Lalle Imamai(AS) sun yi jihadi wajen nesantar da duk wanda ke da alaka da su daga taimakekeniya da azzalumai, sun kuma tsananta wa mabiyansu game da tafiya tare da ma’abuta zalunci da ja’irci da cudanya da su. Abinda aka ruwaito daga gare su game da haka a wannan babin ba zai gididdigu ba, daga ciki akwai abinda Imam zainul abidin (A.S.) Ya rubuta zuwa ga muhammadu bn muslim azzuhuri bayan ya gargade shi game da taimakon azzalumai akan zaluncinsu?
Ashe kiransu gare ka yayin da suka ba su sanya ka dan dutsin nika suna juya zaluncinsu da kai ba .da kuma bango da suke ketarawa ta kanka zuwa bala’insu mai da tsanani na bi ta kai zuwa batansu mai kira zuwa ga zaluncinsu, mai shiga tafarkinsu, suna sanya shakku da kai a zukatan malami, kuma suna jan zukatan jahilai da kai zuwa gare su.waziransu da mafiya karfinsu da mataimakansu ba su kai inda ka kai ba wajen nuna ingancin barnarsu, da shiga da ficen kebatattunsu……………………ka diba zuciyarka domin ba mai dubata baicin kai ka yi mata hukunci, hukunci irin na mutum abin tambaya.
Girman kalmar Ka yi mata hukunci hukunci irin na mutum abin tambaya” ya yawaita. mutum yayin da son ransa ya gallabe shi sai ya mance darajarsa da ke tare da Shi da sirrin karamarsa, wato ma’ana ya ji cewa Shi abin tambaya ne game da ayyukansa, kuma ya kaskanta abinda zai gudana daga ayyukansa sa’an nan kuma ya raya cewa, shi ba shi ne wanda za a yi masa hisabi ba a kan ayyukasa, wannan na daga cikin asirran zuciyar mutum mai umarni da mummuna. Don haka imam ya so ya fadakar da Zuhuri game da wannan sirri na zuciya wada yake kunshe a cikinsa don kada wahami ya yi galaba akansa har ya yi sakaci game da abinda yake kansa game da kansa.
Mafi zurfi game da haka kuma da suranta haramcin taimakekeniya game da azzalumai shi ne maganar safwan jammal tare da Imam Musa Kazim (A.S.) wanda Shi ya kasance daga cikin mabiyan Imam din ne, masu ruwaito hadisi daga gare shi wadanda aka amince da su Ya ce: kamar Yadda ya ruwaito a littafinsa na Ilimin sanin masu ruwaya kamar yadda yake bayanin rayuwar Safwan:
Na Shiga gare shi sai ya ce mini: “Ya Safwan duk wani abu daga gare ka kyakkyawa ne mai kyau in banda abu guda daya.”
Na ce: A sanya ni fansa gare ka, wane abu?
Ya ce: “Ba da hayar rakumanka ga wannan mutumin wato Harunar Rashid.
Na ce: Wallahi ni ban ba shi haya ba ina mai alfahari ko dagawa ko don farauta, ko wasa, sai dai na ba shi haya ne don wannan tafarkin wato don hanyar Makka kuma ba na daukarsa ni da kaina sai dai ina tura shi da barorina.”
Ya ce: “Ya Safwan kudin hayarka na kansu?”
Na ce: E, a sanya ni fansa gare ka.
Ya ce: “Shin kana so su wanzu har su dawo su biya ka kudin hayarka?”
Na ce: “E”.
Ya ce: “To duk wanda ya so wanzuwarsu to yana tare da su, duk wanda ya kasance tare da su to ya kasance mai shiga wuta.”
Safwan ya ce: “Sai na tafi na sayar da dukan rakumana baki daya.”
Idan har son rayuwar azzalumai da wanzuwarsu a kan wannan matsayin yake, to yaya kuma ga wanda yake hada kai da su a kan zalunci, ko kuma yake taimaka musu a kan ja’irci, kuma yaya halin wanda yake shiga cikin jama’arsu ko kuma yake aikinsu ko kuma yake shiga tawagarsu, ko kuma yake bin umarninsu?
________________________
Ma'asumiya Nigerian🇳🇬 News Update;
Wakilinmu;
Mahadi Tukur Almizan