Jiragen yakin sojojin saman Najeriya da ke aiki tare da rundunar Operation Delta safe na can suna ci gaba da fatattakar yan tsagerun yankin Niger Delta da ke satar mai.


 SOJOJIN SAMAN NAJERIYA SUN TARWATSA JIRAGEN RUWA 3 NA SATAR DANYEN MAI

Sojojin sun kuma gano tare da kone wasu haramtattun matatun mai da tankokin dakon mai shake da man sata. Jiragen yakin sojojin saman Najeriya da ke aiki tare da rundunar Operation Delta safe na can suna ci gaba da fatattakar yan tsagerun yankin Niger Delta da ke satar mai. Jiragen sun kuma gano tare da kone wasu haramtattun matatun mai da tankokin dakon mai shake da man sata, inda suka yi ruwan wuta a kan wasu jiragen ruwa 3 na barayin danyen mai a tsibirin Bonny da ke kudancin Birnin Fatakwal.

Wata sanarwar da kakakin hedkwatar rundunar sojojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet ya aikewa sashin Hausa na Muryar Amurka, ta ce an hango jiragen ruwan uku sun huda bututun man inda suke satar danyen man a cikin teku. Nan take kuma a ka tura jiragen yakin su ka yi masu aman wuta inda su ka babbake su baki daya. Jiragen yakin sun kuma gano wasu haramtattun matatun mai da wuraren adana man sata da kuma tankokin dakon mai shake da man da aka tace ba bisa ka’ida ba a kudu maso gabashin garin Idama da ke a jihar ta Rivers, take kuma su ma aka far masu inda su ma aka kone su kurmus.Tuni kuma babban hafsan mayakan saman Najeriyar Sir Marshall Hassan Bala Abubakar, ya sake umartar baki dayan kwanandojin mayakan saman a kasar da su ci gaba da aiki tare da sauran jami’an tsaro don kawo karshen munanan ayuka. Allah Ya kara tona Asirin su amin

DAGA VOA HAUSA ✍️

Real Naseer Umar Alhassan 0015

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post