MATSAYIN AURE A MUSLIMCI !!! (3)

 MATSAYIN AURE A MUSLIMCI  !!! (3)



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @


YADDA AKE ZABIN MACE YAYIN DA AKA TASHI YIN AURE. 



Babu wani abu a muslimci wanda Allah (T) bai yi mana bayanin yadda ake yinsa ko yadda ya kamata ayi shi ba. Duk wani abu wanda yake halas ko haram an bayyana mana su filla-filla, har abinda ya shafi yadda ake neman aure da yadda ake yinsa da kuma hukuncinsa.


Manzon Allah (S. A. W. W) yayi mana bayani kan wasu abubuwa wadanda qarara ba a ambaci hukuncinsu cikin Qur'ani ba, ko wadanda akayi bayanin nasu cikin Qur'ani amma ba kowa ne zai fahimce su ba dole har sai shi (S. A. W. W) yayi mana bayaninsu. 


Rubutunmu na yau zaiyi magana ne kan yadda ake zabin matar aure a muslimci, kuma za muyi amfani da hadisai ne wajen nuni kan hakan.  Ga kadan daga cikinsu :


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


24941- 1-[1] مُحَمَّدُ بْنُ يَعْقُوبَ عَنْ عِدَّةٍ مِنْ أَصْحَابِنَا عَنْ سَهْلِ بْنِ زِيَادٍ وَ أَحْمَدَ بْنِ مُحَمَّدٍ جَمِيعاً عَنِ ابْنِ مَحْبُوبٍ عَنْ إِبْرَاهِيمَ الْكَرْخِيِّ قَالَ: قُلْتُ لِأَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع 

إِنَّ صَاحِبَتِي هَلَكَتْ وَ كَانَتْ لِي مُوَافِقَةً وَ قَدْ هَمَمْتُ أَنْ 

أَتَزَوَّجَ فَقَالَ لِيَ انْظُرْ أَيْنَ تَضَعُ نَفْسَكَ وَ مَنْ تُشْرِكُهُ فِي مَالِكَ وَ تُطْلِعُهُ عَلَى‏ دِينِكَ وَ سِرِّكَ فَإِنْ كُنْتَ لَا بُدَّ فَاعِلًا فَبِكْراً تُنْسَبُ إِلَى الْخَيْرِ وَ إِلَى حُسْنِ الْخُلُقِ  ..........وَ هُنَّ ثَلَاثٌ فَامْرَأَةٌ وَلُودٌ وَدُودٌ تُعِينُ زَوْجَهَا عَلَى دَهْرِهِ لِدُنْيَاهُ وَ آخِرَتِهِ وَ لَا تُعِينُ الدَّهْرَ عَلَيْهِ وَ امْرَأَةٌ عَقِيمٌ لَا ذَاتُ جَمَالٍ وَ لَا خُلُقٍ وَ لَا تُعِينُ زَوْجَهَا عَلَى خَيْرٍ وَ امْرَأَةٌ صَخَّابَةٌ وَلَّاجَةٌ هَمَّازَةٌ تَسْتَقِلُّ الْكَثِيرَ وَ لَا 

تَقْبَلُ الْيَسِيرَ.


Daga Muhammad Bn Ya'aqub, daga Iddati daga cikin Sahabbanmu, daga Sahl Bn Ziyaad da Ahmad Bn Muhammad, gaba daya (dukkansu) daga Ibn Mahbub, daga Ibrahim Al-Karkhiyyi yace : Nace ga Abu Abdullah (A. S) :


" Lalle matata ta halaka (mutu), kuma ta dace dani (a wajen zamantakewa), kuma haqiqa nayi nufin aure. Sai yace min :


" KAYI DUBI A INA ZA KA SANYA KANKA KUMA WA ZA KAYI TARAYYA DASHI CIKIN DUKIYARKA , KUMA KA NUTSU DASHI A ADDININKA DA SIRRINKA. 


IDAN KA KASANCE BABU MAKAWA SAI KA AIKATA (wani auren), TO, KA AURI BUDURWA TA FI KUSANTAKA DA ALKHAIRI KUMA ZUWA GA KYAWAWAN 'DABI'U (domin bata je gidan wani ya bata mata tarbiyyarta ba)................ Kuma su din nan uku ne :-


(1)- Mace mai haihuwa (irin Nana Khadijah) mai (nuna) soyayya (kamar Nana Fatimah), za ta taimaki mijinta akan zamaninsa domin duniyarsa da lahirarsa (kamar yadda wadandan mata biyu suka taimaki mazajansu). Kuma ba za ta taimaki zamani a kansa ba. 


(2)- Da mace marar haihuwa ba ma'abociyar kyawu ba kuma ba mai kyawawan dabi'u ba. Ba za ta taimaki mijinta akan alkhairi ba (domin bata samu alkhairi tare da ita ba). 


(3)- Da mace mai quntatawa/takurawa marar sakin fuska mai zunde, tana qanqanta (abinda za ka bata) mai yawa kuma ba ta karbar (abu) kadan (saboda rainako).


Jinsin farko shi ake kwadaitar da wanda ya tashi neman aure domin za su taimaki miji ta kowacce fuska. Amma jinsi na biyu dana uku babu alkhairi tare dasu. 


24942- 2-[7] وَ عَنْهُمْ عَنْ سَهْلٍ وَ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ يَحْيَى عَنْ أَحْمَدَ بْنِ مُحَمَّدِ بْنِ عِيسَى وَ عَنْ عَلِيِّ بْنِ إِبْرَاهِيمَ عَنْ أَبِيهِ جَمِيعاً عَنِ الْحَسَنِ بْنِ‏ مَحْبُوبٍ‏ عَنْ عَلِيِّ بْنِ رِئَابٍ عَنْ أَبِي حَمْزَةَ عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ قَالَ سَمِعْتُهُ يَقُولُ‏ كُنَّا عِنْدَ النَّبِيِّ ص فَقَالَ إِنَّ خَيْرَ نِسَائِكُمُ الْوَلُودُ الْوَدُودُ الْعَفِيفَةُ الْعَزِيزَةُ فِي أَهْلِهَا الذَّلِيلَةُ مَعَ بَعْلِهَا الْمُتَبَرِّجَةُ مَعَ زَوْجِهَا الْحَصَانُ‏ عَلَى غَيْرِهِ الَّتِي تَسْمَعُ قَوْلَهُ وَ تُطِيعُ أَمْرَهُ وَ إِذَا خَلَا بِهَا بَذَلَتْ لَهُ مَا 

يُرِيدُ مِنْهَا وَ لَمْ تَبَذَّلْ‏ كَتَبَذُّلِ الرَّجُلِ."


Daga gare shi (Muhammad Bn Ya'aqub)  daga Sahl, da kuma Muhammad Bn Yahya, daga Ahmad Bn Muhammad Bn Isah, kuma daga Aliyu Bn Ibrahim, daga babansa, gaba dayansu daga Hassan Bn Mahbuub, daga Aliyu Bn Ri'aab, daga baban Hamzata daga Jabir Bn Abdullahi yace : Na ji shi yana cewa yana cewa :


" Mun kasance a wajen Annabi (S. A. W. W) sai yace :


" LALLE MAFI ALKHAIRIN MATANKU ITA CE MAI HAIHUWA MAI SOYAYYA, MAI KAMIN KAI KUMA MADAUKAKIYA CIKIN IYALINTA KUMA MAI QASQANTAR DA KAI TARE DA MIJINTA, MAI BAYYANAR DA ADO TARE DA MIJINTA, MAI TSARE KAI GA WANINSA. WACCE TAKE JIN MAGANARSA KUMA TANA BIYAYYA GA UMARNINSA. IDAN YA KEBANTA DA ITA DUK ABINDA YA NUFA DA ITA ZA TAYI/BA SHI, KUMA BA TA BA TA YIN SHIGA (dress) KAMAR YADDA MAZA KE YI. "


التهذيب 7- 400- 1597.


Wannan hadisi ya ambato sashen wani abu daga hadisin farko, sannan ya yi qari kan wasu siffofi (qualities) na matar da ya kamata a nema da aure. 


24977- 8-[12] وَ عَنْ عِدَّةٍ مِنْ أَصْحَابِنَا عَنْ أَحْمَدَ بْنِ مُحَمَّدٍ عَنِ ابْنِ فَضَّالٍ عَنْ عَلِيِّ بْنِ عُقْبَةَ عَنْ بُرَيْدِ بْنِ مُعَاوِيَةَ الْعِجْلِيِّ عَنْ أَبِي جَعْفَرٍ ع قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص قَالَ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَ‏ إِذَا أَرَدْتُ أَنْ أَجْمَعَ لِلْمُسْلِمِ خَيْرَ الدُّنْيَا وَ خَيْرَ الْآخِرَةِ جَعَلْتُ لَهُ قَلْباً خَاشِعاً وَ لِسَاناً ذَاكِراً وَ جَسَداً عَلَى الْبَلَاءِ صَابِراً وَ زَوْجَةً مُؤْمِنَةً تَسُرُّهُ إِذَا نَظَرَ إِلَيْهَا وَ تَحْفَظُهُ إِذَا غَابَ عَنْهَا فِي نَفْسِهَا وَ مَالِهِ."


Daga Iddatin daga cikin Sahabbanmu daga Ahmad Bn Muhammad, daga Ibn Faddhaali, daga Aliyu Bn Uqbata, daga Buraidi Bn Mu'awiyata Al-Ijliyyi, daga Abu Ja'afar  (A. S) yace : Manzon Allah (S. A. W. W) ya ce :


" ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA YA CE : "IDAN NAYI NUFIN TATTARAWA  MUSULMI ALKHAIRIN DUNIYA DA LAHIRA SAI NA SANYA MASA ZUCIYA MAI GODIYA, DA HARSHE  MAI AMBATO (sunan Allah) DA GANGAR JIKI MAI HAQURI AKAN BALA'I, DA MATA MUMINA WACCE KE FARANTA MASA (rai) IN YA KALLETA KUMA TANA TSARE SHI (kame kanta) IDAN BA YA NAN AKAN KANTA DA DUKIYARSA. "

 

[12] الكافي 5- 327- 2.


Wannan shine kadan daga cikin abubuwan da ake fara dubawa ga mace idan mutum ya tashi yin aure. 


YAA ALLAH KA DATAR DAMU DA MATA SALIHAI  


🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾🙏🏾


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


         (08137925034)


29th October, 2023/  14th Rabi'us-Sani, 1445.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post