ME AKE NUFI DA IBADA,,,@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @


BA A KOWANNE GURI AKE BAYYANA FARIN CIKI BA


Ma'anar farin ciki dai shine jin dadi cikin zuciya wanda kan iya bayyana a fuska sakamakon faruwa ko aukuwar wani al'amari wanda mutum ke so. Shi wannan farin ciki za a iya kasa shi kashi biyu, wato mai kyau ko mummuna.


Kyakkyawan farin ciki shine wanda ya samu ko aka aikata bisa alkhairi. 


Mummunan farin ciki kuma shine wanda aka yi shi saboda mummunan abu ya auku kan wani dan'uwanka wanda ya kamata ace baqin ciki za kayi a matsayin nuna kana tare dashi. 


Munyi nufin kawo wasu riwayoyi biyu ne daga cikin Hadisan Imam Hassan Al-Askari (A. S) don yin nazari tare da daukar darasi daga cikinsu. Ga su kamar haka :


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


قال الإمام العسكري(ع): ليست العبادة كثرة الصيام والصلاة ، وإنما العبادة كثرة التفكر في أمر الله . 


Imam Askari (A. S) na cewa : " YAWAN AZUMI DA SALLAH BA SUNE IBADA BA, IBADA DAI ITA CE YAWAN YIN TUNANI CIKIN AL'AMRUN ALLAH. "

المصدر : بحار الأنوار


Lalle idan mu kayi la'akari da kyau za mu iya ganin ana samun mutane masu yawan sallah da azumi, amma kuma sai kaga suna aikata abubuwa masu yawa wadanda Allah yayi hani a kansu. Kenan ba za asa wannan aiki nasa ya zama ibada wacce Allah ke so ba, domin ba zai amfanar da mai yinta ba. 


Riwaya ta biyu da muke son kawowa ita ce inda yake cewa :قال الإمام العسكري(ع):


" ليس من الادب إظهار الفرح عند المحزون ."


" BA YA DAGA CIKIN LADABI BAYYANAR DA FARIN CIKI A WAJEN WANDA KE BAQIN CIKI (saboda wani al'amari da ya faru dashi). "


 

المصدر : بحار الأنوار


Ko da shike yawancin mutane ba hankali ko tunani ne dasu ba, amma da sai nace lalle wannan qalu-bale ne ga masu zaman makoki.


Zaman makoki dai zama ne na jimami ba wai na farin ciki ba, amma abin mamaki sai kaga wadanda abin ya shafa ne masu tadin siyasa ko wani abu na duniya wanda ke shagaltar dasu daga abinda ya tara su. Wannan yakan bada dama ga wasu kaga/ji har dariya da qyaqyaci ake yi. 


Lalle ko da mutum na cikin wani farin ciki ba zai zama ladabi ace yana bayyanar da wannan farin ciki nasa gaban wanda ke cikin baqin ciki ba.


Yayin da kake bayyana farin cikinka a gaban wanda ke cikin baqin ciki dayan biyu ne dai zai iya faruwa. Ko dai yaji cewa ba ka damu da damuwarsa ba ko kuma dai yaji kamar kana farin ciki ne na abinda ya same shi, domin ana samun masu nuna farin cikinsu kan wani abin baqin ciki da ya sami dan'uwansu. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


          (08137925034)

         

          Mnnu//Ng0027 

           08088425298

14th October, 2023/  29th Rabi'u-Awwal, 1445.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post