ALMAJIRAN MALAM IBRAHIM YAQUB ALZALKZAKY SUNYI ZANGA-ZANGAR LUMANA TA KIRAN ASAKAR MASU JAGORANSU

ALMAJIRAN SHAIKH IBRAHIM YA'AQUB AL'ZAKZAKY SUN GUDANAR DA ZANGA ZANGAR LUMANA A GARIN ABUJA.

_______________________


Yan uwa Musulmai Almajiran Malam Ibrahim yaqub Alzakzaky, Sun Gudanar da Zanga zangar Lumana yau Litinin 10/12/2018 a Garin Abuja.

Sunyi wannan zanga-zanga ne a cigaba da kiraye-kirayen da ake ma gwamnatin najeriya akan tasaki Shaikh Zakzaky

Sunfara Wannan Zanga-Zanga ne a Maitama dake tsakiyar babban birnin na Abuja,

Bayan zazzagayawa da sukai,

Sun kammala Zanga-zangar a bakin ofishin kare  hakkin dan adam [human-right office] dake maitama Abuja,


Engineer Abdullahi Musa ne ya gabatar da jawabi a wurin daga bisani kuma daya daga cikin Matan  da aka yima rauni A kwanakin baya a lokcin da sojoji suka kaimasu hari lokacin dasukai tattaki, Ta bayyana gaban wakilin da ya fito dan amsar takardun da yan uwa suke dauke dashi na koke Malama Hannatu Basiru da hannunta ya yanke bayan Harbin da Sojoji suka mata a Karo Bridge Nyanya Abuja.


Sheikh Muhammad Abbari ya gabatar da jawabin rufewa ya kuma yi addu'a aka sallami kowa.


Anyi Lafiya Ankammala Lafiya

_________________________

Ma'asumiya Nigerian🇳🇬 News Update.

Wakilinmu;

👇🏽

Mahadi Tukur Almizan

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post