta wannan Number 08149993999 ko yakira wannan 07058482032 Sai munjiku... Anan zamu tsaya  sai kun ji mu a wani tutorial di, domin yin tambaya ko sharhi ko tsokaci sai ka yi comment a kasa Mu huta lafiya sai kun sake jin mu a wani tutorial din nan gaba.

Kada Ku manta kuna tare da Shafin Ma'asumiya Nigeria News Update tare da Wakilinmu Mas'udu Dan Masani Shinkafi 08149994999

4 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

  1. Muna godiya Maasumiya kan wannan sadaukarwa da kukeyi wajen ganin kun wayarda kan al'umma da ilimomi daban daban akan waya da computer, Allah ya kara daukaka .

    ReplyDelete
  2. Rise Of The Lycans do have some great fighting scene between the werewolves and the vampires, it is a nice movie:: Tiktok 18+

    ReplyDelete
  3. Adobe Photoshop likewise has apparatuses that will actually want to assist with tidying up an image or even work on its appearance.
    shadow creation service

    ReplyDelete
Previous Post Next Post