JAWABIN SHEIKH YAQUB YAHAYA NA TARON TUNAWA DA WAKI'AR ZARIYA TA 12/12/2015. NA HARISAWAN AZZAHRA [A S] ZONE KATSINA 22/12/2018.




Bayan godiya ga Allah da Salatin Manzon Allah da Iyalan gidansa. Sheik Yaqub Yahya ya fara gabatar da Jawabi akan Waki'ar Zariya ta 12/12/2018.

 Sheik Yaqub ya fara da cewa "Tabbas wannan Waki'ar ba wai bamu san da ita ba ne a'a, mun san da ita, sai dai bamu san yaushe zata zo ba, wane hali zata zo dashi, yaushe zata kare shi ne bamu sani ba!, tabbas dukkan wanda ya kama wannan tafarkin na Allah yana tattare da Jarabawa ta ciki da ta waje kala-kala".

Jarabawar nan Allah kadai yasan mi yake nufi a kan ta, wani har a gama wannan Waki'ar ko ciwo ba zai ji ba, wani ko gidan Yari ba zai je ko so daya ba! amma Allah zai Jarabceshi da wata nau'in Jarabawa.

Allah ya kawo mana Waki'a kuma ya kawo mana natsuwa acikin ta akan abin da ya kamata muyi, tabbas an Zalunci Malam Zakzaky Zalunci na karshe wanda ba'ataba yima wani irin wannan Zaluncin ba! ko a cikin Tarihi sai Imam Husain (A.S) daga shi, sai Malam Zakzaky.

Zaluncin da aka yima Malam Zakzaky H a wannan karnin babu wanda aka taba yi ma irinsa a doron Duniya, bamu sani ba ko a yakin Jahiliyya, amma a Muslunci bamu taba jin irinsa ba.

Ita Mutuwa umurni ne na Allah, duk kan wanda kwanan sa ya kare shi zai mutu, Shahada zabin Allah ce sai mai Rabo ke samun Shahada.

Sheik Yaqub Yahaya Wakilin 'yan uwa Musulmai Almajiran Sayyeed Ibrahim Zakzaky na Da'irar Garin Katsina. Ranar Asabar 22/12/2018, wajen Taron tunawa da Waki'ar Zariya ta shekara ta 2015, wanda Harisawan Azzahra [S A] Zone suka shirya a Markaz Katsina.
_________________________________
Ma'asumiya Nigeria News Update tare da : Isma'il Abubakar Idris Katsina.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post