KAFIN KISAN TA'ADDANCIN SOJOJIN NIGERIA A ZARIYA; Shek Zakzaky (h) ya Bayyana cewa;



Daga Shafin (M.N.N.U) (Ma'asumiya)


"Dazun abin da aka ce mana; an tara Sojoji a sansaninsu, an ce musu; Al-Zakzaky zai yi bore, saboda haka su zama cikin shiri komai na iya faruwa. To, me ya kawo sunan Al-Zakzaky kai da kake ‘training’? Kuma in ya yi bore, ina ruwanka da Boren? Na dauka idan ma wani abu ne, ba aikin ‘yan Sanda bane? Sai dai in Dan Sanda ya
gayyaceka ka taimaka masa, amma Soja da Bindiga an ce mishi Al-Zakzaky zai yi bore ya zama cikin shiri, komai na iya faruwa. Wannan abin da aka gaya musu dazun ke nan. Kuma aka ce su rike Bindigoginsu, yanzu haka Bindigogin na hannunsu, kuma suna nan yanzu cikin shiri.
"Kuma sun shigo Motoci ne ba kadan ba. Tun kwanaki suna ta shigowa (Zariya), har da inda aka ga Mota Goma da Turawa zalla, sun shigo sun je Basawa, shekaranjiya wancan. Kuma yanzun Mota goma, Mota 20 duk suna shiga. To, kuma duk ba za mu damu ba. Amma me ya kawo sunan Al-Zakzaky? Da yake shi Soja ana mishi tarbiyyah ne da cewa; su mutanen gari sune abokanan gabansa. Shi za shi ya yi kisan kai ne kawai.
"To, wala Allah su zama cikin shiri, kila sun shirya suna da wani ‘unit’ wanda zai sa bakin kaya, yaje ya yi ta’addanci, suce; to, ka gani, dama mun gaya muku. Daga nan kuma sai su shigo gari, su shiga kisan kai. Ganin cewa; abin ya bayyana an san shirin su, bai damu Magidantansu ba, amma kila ya dami su ‘agents’ din su na nan."

— Shaikh Ibraheem Zakzaky, a ranar 22 Almuharram, 1436 (2014).

*Daga Ma'asumiya Nigeria news updates*
Dan Masani 08149993999

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post