TSARI NA ADALCI NE ZAI IYA TSAYAR MANA DA SHUGABANNI MASU ADALCI



"Ya kamata mu sani cewa; wannan ba shi ne zai kai mu ga gyara ba. Kuma ko da za a ce misali mutane duk su ce wai Babangida ya sauka, idan ya sauka wani wanda ya fi shi zalunci zai hau. Tunda haka al'amarin ya kasance. Lokacin Shagari, mutane suna ta cewa Shagari ya sauka. Yana sauka Buhari ya zo. Kuka ce kayya kayya ai gara Shagari. To bayan an kau da Buhari, to yanzu kuma ana cewa gara Buhari. To idan ma yanzu Babangida ya kau, sai an ce ina Babangida? Kamar mota ce ta rigaya ta lalace, sai ka ce ai direban ne bai iya ba, ka cire wannan ka sanya wancan. To idan ba ka gyara motar bace, babu yadda za a yi ta koma daidai, saboda ainihin lamarin ba direban bane, motar ce. Don mu gane, dole sai tsari na adalci ne, zai iya tsayar mana da shugabanni masu adalci. Saboda haka ya zama kokarinmu shi ne mu tabbatar da tsari mai adalci. Dole kuma da ma tsari mai adalci sai shugabannin masu adalci."

Wani yanki daga cikin jawabin Pre-hudba, wacce Shaikh Ibraheem Zakzaky ya gabatar a Masallacin Juma'a na ABU, Zariya a farkon watan Mayun shekarar 1992 (28 ga Shawwal 1412).

Daga Shafin Jawaban Shaikh Zakzaky
_____________________
Daga wakilinmu:
Mahadi Tukur Almizan

DE YOUNG ACTIVIST

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post