Tofa Ƴan sandan Najeriya na kokawa kan hare-haren da ake kai musu



Babban sufeton 'yan sandan Najeriya ya bayyana takaici kan yadda ya ce ana samun ƙaruwar hare-haren da ake kai wa 'yan sanda a sassan ƙasar.Egbetokun Olukayode Adeolu, ya kuma yi kashedi da kakkausan harshe game da hakan.

Shugaban 'yan sandan ya bayar da umarni a gudanar da cikakken bincike kan ire-iren waɗannan hare-hare, don a zaƙulo waɗanda suke aikata hakan, kuma a hukunta su kamar yadda doka ta tanada.CSP Al-Mustafa Sani, babban jami'i a ofishin hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan Najeriyar, ya yi wa BBC ƙarin bayani dangane da lamarin.

Ya ce, "A wannan ɗan lokacin da muke ciki a hare-haren da ake kai wa ƴan sanda ba a wajen aikinsu kaɗai ba har gidajensu ake binsu ana kai musu wannan irin hari wanda yakan kasance mai tsanani wanda ake ƙoƙarin kashe su ko kuma a illata su a harin. "A kwanakin baya ma a nan Abuja an aje gidan wani supeto na ƴan sanda aka kai masa wannan hari inda aka sassara shi da adda aka ji masa munanan raunuka, wanda yanzu yana can asibiti yana karɓar magani, da kuma ire-iren waɗannan," in ji shi.

Ya ƙara da cewa, " a kwanakin baya ma can an kai wa wani DPO hari wanda suna wajen aiki aka same shi, shi ma aka halaka shi."


Real Naseer Umar Alhassan 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post