IRAN TA GWADA JIRAGEN YAKI MARASA MATUKA DA TA KERA SAMFURIN ABABIL-2 A CIKIN NASARA.


 Daga Bin Muhammad

A ci gaba da gudanar da atisayin da sojojin ruwa na kasar Iran keyi, a Jiya sun gwada jirgin yaki mara matuki samfurin Ababil-2 da kasar ta kera, wanda ya gudana a cikin nasara.

A Shekaran Jiya Talata ne sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran suka fara atisayen hadin gwiwa, inda ake gwada jiragen yaki marasa matuka samfari daban-daban da kasar ta kera.Mai magana da yawun atisayin yace: A lokacin da aka shiga manyan matakai na hadin gwiwa a wannan atisayi, jirgin yaki samfurin "Violin 19" maras matuki ya shiga aikin a karon farko, kuma ayyukan na'urorin yaki na zamani da aka gwada a fagen jiragen sun yi nasara.

Birgediya Janar Ali Redha Sheikh yace: A yayin wannan atisayi, an samu gagarumar nasara a dukkanin bangarori, inda aka gwada jiragen yaki fiye da 200 masu gudanar da ayyuka daban-daban na yaki. A nasa bangaren, kwamandan rundunar hadin gwiwa Admiral Habibullah Sayyari ya bayyana cewa: An gudanar da wannan atisayen na hadin gwiwa tare da sanya hannu na dukaknin bangarori na rundunonin soji ruwa da sama da kuma na sama na kasar Iran. Ya kara da cewa: A cikin sa'o'i na farko na wannan atisayi, an gwada jiragen yaki marasa matuka masu gudanar da ayyukan leken asiri da tattaro bayanai, da kuma wadanda ake amfani da su wajen ayyukan tsaron kan iyakokin kasar, da kuma masu aiko bayanai kan duk wani yunkuri na kawo hari kan kasar, kuma dukkanin gwaje-gwajen sun gudana cikin nasara.

Real Naseer Umar 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post