MAULUDIN MANZON RAHAMA ( S ) A HALƘA IMAM ALIYU ZAINUL-ABIDEEN DA'IRAR KUDAN

 MAULUDIN MANZON RAHAMA ( S ) A HALƘA IMAM ALIYU ZAINUL-ABIDEEN DA'IRAR KUDAN_Ma'asumah Nigeria News Update

 

'Yan uwa Musulmi Almajiran Sayyid Ibraheem ( H ) na cikin Garin Kudan sun Gudanar da Gagarumin Bikin Mauludin Manzon Allah ( S ). Wanda suka saba shiryawa dukkan shekara bayan kammala Mauludin Da'irar Kudan.


Bayan buɗe Taro da addu'a, an gudanar da karatun Alqur'ani Mai Girma. Daga bisani an Gudanar da Ziyar Manzon Allah. Tare da Salatin Annabi Muhammad bayan Idar da Ziyar Manzon Allah ( S ).


Bayan Gabatar da Babban baƙo wanda Shaikh Junaidu Muhammad Sani Kudan ya gabatar da Babban baƙo mai jawabi Shaikh Abdulhamid Bello Zaria. Inda ya bayyana wa su Darusa akan Rayuwar Annabi Muhammad Bin Abdullah ( S ).


Shehin Malamin ya fara bayyana Tarihin Rayuwar Manzon Allah ( S ) Tun, daga Ranar da ya zo wannan Duniya Har zuwa komawar sa. 


Shaikh ya kara da cewa; Manzon Allah mutunne mai kamala sosai wanda koda kuwa za a zo cikin Maka ayi magana akan Mutum Mai kalama to, lallai babu kamar Manzon Allah. Koda anyi magana a loƙacin Shi ne dai za a kawo mutum Mai kalama Muhammad Bin Abdullah.


Cewar: Shaikh Abdulhamid Bello Zariya. Ya yin Gudanar da Jawabinsa a cikin Garin Kudan wanda yake Gudana a cikin wannan Daran.


Daga_ Faruq Sani Kudan


Ma'asumah Nigeria News Update

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post