IYALAN MANZON ALLAH (S) NE SUKA FARA ZAMAN JUYAYIN ASHURA

 


MUNA DA RUWAYOYI DAGA A’IMMA (AS) A KAN JUYAYIN DA MUKE YI


Sannan kuma har wala yau, mu muna da ruwaya daga Imam Hasan al-Askari (AS), wanda yace, alamomin Mumini guda biyar ne, daga cikinsu sai ya ambaci Ziyaratul Arba’in. Yana daga cikinsu, sauran guda hudun ba sai mun kawo su ba tunda ba muhallinsu ba ne. Ziyaratul Arba’in na daga cikin alamomin Mumini, kuma wannan ziyarar Arba’in din yake nufi.

To, kaga kenan idan ma mutum ya ga muna abu, shi ya shafa bai gani ba, sai mu ce to in ka tambaye mu, mu muna da hujjarmu. Sannan kuma duk koyarwar A’imma dinmu, muna da har da Nassin Ziyarar Arba’in, sananne ne. To kaga kenan Tattakin da ake yi, a wurinmu ba kirkirarren abu ba ne, ba kuma mu ne muka ga ya kamata mu yi sai muka yi ba, dama zaunanne ne a koyarwar da Iyalan gidan Annabi (S) suka yi mana.

IYALAN MANZON ALLAH (S) NE SUKA FARA ZAMAN JUYAYIN ASHURA

To kuma haka ma zaman Aza na Shahadar Abi Abdullahi (AS), wanda shi ma Imam Zainul Abidin (AS) a lokacin da Yazidu yace ya roki komai zai masa. Bayan da duk abubuwa suka sukurkuce masa, Yazidu ko gari ya shiga sai ya ji ana la’antarsa, duk abin ya dame shi, sai ya zama yana tunanin su iyalan gidan Annabi su koma Madina. Har ma dai ya yi wasu abubuwa yana tunanin kamar ko ya fita kunya ne? Ya dauko Kwando shaqe da zinarori wai ya kawo musu.

                Mnnu//Ng0027

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post