Za mu kawo wa Najeriya ɗaukin dala biliyan 2.5 don yaƙi yunwa


 Za mu kawo wa Najeriya ɗaukin dala biliyan 2.5 don yaƙi yunwa'Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ta alƙawarta samar da dala biliyan 2.5 domin taimaka wa Najeriya wajen cimma burinta na yaƙi da yunwa da wadata al'umma da abinci a ƙasar.

Daraktan hukumar a Najeriya, Mista David Stevesson, ne ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci ayarin jami'ansa don kai ziyara ga ministar jin ƙai da yaƙi da fatara, Dakta Betta Edu a Abuja, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito.Ya ce "mun tattauna game da yaƙi da yunwa a Najeriya, da kuma ayyukan jin ƙai a kowacce ƙaramar hukuma a faɗin ƙasar, sannan mun tattauna kan shirin samar da abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya .Ya ce za a gudanar da shirin ne ta hanyar tallafa wa ƙananan hukumomi wajen sayen abinci domin rarraba wa mabuƙata, da kuma ba su tallafin kuɗi da na abincin kai tsaye.Don haka nake son bayyana cewa Hukumar Samar da Abinci ta Duniya za ta kashe dala biliyan 2.5 domin yaƙi da yunwa a Najeriya cikin shekara biyar masu zuwa', in ji daraktan.

Mista Stevesson, ya kuma ce hukumarsa ta ɗauki sunayen mutum miliyan biyu da dubu ɗari ɗaya waɗanda za su ci gajiyar shirin.Ya kuma bayyana fatan ci gaba da aiki kafaɗa-da -kafaɗa da ma'aikatar jin-ƙai ta Najeriya domin cimma wannan buri.Jami'in ya dai bayyana aniyar hukumar wajen tallafa a gwamnatin tarayya don magance matsalolin jin-ƙai tare da yaƙi da yunwa, musamman ta fuskar wadata ƙasar da abinci.”Muna farin ciki kan matakan da shugaban Najeriya ya ɗauka na kawar da yunwa tare da rage buƙatar ayyukan jin-ƙai a Najeriya", in ji shi.Ya ci gaba da cewa ”sabbin tsare-tsare da ministar jin-ƙai ta zo da su, za su bai wa hukumarsa damar cimma nasarori masu yawa tare da ma'aikatar".

Real Naseer Umar Johnson 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post