Yadda aka gudanar da taron karfafa juna da Kwakwafa tunanikka akan Harkar a Da'irar Babban Rami



Taron wanda Da'irar tare da haɗin gwiwar dandalin matasan na garin Babban Rami dake cikin karamar hukumar Mashegu a jihar Neja. Sheikh Aliyu Tirmizi Kaduna shine Babban Bako a wurin taron da ya gudana jiya Lahadi 31/12/2023.


An soma taron tun misalin ƙarfe 10:30am na safiyar jiya Lahadi, a Government day secondary school, Babban Rami.



Taron wanda aka shirya domin zaburantarwa da karfafawa tare da Kwakwafa tunanikkan yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzkay (H), akan gwagwarmayar tabbatar da addinin Musulunci karkashin jagorancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H).


Daruruwan yan uwane maza da mata suka halarci taron wanda aka shirya na wuni daya.



Kafin jawabi babban Bako, Malam Muhammad Tukur wakilin yan uwa Musulmi na garin Babban Rami, yayi takaitaccen bayanin makasudin shirya wannan taron.


Malam Ibrahim Ahmad Imam shine mai jawabi na biyu. Sannan jawabin Babban Bako Sheikh Aliyu Tirmizi Kaduna wakilin yan uwa Musulmi almajiran Shaikh Zakzkay na Da'irar Kaduna 


Sheikh Aliyu Tirmizi, ya taɓo janibobi da daman gaske kama daga manufar da'awar Sayyid Zakzaky, yadda dan gwagwarmaya ya kamata ya kasance, yadda dan uwa ya kamata ya kasance a cikin al'umma da yake rayuwa a cikin ta, mujahada da sauransu.


Sheikh Tirmizi yayi bayanin sosai. Kafin aka je sallah da cin abinci.


Bayan dawowa aka yi tambaya da amsa, filin tattaunawa, sai ta'aliki da Sheikh Tirmizi Kaduna ya gabatar. Inda ya jaddada muhimmancin neman ilimi ga matashin dan gwagwarmaya.


Sai aka yi addu'a da Sheikh ya gabatar.


Daga wakilinmu

📸 Auwal M Tukur

1/1/ 2024.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post