BARAZANAR MUTUWA BA TA KARA MANA KOMAI SAI DAKEWA.



Mu a wurin mu kamar yadda Imam Husaini yake tare da Sahabbai wadanda yace bai san Sahabbai kamar Sahabban sa ba irin wadannan Hilal bin Nafi'i dinnan irin wadanda suka ce yi damu gabas ko yamma duk inda kai zamu bi muna tare da kai muna bisa basira kan cewa muna tare da gaskiya ne,


to irin wadannan ne muma zamu dake mu kasamce, wannan saura din Imam Husain abinda ta koyar kenan, nasara ta wata hanya da ba'a tsammani,


su suna tsammanin da karfin tsiya ne da haukataku da makami dashi ake nasara.


Billahi alaikum in mutum yana da hankali ya duba ya gani makami aka sa aka tara mutanen nan da kuke gani?,

fada akayi?

zagi akayi?

Hankali da ilimi, to amma kuma wannan me ya tattara wannan?

Jinin Imam Husain da jinainan Iyalan Gidan sa da Sahabban sa shi ya tattara mu tare, so yanzu sai ana mana barazanar za'a shekar da jinin mu,


BILLAHI ALAIKUM WANDA YAKE GANIN SHI BA ZAI BADA JININ SA BA TO DAMA YA JA BAYA,


Saboda haka duk abinda zakuyi munfi..., in shawara zamu baku sai muce kar ku, kar kuyi, kar kuyi kuskuren daukan matakin karfi, shawara muka baku amma in kuka kuskure kukayi, to albishirin ku da hasarar duniya da lahira, albishirin ku zaku tambatsa al'amarin ta inda ba ku zato kuma wallahi tallahi sai kunyi da na sani.


Sheikh Ibraheem Zakzaky (H)

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post