BAHASI AKAN ZALUNCI

BAHASI AKAN ZALUNCI

__________________________

ZALUNCI: 

Allah Yace ""Na Haramta Wa Kaina

Zalunci Kuma Na Sanya Zalunci Ya Zama Abin

Haramtawa A Tsakanin ku""-Hadith

Sabawa Shari'ar Allah Da Koyarwar Manzon Allah

(Annabi Muhammad S.a.w.w) Shine Asalin

"ZALUNCI".

-Kashe Rai Ba Tare Da Wani Hakki Na Shari'ahba

Zaluncine

-Cin Dukiyar Maraya Zalunci Ne

-Cin RIBA Zalunci Ne

-Kin Biyan Bashi,Alhalin Kana Da Ikon Biya

Zalunci Ne

-Fifita Wata Ko Wasu Daga Cikin Matanka Akan

Wata Ko Wasu Zalunci Ne

-Tauye Mudu Zalunci Ne

-Cinhanci Da Rashawa Zalunci Ne

-Magudin Zabe Zaluncine

-......

Shin Ko Kunsan Zalunci Duhune Ranar

Alkiyama ?

Shin Ko Kunsan ZALUNCI 'Yana Daya Daga Cikin

Abu Hudu Da Annabi S.a.w Ya Nuna Mana Cewa

Babu Wani Abu Da Yafi Cancanta Allah Ya Kama

Bawa Dashi Kamar Su' ?

Mun Sani Ko !!! To Me Yasa Muke Aikata

Zalunci ?

Ya Zama Wajibi Akaina

Ya Zama Wajibi Akanka

Ya Zama Wajibi Akanki

Ya Zama Wajibi Akan Mu Gaba Daya Mu Gyara

Halayenmu,Mu Nesanci Zalunci Komai

Kankantarsa.

Allah Ka Tsaremu Daga Kafurcewa Shari'o'inKa.

Allah Ka Sanyamu Daga Cikin BayinKa Salihai.

Allah Ka Rabamu Da Zalunci Da Dangoginsa.

._______________________

Ma'asumiya Nigeria🇳🇬 News Update

Wakilinmu:

Mahadi Tukur Almizan

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post