SOJOJIN NAJERIYA SUN KAI HARI KAN MASU ZANG_ZANGAR LUMANA A ZAMFARA

______Mutanen garin Kucere da Tsafe sun rufe babbar hanyar Zariya da zai kai ka har zuwa Gusau har Sakkwato, mafi yawan wadanda suka yi hakan, mutanen da suka gudo daga kauyakunsu ne sakamakon ta'addancin da ake musu ba dare ba rana. Wadanda suka tare hanyar sun ce sun yi hakan ne domin jawo hankalin gwamnati akan yadda kashe-kashe, garkuwa da jama'a yake ta 'kamari a jihar Zamfara a kwanakin nan, amma kamar ba gwamnati a kasar. Sun ce: maharan haka suke shiga kauyakunsu gaba-gadi ba tare da wata barazana daga jami'an tsaro ba, su kashe su, su kona dukiyoyinsu, su tafi da matayensu. 


Sun yi kira ga gwamnatin jiha da na tarayya akan lallai fa da su dau matakin da ya dace, domin da alama kashe-kashensu da ake yi a kowacce rana karar da su ake nufin yi ba tare da an ankare ba.

-AMR

__Suna cikin wannan zanga_zanga ta Lumana kwatsam sai jami'an  sojojin najeriya suka dira akansu, sunyi harbin kan mai uwa da wabi sunkashe mutanen sama da hamsin sun jikkata wasu da dama,
___________________________________
Ma'asumiya Nigerian News Update;
Wakilinmu;
    |
Mahadi Tukur Almizan
DE YOUNG ACTIVIST

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post