Ma'aikatan Majalisar tarayyar Najeriya🇳🇬 Sun shiga yajin aiki,


Labarin da ke iske mu yanzu yanzu da dumin sa shine na rufe majalisar tarayyar Najeriya da mafusatan ma'aikatan ta suka yi da sanyin safiyar yau tare da hana shiga da fita.

ma'aikatan suna kukan rashin biyan su albashi da sauran hakkokin su da aka tauye masu na tsawon watanni.


Tun Asabar nedai kungiyar ma'aikatan na majalisar suka fitar da sanarwar far yajin aikin,

Shugaban Kungiyar, Bature Mohammed, cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, ranar Asabar, ya ce sun yanke shawarar hakan ne bayan wani taron gaggawa da suka yi a ranar 14 ga watan Disamba.

Ana sa ran Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudinsa na 2019 ne a wani zaman hadin gwiwa a tsakanin Majalisar Dattijai da ta Tarayya a ranar Laraba 19 ga watan Disamba.

Mohammed ya ce, yajin aikin na, ‘a tauna tsakuwa domin aya ta ji tsoro,’ da za su yi, zai kai har zuwa ranar 20 ga watan Disamba, domin neman a biya masu wasu bukatu na su.

Shugaban ya shawarci daukacin ma’aikatan Majalisun da su kaurace wa bakin aikin na su a tsawon wannan lokacin.

A ranar 4 ga watan Disamba ne, ‘yan kungiyar suka rufe Majalisun, a lokacin da suka hana ‘yan Majalisun zama a cikin Majalisun.
Daga cikin bukatun na su akwai, samar masu da sabon tsarin aiki, yi masu karin girma da kuma a biya su kashi 28 na karin kudin albashi da aka yi a kasafin kudin 2018.
    ___________________
Ma'asumiya Nigerian 🇳🇬 News Update,
Wakilinmu;
      👇🏽
Mahadi Tukur Almizan
DE YOUNG ACTIVIST

Mon, 17/12/2018

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post