MUHIMMANCIN NEMAN ILIMI GA RAYUWAR ƊAN ADAM.

 MUHIMMANCIN NEMAN ILIMI GA RAYUWAR 'DAN'ADAM.



  Bismillahir-rahmanir-rahiim...✍️


Ilimi haske ne da shiriya, kamar yadda jahilci duhu ne da bata. Ilimi idan ya hadu da imani, daukaka ne duniya da lahira, kuma aiki shine ribar ilimi, kuma shine asasin ilimi, don haka ya wajaba ga daliban ilimi yin aiki da iliminsu, in ba haka ba kuwa, sai ilimin ya zama hasara gare su kuma mara amfani, Domin malamin da baya aiki da ilimin shi, kamar fitila ce haska wani kona kanki.  


Ilimi shiriya ne, Kuma Gadon Annabawa ne da abinda suka bari domin a tuna su. Kuma ma'abota ilimi Dangin su ne kuma magadan su ne, Ilimi Rayuwar Zuciya ne, Hasken Basira ne, Waraka ne ga Kiraza, Dausayi ne na Hankula, Daɗi ne na Rayuka, Ɗebe kewa ne ga wanda suka shiga Damuwa, Hanyace ga wanda suka shiga ruɗu, Ma'aunine da ake auna Zantuka da aiyuka da Halaye, Shine abin hukunci na rabewa tsakanin Shakka da Yaƙini, da haske da bata.


Manzon Allah (saww) yace "NEMAN ILIMI FARILLA NE AKAN KOWANNE MUSULMI DA MUSULMA". Ilimi yana sama da dukkanin wata baiwa wacce Allah yake yiwa 'Dan Adam. Sannan tun farko wannan jinsin namu ya samu daukaka ne saboda albarkar ilimi. Allah ya Umurci Mala'iku sunyi Sujjadah ga Annabi Aadam (as) ne saboda fifikon ilimin da yayi musu.


Sai dai Mafiya yawan mutanenmu awannan zamanin basu dauki

neman ilimin addini amatsayin da ya kamata su daukeshi ba, Sun daukeshi ne amatsayin wani abu na wucin-gadi (Wato kamar bai zama lallai akansu ba). Domin zaka ga a wannan zamanin zamu ga Mafiya yawan Iyaye basa iya kashe ma 'Ya'yansu Rabin kudaden da suke kashe musu akan karatun boko. Na'am Babu laifi, Amma de ya zama an baiwa ilimin Addini muhimmanci. 


Ilimin addini abu ne wanda ya zama Wajibi ka nemeshi tun daga zanin goyo, har zuwa Qabarinka, Babu ranar denashi, Domin kuwa idan kaje ma Allah amatsayinka na jahili, to fa baka da sauran wani uzuri awajensa Allah (SWT). "Ban sani ba" Ko kuma "Ban samu lokaci ba" Ba zasu zama Uzuri agareka ba aranar Alkiyama. Domin kuwa Ubangiji ya riga ya rayaka har zuwa shekarun balaga. Watakil ma har kayi aure ka haihu.


Hakika addinin musulunci ba a yinsa bisa jahilci, saboda haka muna iya ganin farkon sakon da Allah (Ta'ala) Ya aiko wa Manzon Sa Muhammad 'Dan Abdullahi (SAWA), Umarnine dangane da yin  karatu, kamar yadda ya zo cikin Alkur'ani Mai tsarki, Qarkashin suratul Alaq, aya ta daya zuwa ta biyar: ".             


Bayan wannan akwai ayoyi Masu yawa da suke Umarni da neman ilimi, karatu da koyarwa, wadanda suka hada da hadisul Kudsi da suke nuna wajibcin neman ilimi a Musulunci.


Tabbas bautar Allah (Ta'ala) bata kammala sai da ilimi, Ilimi kuwa baya cika sai da karatu, bisa la'akari da cewa sai an san Allah(Ta'ala) kafin a bauta masa, Kamar yadda Shi Madaukakin sarki ya fada ta bakin Manzonsa mai girma cewa; "Ku San ni kafin ku bauta mini, idan ba ku sanniba ya za ku bauta min". Hada da hadisan Manzon (SAWA) Masu yawa da suke nuni kan, Ba'a Addini bisa jahilci, wannan yana nuna mana cewa dole ne mu tashi mu yunkura don neman ilimin addini, har ma da ilimin kimiya da fasaha na zamani, da haka ne za mu iya sanin yadda ya kamata mu bauta wa Allah(Ta'ala).


Babu shakka ilimi na Addini yana da yawan gaske, tare da mahanga daban-daban, bisa nazariyyan Jama'a Masu yawa, Wadanda suke ba da fahimtarsu dangane da Addini kan abin da ya shafi sanin Allah (Ta'ala), Adalci, Kaddara, Manzanci, Littattafa, Mala'iku, hada da ranar Qiyama.


   ___JAN HANKALI


Ina kira mazan mu da matan mu da mu tashi haikan, mu zage dantse wajen neman ilimin Addini da na boko. Lokaci bai kure maka ba, Gemu ba ya hana neman Ilimi, Don haka baka yi Girma ba, Uwar gida lokaci bai kure miki ba. A dage wajen neman ilimi, idan har kana so ka samu shiga Aljannah, to ba'a shigarta sai da Ilimi. Domin yazo acikin hadisul Kudsi Allah (Swt) Yana cewa; Ya halicci Aljanna da koramu, amma bai bar ko da taku daya mazaunin jahiliba. Da wannan nake cewa Wassalam...


     ____ Fatima Adamu Tinja.📝

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post