Daga Shading Ma'asumiya Nigeria News Update
Mu Dauko AlQur'aninmu mu Ajiye A gaban mu, Mu duba Acikin (Suratul Ibrahim:42) Allah (t) yana Cewa:
"Kada ka tsammaci Allah mai sha'afa ne game da abin da azzalumai suke aikatawa, sai dai kawai yana jinkirta musu ne saboda ranar da idanuwa zasu zazzaro".
Acikin littafin Nahjul balaga huduba ta 219: Imam Aliy (as) yana Cewa: "Wallahi idan da za a ba ni Sammai bakwai da kuma abin da yake kasan falakinta, a kan in saba wa Allah game da tururuwa da in kwace mata Sha'irin da ta jawo, ba zan aikata ba".
Wannan shi ne matukar abin da mutum zai iya surantawa game da kame kai da tsoratarwa daga zalunci da kyamar yinsa.
Shi ba zai zalunci tururuwa ba a kan kwayar sha'ir koda kuwa an ba shi sammai bakwai, to yaya halin wanda yake zubar da jinin musulmi, yake handame dukiyoyin mutane, yake cin Mutuncin Su??
Kuma Wannan ita ce tarbiyyantarwar Ubangiji da addini yake bukatar ta daga kowane mutum.da Wannan Tarbiyyar Sayeed Zakzaky (h) ya Tarbiyantar da Almajiransa inda ya koyar damu dako Tarmani, ko ince kiyashi yacijemu to mu dauke shi mu ajiye a gefe yawuce abinshi.
Balle wasu tsinannin Allah suce muna dauke da ababe masu fashewa harda kokarin kwace motar makamai......
Illahy ya ninka Bala'o'in da Mutun bazai iya daukaba ya Dorasu da General Buhari tare daduk mai sa Hannu wajen kisanmu,kamunmu, ko Murna akan Abunda akayi mana Don Girma da Matsayi Martaba Na Manzon Allah (Saww).