ANNABI MUHAMMAD (S. À. W. W) À MATSAYIN HASKE !!!

 


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @


SHEKARU DUBU DA SHA BIYAR (15,000) INA HASKE KAFIN HALITTAR ADAM (À. S)


Samuwar Manzon rahma Muhammad Bn Abdullah (S. À. W. W) a  matsayin haske tun ka fin halittar Annabi Adam (À. S) na tabbatar mana ne cewa shine farkon halitta daga cikin halittun 'ya'yan Adamu (BANI ADAM). 


Allah (T) yayi bayaninsa cikin Al-Qur'ani ta yadda za musan tabbas shine farko a halitta. 


👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇👇


الآيات آل عمران‏: " وَ إِذْ أَخَذَ اللَّهُ مِيثاقَ النَّبِيِّينَ لَما آتَيْتُكُمْ مِنْ كِتابٍ وَ حِكْمَةٍ ثُمَّ جاءَكُمْ رَسُولٌ مُصَدِّقٌ لِما مَعَكُمْ لَتُؤْمِنُنَّ بِهِ وَ لَتَنْصُرُنَّهُ قالَ أَ أَقْرَرْتُمْ وَ أَخَذْتُمْ عَلى‏ ذلِكُمْ إِصْرِي قالُوا أَقْرَرْنا قالَ فَاشْهَدُوا وَ أَنَا مَعَكُمْ مِنَ الشَّاهِدِينَ‏."


" KUMA A LOKACIN DA ALLAH YA RIQI ALQAWARIN ANNABAWA: " LALLE NE BAN BA KU WANI ABU BA DAGA LITTAFI DA HIKIMA, SA'AN NAN KUMA WANI MANZO YA JE MUKU, MAI GASKATAWA GAME DA ABINDA KE TARE DAKU ; LALLE NE ZA KU GASKATA SHI, KUMA LALLE NE ZA KU TAIMAKE SHI. " YACE : " SHIN, KUN TABBATAR,  KUMA KUN RIQI ALQAWARINA AKAN WANNAN A GARE KU ?   SUKA CE : " MUN TABBATA. " YACE : " TO,  KU YI SHAIDA, KUMA NI A TARE DAKU INA DAGA MASU SHAIDA. "


 الأعراف‏: " وَ إِذْ أَخَذَ رَبُّكَ مِنْ بَنِي آدَمَ مِنْ ظُهُورِهِمْ ذُرِّيَّتَهُمْ وَ أَشْهَدَهُمْ عَلى‏ أَنْفُسِهِمْ أَ لَسْتُ 

بِرَبِّكُمْ قالُوا بَلى‏ شَهِدْنا أَنْ تَقُولُوا يَوْمَ الْقِيامَةِ إِنَّا كُنَّا عَنْ هذا غافِلِينَ أَوْ تَقُولُوا إِنَّما أَشْرَكَ آباؤُنا مِنْ قَبْلُ وَ كُنَّا ذُرِّيَّةً مِنْ بَعْدِهِمْ أَ فَتُهْلِكُنا بِما فَعَلَ الْمُبْطِلُونَ‏."


" KUMA A LOKACIN DA UBANGIJINKA YA KARBI (alqawari) DAGA  'YA'YAN ADAM, DAGA BAYANSU, À ZUCIYARSU, KUMA YA SHAIDAR DASU AKAN RAYUKANSU, YACE: " SHIN, BA NINE UBANGIJINKU BA ! "SUKA CE : " NA'AM, MUNYI SHAIDA ! " YACE : " KADA KACE A RANAR QIYAMA : LALLE NE MU DAGA WANNAN (alqawarin da mu kayi) GAFALALLU NE. " KO KUMA KUCE : " ABIN SANI DAI IYAYENMU NE SU KAYI SHIRKA DAGA FARKO, KUMA MU MUN KASANCE ZURIYA DAGA BAYANSU. SHIN, ZA KA HALAKAR DAMU SABODA ABINDA MASU BARNA SUKA AIKATA ? "


172-173


 الشعراء: " الَّذِي يَراكَ حِينَ تَقُومُ وَ تَقَلُّبَكَ فِي السَّاجِدِينَ‏ ."


" SHINE WANDA KE GANINKA YAYIN DA KAKE TASHI (cikin dare kana ibada),  DA KUMA JUJJUYAWARKA CIKIN (tsahon) MASU SUJADAH. "


الأحزاب‏ : "وَ إِذْ أَخَذْنا مِنَ النَّبِيِّينَ مِيثاقَهُمْ وَ مِنْكَ وَ مِنْ نُوحٍ وَ إِبْراهِيمَ وَ مُوسى‏ وَ عِيسَى ابْنِ مَرْيَمَ وَ أَخَذْنا مِنْهُمْ مِيثاقاً غَلِيظاً لِيَسْئَلَ الصَّادِقِينَ عَنْ صِدْقِهِمْ وَ أَعَدَّ لِلْكافِرِينَ عَذاباً أَلِيماً."


" KUMA A LOKACIN DA MUKA RIQI ALQAWARIN ANNABAWA DAGA GARE SU, KUMA DAGA GARE KA, KUMA DAGA NUHU DA IBRAHIM, DA MUSA DA ISAH 'DAN MARYAMA, KUMA MUKA RIQI WANI ALQAWARI MAI KAURI DAGA GARE SU. "


" DOMIN YA TAMBAYI MASU GASKIYA AKAN GASKIYARSU, KUMA YA YI TATTALIN WATA AZABA MAI RADADI GA KAFIRAI. "

7-8


مجمع البيان 8: 339.


تفسير فرات بن إبراهيم عَنْ جَعْفَرِ بْنِ مُحَمَّدٍ الْفَزَارِيِّ بِإِسْنَادِهِ‏ عَنْ قَبِيصَةَ بْنِ يَزِيدَ الْجُعْفِيِ‏ قَالَ: دَخَلْتُ عَلَى الصَّادِقِ ع وَ عِنْدَهُ ابْنُ ظَبْيَانَ وَ الْقَاسِمُ الصَّيْرَفِيُ‏ فَسَلَّمْتُ وَ جَلَسْتُ وَ قُلْتُ يَا ابْنَ رَسُولِ اللَّهِ‏ أَيْنَ كُنْتُمْ قَبْلَ أَنْ يَخْلُقَ اللَّهُ سَمَاءً مَبْنِيَّةً وَ أَرْضاً مَدْحِيَّةً أَوْ ظُلْمَةً أَوْ نُوراً قَالَ 

كُنَّا أَشْبَاحَ نُورٍ حَوْلَ الْعَرْشِ نُسَبِّحُ اللَّهَ قَبْلَ أَنْ يَخْلُقَ 

آدَمَ ع بِخَمْسَةَ عَشَرَ أَلْفَ عَامٍ فَلَمَّا خَلَقَ اللَّهُ آدَمَ ع فَرَّغَنَا فِي صُلْبِهِ فَلَمْ يَزَلْ يَنْقُلُنَا مِنْ صُلْبٍ طَاهِرٍ إِلَى رَحِمٍ مُطَهَّرٍ حَتَّى بَعَثَ اللَّهُ مُحَمَّداً ص الْخَبَرَ."


Sannan kuma ya zo cikin Tafsir na Furrat Bn Ibrahim, daga Ja'afar Muhammad Al-Fazaariy, da isnadinsa daga Qabisata Bn Yazeed  Al-Ju'ufiy  yace :


" Na shiga wajen Sadiq (A. S),  kuma tare dashi akwai Ibn Zubyaana da Qaseem Al-Sairafiyyi, sai nayi sallama na zauna, kuma nace: Yaa dan Manzon Allah (S. A. W. W), à ina kuke kafin Allah ya halicci sama ginanniya, da kuma qasa shimfidaddiya, ko kuma duhu ko haske  ?  Yace :


" MUN KASANCE AN KAMANTAMU HASKE NE A GEFEN AL'ARSHI MUNA YIWA ALLAH TASBIHI TUN KA FIN YA HALICCI ADAMU DA SHEKARA DUBU GOMA SHA BIYAR (15,000). YAYIN DA ALLAH YA HALICCI ADAMU (À. S) SAI YA SANYA MU CIKIN TSATSONSA, BAI GUSHE BA YANA CIRO MU DAGA TSARKAKEKKEN TSATSO ZUWA GA MAHAIFA MAFI TSARKI, HAR ALLAH YA AIKO DA MUHAMMADU (S. À. W. W). " 


تفسير فرات: 207.


تفسير فرات بن إبراهيم جَعْفَرُ بْنُ مُحَمَّدِ بْنِ بِشْرَوَيْهِ الْقَطَّانُ بِإِسْنَادِهِ عَنِ الْأَوْزَاعِيِ‏ عَنْ‏ صَعْصَعَةَ بْنِ صُوحَانَ وَ الْأَحْنَفِ بْنِ قَيْسٍ عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ‏ قَالَ قَالَ رَسُولُ اللَّهِ ص‏ خَلَقَنِيَ اللَّهُ نُوراً تَحْتَ الْعَرْشِ قَبْلَ أَنْ يَخْلُقَ آدَمَ ع بِاثْنَيْ عَشَرَ أَلْفَ سَنَةٍ فَلَمَّا أَنْ خَلَقَ اللَّهُ آدَمَ ع أَلْقَى النُّورَ فِي صُلْبِ آدَمَ ع فَأَقْبَلَ يَنْتَقِلُ ذَلِكَ النُّورُ مِنْ صُلْبٍ إِلَى صُلْبٍ حَتَّى افْتَرَقْنَا فِي صُلْبِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَبْدِ الْمُطَّلِبِ وَ أَبِي طَالِبٍ فَخَلَقَنِي رَبِّي مِنْ ذَلِكَ النُّورِ لَكِنَّهُ لَا نَبِيَّ بَعْدِي‏.


A wata riwaya cikin Tafsir na Furrat, da isnadinsa daga Auzaa'iyyu, daga Sa'asa'ata Bn Suhaana, da Ahnaaf Bn Qais, daga Ibn Abbas yace :


Manzon Allah (S. À. W. W) yace :


" ALLAH YA HALICCE NI HASKE A QARQASHIN AL'ARSHI TUN KA FIN YA HALICCI ADAMU (A. S) DA SHEKARU DUBU GOMA SHA BIYU (12,000). YAYIN DA YA HALICCI ADAMU (A. S) SAI YA JEFA HASKEN CIKIN TSATSON ADAMU (A. S), YA ZAMA YANA CIRO WANNAN HASKE DAGA TSATSO ZUWA TSATSO, HAR YA RABA MU CIKIN TSATSON ABDULLAHI  BN ABDUL-MUDALLIB, DA ABU 'DALIB. DAGA WANNAN HASKE UBANGIJINA YA HALICCE NI, SAI DAI SHI BABU WANI ANNABI BAYANA (ballantana ace dan Abu 'Dalib (Ali) ne Annabi a bayana ba. 


تفسير فرات: 207.


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏽Ado Isah Guda.


              (08137925034)


26th September, 2023/  11th Rabi'u-Awwal, 1445.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post