Acikin Shirin Kaddamar da Gidauniyar ne |

Kungiyar da Shararriyar Yar TikTok dinnan take Jagoran ta a Fadin Jihar Wadda aka fi Sani da Rabi'atu Buzuwa.
A bayanin da Rabi'atu Buzuwa Ke ma Wakilin Shafin MA'ASUMAH ta shaida mana Cewa "An Kaddamar da Gidauniyar ne da nufin Taimakawa 'Yan Gudun Hijira Mata da Maza da Yara wadanda aka kashewa Mazaje, da Marayun da aka bari da Gajiyayyu da mararsa lafiya Dake Cikin Fadin Jihar, inda taci gaba da Cewa a Sannu Wannan Gidauniyar Zata fadada a Kowace local Government Dake Jihar da ma Wasu jihohin insha Allah.
Shafin MA'ASUMAH ya tattauna Da Wasu Daga Cikin Gajiyayyu da Wannan Gidauniya Ta taimaka inda ta bayyana yadda Sukaji Dadi da Farin Cikin yadda akayi SHARIY AL-ALAWY Yasan Dasu, tare da yiwa sharif Addu'a da fatan Alkhairy....
An Kaddamar Da Wannan Gidauniya Ayau Acikin Unguwar saminaka Dake Garin Gusau ta Jihar Zamfara inda aka Raba Abinci da Sauran ababe ga mabukata
Da karshe Anyi Addu'a ga Sharif Al-alawy da hotuna da Bidiyo ga Wakilan da suka Jagorancin Raba kayayyakin ga mabukata.
Ga Wani guntun Bidiyo ku kallah a kasa
👇
Mas'udu Dan Masani Shinkafi ✍️
Whatsapp 08149993999