daya daga cikin manyan APC a cikin Kudancin Najeriya, Ganiyu Johnson ya bayyana cewa Shugaban Kasa Buhari zai yi wa Atiku fintinkau a zaben 2019. Johnson yace APC ce za ta lashe zaben da za ayi a sabuwar shekara.
Tsohon kwamishinan ayyuka na Jihar Legas, Ganiyu Johnson ya bayyanawa ‘Yan Jarida cewa babu yadda Atiku Abubakar zai yi da Buhari a 2019. Johnson yace ko da Buhari bai tsaya muhawar da PDP ba, zai yi nasara hankali kwance.
Tsohon kwamishinan yace a Najeriya jama’a ba su damu da muhawarar zabe ba. Johnson ya kuma ce adadin Kananan Hukumomin da ake da su a Jihar Kano da Jigawa kurum sun zarce yawan duka Kananan Hukumomin Inyamurai.
Babban ‘Dan siyasan na Legas wanda yanzu yake neman kujerar Majalisa yace ba za a iya gane wanda zai yi nasara a zabe wajen mukabala ba, a cewar sa akwai ‘Yan kauye da Mutanen da ke kasuwa da babu ruwan su da wani dogon surutu..
Ganiyu Johnson wanda aka fi sani da GAJ dai yace babban abin da ke cin zabe shi ne yi wa al’umma aiki.
Kwanaki ne Johnson yayi murabus daga mukamin sa domin ya nemi kujerar Majalisar Tarayya na Yankin Oshodi Isola II na Legas..
___________________
Ma'asumiya Nigerian 🇳🇬 News Update,
Wakilinmu;
👇🏽
Mahadi Tukur Almizan
DE YOUNG ACTIVIST
Tags:
Labaran Duniya