MATSALOLIN WASU DAGA CIKIN MATA GUDA BIYAR (5), WANDA SUKAN IYA ƁATA ZAMANTAKEWA

 


Daga - Fatima Adamu Tinja..✍️

1.Kwadayi:Galiban ‘yan  mata ko iyayensu suna neman mai kudi ruwa a jallo ne domin su je su huta. Ba ace karki yi soyayya ko ki auri mai zaman banza ba,amma wanda ya san ciwon kansa yake kuma da zuciyar nema tattare da nagartar halaye, idan kika same shi ya kamata ki saurare shi.


2.Dogon buri:wasu matan akan same su da dogon buri. Da zaran ta ga kawarta ta mallaki kayan sawa masu tsada,ko manyan wayoyi,ko wani abu  mai kayatarwa a nan kuma sai ka ga mace ta jefa kanta a cikin halin takuruwa da dogon buri.


3.Karya: Wasu mata  suna amfani da karya a yayin mu’amalar soyayya,a nan ya kamata ki riki gaskiya a matsayin makaminki domin karya tana karewa amma kuma gaskiya tana habaka da dawwama ne.


4.Wulakanci: Shi ma yana lalata alakar soyayya,ya kamata ki mutunta wanda ya bayyana miki so.


5.Shawarwarin kawaye:ya kamata ki kasance mai ra’ayin kan ki tattare da shawartar iyayenki ko ‘yan uwanki a kan lamarin soyayya da dukkanin rayuwa.Ba ace ka da ki saurari shawarar kawaye ba,amma ki duba wacce za ki karbi shawara daga wajenta.


    ____Zamuci gaba insha Allah.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post