Amurka Ta Gargaɗi Isra'ila Kan Harar Hizbullah: Zaku Fuskanci Babban Ƙalubale Idan Kuka Yaƙi Hamas Da Hizbullah A Lokaci Ɗaya - cewar Amurka

 


Fadar White House da CIA sun tabbatar cewa Isra'ila ba zata iya yin nasara akan Hizbullah da Hamas ba a lokaci ɗaya.


Jaridar New York Times ta ruwaito a jiya asabar 21 ga watan Oktoba cewa "Jami'an Gwamnatin Amurka sun gargaɗi ministan tsaron Isra'ila da wasu jami'an tsaron Isra'ila kan kaima Hizbullah hari, tun bayan harin Hamas kan Isra'ila na ranar 7 ga watan Oktoban da muke ciki".


Fadar White House ta cigaba da gargaɗin shugabannin haramtacciyar ƙasar Isra'ila ne saboda kauce ma shigo da Hizbullah cikin wannan yaƙi tsakanin Isra'ila da Hamas dake jagorantar ƴan sauran dakarun gwagwarmayar Palasɗinawa, kamar yadda wani jami'in gwamnatin Amurka da Isra'ila suka shaidawa ma jaridar ta New York Times.


Amurka tana jiye ma Isra'ila tsoron shan wahala wajen fuskantar waɗannan dakaru biyu na Hamas dake kudanci da kuma ƙaƙƙarfar rundunar Hizbullah dake Arewaci.


Jaridar ta New York Times ta bayyana cewa CIA ta tabbatar da cewa Isra'ila zata fuskanci ƙalubale idan har zata yaƙi Hizbullah da Hamas a lokaci guda.


Hizbullah dai ta mallaki sama da missiles da rocket 130,000 tare da zaratan dakaru waɗanda suke da ƙwarewa domin sun yaƙi ISIS da AlQa'eda a Syria a shekarar 2011.


Jami'an na Amurka sun damu sosai, domin yaƙi tsakanin Isra'ila da Hizbullah zai jefa Amurka yaƙi da Iran, a matsayin Amurka na babbar mai goyon bayan Isra'ila, ita kuma Iran mai goyon bayan Hizbullah.


Iran da Hizbullah dai duk sun gargaɗi Isra'ila da Amurka akan cigaba da kai hari Gaza, wanda yayi sanadiyyar kashe Palasɗinawa samada 5000, ciki harda yara 1,600.


Jami'in na gwamnatin Amurka da ya tattauna da New York Times ya bayyana cewa Benjamin Netanyahu ya ƙaddamar da hare hare kan Hizbullah ne a bisa shawarar ministan tsaron Isra'ila Yoav Gallant, dalilin Yoav Gallant shine Hizbullah tafi zama barazana a garesu fiye da Hamas.


A ziyarar Anthony Blinken da Joe Biden suka kai Isra'ila, duk sun gargaɗi takwarorin su na Isra'ila kan harar Hizbullah.


Tun bayan ƙaddamar da Operation Aqsa Flood Isra'ila da Hizbullah suke kaima juna hare hare da rokoki.


Ko a wani hari da Hizbullah ta kai akan sojojin Isra'ila ta kashe wani soja mai suna Omer Bala, mai shekaru 22, Balva kwamanda ne na Bataliyon ta 9203 ta Alexandroni Brigade dake Herzliya.


Itama Isra'ila ta shahadantar  da wasu sojojin Hizbullah har 16 zuwa jiya asabar.


✍️ Mahadi Tukur Almizan | Ma'asuma Nigerian News Update.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post