TUNATARWA DAGA SHAIKH ZAKZAKY

*TUNATARWA DAGA SHAIKH ZAKZA

In kana karatun salla, lalle ba bukatar ka sa sifika mutanen gari su ji kana karatu

“Kada ka bayyana sallarka, kuma kada ka boye; ka bidi baina-baina tsakanin wannan.” (Isra’i: 110) Kai ba mai daga murya ba a yayin da kake salla ke nan. Kar ka daga sautinka yayin da kake salla, kuma kar ka boye ta yadda kai ma ba ka san mai kake karantawa ba. Ya zama baina-baina.

Nan mai sharhi ya kawo cewa, an ruwaito daga Imam Ja’afarus Sadik, dangane da tafsirin wannan ayar, ya ce, bayyana murya shi ne dagawa, boyewa kuma ko kunnenka ma ba ya ji, ba ka jiyar da kanka ba ke nan. Ka yi karatu tsakanin biyun nan. Ba ka daga murya, ba ka boyewa.

Fassarori daban-daban, amma wanda aka tafi a kai a kan sallah ne. Kira’an salla a inda ake bayyana karatu, akwai ladabi na komai, akwai ladabi na bayyana karatun. Ba ana rara murya ne in ana karatun ba, sawa’un kai kadai kake salla, ko kai Liman ne. In kai kadai kake salla, za ka jiyar da kanka ne, ba kana jiyar da gari ba ne. Haka zalika in kai Liman ne, mustahabbi ne ya zama akalla wasu sun ji karatunka ko yaya. Amma duk da haka bai zama lazim ka rara murya kowa ke bin ka ya ji ba.

Bai zama lazim alal misali a masallaci babba, ya zama har na sahun baya sai ya ji ka ba ko na waje. Abin da ya zama lazim akalla wasu suna ji, ko da wadanda suke bayanka ne, ko da mutum uku ko hudu da suke bayanka ne. Sauran mutane idan sun ji murya, amma ba su ji tangaran me kake karantawa ba, amma suna ji, to ya wadatar.

Sauran kuma wanda bai ji ba sam-sam, bayaninsa na cikin littafin fikihu. Za ka ga cewa idan kana jin karatun Liman, lazim ka yi shiru yayin da yake bayyana karatu. Haka zalika ko ba ka jin abin da yake fadi, in kana dan jin alamar sauti-sautinsa, ko da ba ka san me yake karantawa ba, lazim shiru za ka yi, ba za ka karanta komai ba.

Amma babu bukatar daga murya wajen karatu na sallah. Akwai ruwayoyi daban-daban, wasu suna cewa wannan ya faru ne a Makka, in Manzon Allah yana salla, in suka ji muryarsa sai su cutar da shi, shi ne aka ce ya sassauta. Amma wannan lallai ladabin yana nan a kowane lokaci har yanzu kuwa. Ladabi ne da Alkur’ani ya koyar da mu, kuma sunna ta koyar da mu cewa ba a daga murya in ana karatun salla.

*Don Allah Malam wa kake wa sallah?*

Yanzu muna wani zamani wanda yanzu ya zama wani yayi kuma. In ka yi magana, sai ya ce ya gani a kasar waje haka ake yi, ba a littafi a rubuce ba. Yanzu mutane suna sa sifikoki su cika gari da ihu, wai suna karatu, har da tsakar dare, wai suna tahajjud. To, tambaya: Don Allah Malam wa kake wa sallah? Kana wa mutanen gari ne? Mene ne na sa sifika da karfin tsiya ka rara murya, duk gari na jin karatu, kana salla? Wa kake wa sallar? Allah kake wa? To, shi Allah din ne ya ce ma yana bukatar sifika don ya ji ka sosai? Ko ko mutanen gari kake wa?

In mutanen gari ne, ba ka bukatar ka yi wa mutanen gari sallah. Sallah ka tsaya gaban wane ne kana wa sallah? In dai Allah (T) kake bautawa, to ba ka bukatar mutane gari su ji kana karatu. Mutanen gari, akwai bukatar su ji karatunka? Ko mutanen unguwa, akwai bukatar su ji karatu, har da matan aure a gida? Su ji cewa ka iya kalkala da gunna da ikhfa’i da izhari. Akwai bukatar su ji ne?

In kana so ka koya musu tajwidi, sai ka ce akwai ajin tajwidi. In an gama salla, sai ka ce akwai ajin tajwidi, wanda yake so ya koya, ga Malam Saleh Mai kalkala ya iya. Saboda haka an bude sabon aji. Sai ka zo ka yi musu kalkalarsu a cikin aji. Ka kalkale yadda ka ga dama, ka gunnance. Ka ga kana koya musu tajwidi ne.

Amma kana karatun salla, lalle ba bukatar ka sa sifika mutanen gari su ji kana karatu. Don ba mu san hikimar wannan ba. Me ake nufi da yin wannan? Ana bukatar mutanen gari su ji ne? Ko ko mutanen da suke sallar ne suke bukatar su ji? In mutanen da suke bin ka sallar ne su ji, sifikar cikin masallaci ta wadatar, banda na waje; ko shi ma ba a bukatar ka rara murya. Nakan ce wai meye ma’anar wannan sa murya da suke yi su cika gari? Har da kiran salla da ta da ikama shi ma da takbir din kowane ruku’u da sujada. Domin kiran salla yana da ma’ana. Ma’anarsa shi ne a kira mutane su zo masallaci, amma ba duk mutanen gari ba.

*Masallaci da aka sani a littattafai guda uku ne*

In masallacin unguwa ne, na ‘yan unguwarku. Don masallatai suna da ka’ida a shari’a. Masallaci da aka sani a littattafai guda uku ne. Masallacin kabila, shi ne masallacin unguwa, sai masallacin kasuwa wanda galiba akan hadu a ci kasuwa a bayan gari ne, yakan zama Azuhur da La’asar za su kama mutum a kasuwa, ba a ce lazim ya shigo gari ya yi salla ba, sai a yi masallaci a kasuwar. Wadanda suke wurin sai su halarci sallar. Sai kuma masallaci Jami’i, shi ne na gari, na Juma’a. Saboda haka masallatai iri uku ne.

Masallacin kabila yakan zama abin da aka saba guda daya ne, haka nan masallaci Jami’i na gari guda daya ne, haka yake a ka’ida. Amma yanzu sai ka ga mutane ko’ina sun yi su barkatai. Tun tsakar dare an rika kwantsama kiran salla har gari ya waye. Wasu ma sai su sa kaset, ko su sa karatu ko wa’azi. A irin haka nan ne a Jos, sai su ma kiristoci suka rika sakawa, sai suna zagin Allah da Annabi da Alkur’ani da musulmi a cikin nasu kaset din. Ya zama hayaniya kawai.

Ni ban san hikimar rara murya a sifika ana karatun Alkur’ani ba. Ana yin salla, ana yi wa wane? Ka san akwai walakin ko? Takan kai ma wani lokaci ma, na ciki ba ya ji, amma na waje can yana ji, to wa ake wa karatun? Na wajen. Lalle lazim su ake wa. Kawai shi dai yana so ya gwada cewa shi ya je ya koyi karatu. Ya ja wasu ayoyi, ya rika kalkalewa, a ce kai! Hala Salele ne? A ce ai shi ne. A ce in da Bala Mai kafiya ne da yanzu karatun ya fi haka nan, ya fi Salele.

In kuma ba shi ne niyyar ba, sai a gaya mana. In ba ana so a jiyar da mutanen gari ba ne, to a cire sifikoki a dawo da su nan cikin masallaci don a ji. Ikama da takbir duk su ma ana yi ne don wadanda suke nan su ji. Amma kiran salla akan yi don ‘yan unguwa su ji. Amma shi ma sai ka daidaita sifika din daidai jin wadanda za su zo su yi salla a masallaci din, ba don jin duk gari ba. Shi kuma na masallaci, daidai jin masallaci din. Hatta na jin masallacin bai zama lazim ba.

Ba a ce in kana salla ka rara murya ba. Rara murya ma in ya kai wani mikdari yana iya muni. In ya yi muni sai ya zama ka yi abin da aka hana ka. Ba a bautan Allah da abin da ya hana. Duk lokacin da ka bauta wa Allah da abin da ya hana ka, to ba za a karba ba. Duk abin da ka ji an ce maka kar ka yi, to ba za ka yi ne ya zama ibada ba. Tambaya: Ana iya bauta wa Allah da abin da ya hana? Amsa: A’a. Duk abin da aka ce maka kada ka yi, ba za ka yi shi ya zama ibada ba. Tunda an hana ka daukaka murya a karatun salla, to in ka rara muryarka lalle ka bata al’amari, tunda ka yi abin da aka hana ka.

*Wannan wani bayani ne da Shaikh Ibraheem Zakzaky ya yi lokacin da yake tafsirin aya ta 110 a cikin Suratu Isra’i. Ibrahim Musa ne ya nakalto muku.”*

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post