YADDA ZAKA DAWO DA SAKONNIN WHATSAPP DINKA


Akwai da yawa daga cikin mutane da kan bukaci canjin waya lokaci zuwa lokaci, wasu kuma formmating ko kuma restore suke bukatar yi ma wayarsu (saboda wani dalili), babban abin da kan zo musu a rai shine, yadda zasu rasa duk wasu messages ko kuma chats dake a cikin whatsapp dinsu. Wasu mutanen zaka ga sun tara dubban messages a cikin whatsapp din su wadanda kuma ajiyarsu tana da matukar amfani a garesu. A cikin wannan kasidar, mun kawo muku hanyoyin da zaku domin yin transfer din message dinku zuwa ga wani wajen na daban kafin ku siyar da ita ko kuma kafin ku yi formatting dinta, da kuma yadda zaku iya maido da messages din a yayin da kuka canja wata wayar.
Farko domin fitar da messages dinka sai ka bi wannan haryar:
1. Ka fara cire whatsapp din (wato kayi Uninstalling din shi)
2. Ka shiga cikin kan wayarka (idan nan ne kayi installing din whatsapp)
3. Sai ka gano foldar Whatsapp
4. Kayi kofin wannan foldar ga baka dayanta ya zuwa wani wajen (zaka iya amfani da computer ko kuma ka tura ma wata wayar ta hanyar Xender)
Idan kuma ka canja wayar, ko kuma kayi formatting din, sai ka bi wadannan hanyoyin domin maido da messages din ka.
1. Ka fara installing whatsapp din
2. Sai ka turo wannan foldar whatsapp da ka ajiye a wani gurin (kana iya sanya ta a kan memory dinka)
3. Sai ka shiga cikin foldar Whatsapp din ka yi installing a cikin wayarka (ba wacce ka turo din ba), ka goge duk wani abin da ke cikinta
4. Sai ka je cikin foldar Whatsapp din ka turo kayi copying din duk wani abu da ke cikinta, sai ka je cikin foldar wannan Whatsapp da kayi installing (cikin wayarka) ka sanya su.
5. Da zaran kayi wannan sai ka je ka shiga cikin whatsapp dinka.
6. Da ka shiga zaya nuno maka cewa akwai wasu kaya da ke cikin wannan folda taka, kana bukatar maido da su? Sai ka zabi Next.

Da zaran ka kammala wannan mataki na 6, zaka ga Komai naka na da ya dawo kamar Scan baya.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post