ABINDA YAKE FUSKANTO MU!!! 01
A kowace rana Opportunities  na zuwa garemu waɗanda ya kamata muyi amfani da su wajen baiwa wannan gwagwarmaya gudummawa, amma sam mu hankulan mu da tunanukan mu suna wani waje!!


A jiya Laraba Ahmad Wulayatul-haq ya rubuta wata magana ta Sayyid Hameed wadda yayi ma taken "SAMARI A CIKIN HARKA/ SOCIETYN HARKA" a  maganar Sayyid Hameed ya yi jan hankali kan yadda mu ke gafala da abubuwan da ake faɗi mana za su faru maimakon mu ɗauki mataki tun da wuri a'a sai lokaci ya ƙure mana sannan muke farga,  wannan maganar ta Sayyid Hameed ta sa zan bamu misalai da wasu abubuwa dake faruwa a yanzu kuma in ja hankalin mu tayiwu wasunmu su farka.


Matsalar da muke samu shine mun kasa ankarewa da abubuwan dake faruwa a zagaye damu yau da kullum misali a cikin maganar Sayyid Hameed ya faɗi cewa 👇


"Duk abunda ake cemana zai faru damu yana faruwa gradually. Yanata faruwa yana faruwa har sai yazo point din da ba zamu iya komai ba, muna gayamuku cewa akwai wani Danja Babba dake fuskantarmu yanzu. 


"Wanda wasu ne zasu turo mana (Turawa) kamar yanda sukayi a iraqi da Afganistan for instance, mali gashi nan anayi Kusa damu, da sungama zasuzo kanmu".


Idan ka karanta wannan maganar saika koma kayi nazarin abubuwan da Jagora (H) yake ta faɗi mana na daga shirye shiryen ƙasashen Yamma na mallake wannan al'ummar da ganin bayan ta, ka ɗauki abu na baya bayan nan, kafin a fara Kidnapping ɗin mutane da sace sacen dabbobi a yankunan Zamfara, Katsina da Kaduna, Abba (H) ya yi cikakken bayani na shirin wannan mummunar aika aikar amma kowa yayi biris kamar kawai labari ake bamu, amma me ya faru ba ayi shekara ɗaya da yin maganar ba wannan musibar ta fara addabar waɗannan yankunan ga ta nan muna ta fuskanta har yanzu, yanzu kowa ya fahimci abinda su Abba (H) suka fadi a wancan lokacin ba labari bane kawai, tunda gashinan yana faruwa da wanda ya yarda da wanda bai yarda ba kowa ya ga zahiri.


To yanzu ga wata sabuwar musiba tana shirin faruwa ƙari akan wadda muke ciki, amma duk mun kawar da kai daga gareta sai tazo ta cinye mu sannan mu fara neman ɗaukar matakai wanda yanzu ne yakamata mu yaƙe ta, ƙila idan muka farka Allah ya yi amfani da mu ya daƙile ta.


Wannan musiba itace sabon irin abinci da za a samar wa manoma su shuka su ciyar damu, wanda a yanzu a hukumance gwamnatin Najeriya ta amince da sabon irin masara da aka samar wanda ake Kira 'Tela Maize" da ƙungiyar 'AATF' wadda  Bill Gate ya ɗauki nauyi samarwa, wannan iri ne daga irin  "Genetically Modified Organisms" (GMO), bala'in dake tattare da wannan irin yafi bala'in Boko Haram a cewar masana, nasan yanzu haka ma wani yana karanta rubutun nan yanajin abun kamar bai shafe shi ba tun da shi ba manomi bane, ko kuma kawai ana ƙalubalantar wani sabo cigaba ne da aka samu, to bari inyi maka yadda zaka gane yana da alaƙa dakai.


Mu koma kan waccan maganar ta Sayyid Hameed, sai in tuna maka cewa Indai kai ɗan harkar musulunci ne karkashin jagorancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) dake gwagwarmayar tabbatar adalci da kawar da zalunci wato tabbatar addini kenan, kasan an fadi maka cewa turawan nan zasu zo dakan su domin cimma hadafin su na mallake mu da ganin bayan duk wanda zai ja da su musamman ma'abota addini, to kana jiran sai sunzo da sojoji sanye da kaki ɗauke da makamai sannan zaka gane sunzo dakan su kenan?


Zuwa da kansu yana nufin zuwan su ta kowace fuska, a yau muna fuskantar su ne ta janibin  tattalin arziki dan haka aikin mu ne yaƙar wannan musibar tun kafin ta auku.


Abinda baka sani ba shine wannan yana daga cikin Agenda ɗin su ta SDGs Agenda 2030, kagane cewa abun shiryeyyen abu ne da suka shirya mashi kuma suka biyo ta hanyar da hankulan mu ba za su kai ba.


Wato duk wani dan guntun bayani da za a yi maka akan haɗarin wannan Irin da ake so manoma su fara nomawa ba zaka fahimta ba, Alhmdllh Dr. Shamsuddeen Hassan yayi kokarin bayyana ma mutane haɗarin dake tattare da wannan Iri na abinci a cikin rubutukan da yayi na fallasa shirin 'Mamaya 2030', sannan kwanan nan da labarin amincewar Federal ya fito ya kara yin wani gajeren rubutu.


Hakanan na naga Articles masu yawa a Internet dangane da haɗarin dake tattare da wannan iri na "Genetically Modified Organisms" (GMO)


Yakamata muyi tunanin abubuwan da zamu iya yi akan wannan musiba tun kafin ta fara cin mu.


Zamu cigaba a rubutu na gaba.


©️ Mahadi Tukur Almizan

04- July - 2024

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post