Sakon Shek Zakzaky_ KAYI AIKIN DA YA RATAYA A WUYANKA DON ALLAH

KAYI AI
"muhimmnin abu, kai ka zama kana yin aikin da ya rataya a wuyanka kuma ka yi saboda Allah. Wannan muhimmin abu ne. Ka yi don Allah.” Ya jaddada. Sannan ya ci gaba da cewa; “karka damu da sukan mai suka, kar sukan mai suka yasa ka bari, in haka nan ne, ya zama ba kana yi don Allah ba ke nan. Idan wani ya soke ka, ka ce; tunda abin haka nan ne, ka bari, to, dama kana yima wane ke nan? Shi kake yi ma ke nan. Amma in kana yin abu dan Allah ne, sai wani ya soke ka, ina ruwanka. Ya yi ta sukan ma man. Karka damu da mai soke-soke, dabi’ar mutane ne, in dai an hadu sai an yi wannan. Dabi’ar mutane ne, ba yadda za a yi ka raba su da wannan, amma almuhim ya zama kana yi dan Allah.”
https://maasumiya.blogspot.com

Cewar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a lokacin da yake rufe taron Harisawa na kwanaki biyu a kan; kyautata alaka a tsakanin harisawa da wakilan Harka da wakilan 'yan uwa a muhallin Husainiyyah Bakiyyatullah.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post