Idan shimr Ibn ziljaushan (شمر بن ذي الجوشن) dan shi'a ne; saboda ya taba kasancewa tare da Imam Ali (AS) a Yakin siffin, kenan Ammar bin Yasir, Abdullahi Ibn Musa, Abu Musa Al-sha'ari... 'yan shi'a ne? hakan yana nufin cikin sahabbai a kwai 'yan shi'a? Kenan zancen dan saba'a ne ya kirkiri shi'a ne; karya neE???

 



IDAN SHIMR IBN ZIL JAUSHAN (شمر بن ذي الجوشن) DAN SHIA NE; SABODA YA TABA KASANCEWA TARE DA IMAM ALI(AS) A YAKIN SIFFIN, KENAN AMMAR IBN YASIR, ABDULLAH IBN ABBAS, ABU MUSA AL-ASH'ARI... 'YAN SHIA NE? HAKAN YA NUFIN CIKIN SAHABBAI AKWAI 'YAN SHIA? KENAN ZANCEN DAN SABA'A NE YA KIRKIRI SHIA; KARYA NE???


SHIMR IBN ZIL JAUSHAN (شمر بن ذي الجوشن) YARON UBAIDULLAH IBN ZIYAD NE; GWAMNAN YAZID IBN MU'AWIYA A KUFA (IRAQ). - INJI IBN KASIR, AZ-ZAHBI, IBN ASAKIR, IBN HAJAR AL-ASKALANI...


ANNABI MUHAMMAD(SAW) YA GAYAWA IMAM HUSAIN(AS); SHIMR IBN ZIL JAUSHAN NE ZAI KASHE SHI. - INJI IBN ASAKIR


IMAM HUSAIN(AS) YA TABBATAR DA SHIMR IBN ZIL JAUSHAN DAN WUTA NE, HASALIMA SHIMR DA KANSA YA TABBATAR DA SHI DAN WUTA NE. - INJI AT-TABARI...


Ibn Asakir ya riwaito Al-Khalifa ya na cewa:


Shimr Ibn Zil Jaushan ne ya jagoranci kashe Husain(as). Umar Ibn Sa'ad shine kwamandan rundunar da ta [kashe Husain(as)]:


قال بن عساكر:


أخبرنا أبو غالب الماوردي أنبأ محمد بن علي أنبأ أحمد بن إسحاق ثنا أحمد بن عمران ثنا موسى بن زكريا ثنا الخليفة العصفري قال الذي ولي قتل الحسين شمر بن ذي الجوشن وأمير الجيش عمر بن سعد...


- تاريخ مدينة دمشق : ابن عساكر، ج ٢٣، ص ١٩٠، ترجمة ٢٧٦٢. تاريخ الوفاة : ٥٧١. تحقيق : علي شيري. تاريخ النشر : ١٤١٥. دار الفكر للطباعة والنشر والتوزيع.


Ibn Kasir ya tabbatar da Shimr Ibn Zil Jaushan babban yaron Ubaidullah Ibn Ziyad ne. Ubaidullah [Gwamnan Yazid a Kufa (Iraq] shine ya ba Shimr umarnin kashe Husain(as):


Ibn Kasir ya riwaito Uqba Ibn Sam'an ya na cewa; ina tare da Husain(as) tun daga Makkah; har aka kashe shi, tabbas Ubaidullah Ibn Ziyad ne ya tura Shimr Ibn Zil Jaushan akan ya kashe Husain(as), Ubaidullah ya ce da Shimr ka je ka ce da Husain(as) da Magoyabansa su yiwa (Yazid) mubaya'a, in sun ki, ka ce; Umar Ibn Sa'ad ya kashe su, idan ya ki, ka kashe, sannan ka jagoranci rundunar [ku kashe Husain(as)];


قال بن كثير:


روى أبو مخنف: حدثني عبد الرحمن بن جندب، عن عقبة بن سمعان. قال لقد صحبت الحسين من مكة إلى حين قتل ...إن عبيد الله بعث شمر بن ذي الجوشن فقال: اذهب فإن جاء الحسين وأصحابه على حكمي وإلا فمر عمر بن سعد أن يقاتلهم، فإن تباطأ عن ذلك فاضرب عنقه ثم أنت الأمير على الناس...


- البداية والنهاية : ابن كثير، ج ٨، ص ١٧٩ - ١٩٠. تاريخ الوفاة : ٧٧٤. تحقيق : تحقيق وتدقيق وتعليق : علي شيري. الطبعة : الأولى. تاريخ النشر : ١٤٠٨ - ١٩٨٨ م. دار احياء التراث العربي.


Daga cikin dalilan da ke alamta umarni ne aka bawa su Shimr Ibn Zil Jaushan akan kashe Husain(as), shi kansa Shimr ya tabbatar da hakan; kamar yanda aka riwaito daga bakinsa:


Az-Zahbi, Ibn Hajar Al-Askalani, Ibn Asakir... sun riwaito Abu Is'haq ya na cewa; Shimr Ibn Zil Jaushan ya ba Sallah, wasu lokuta ya kan zo Masallacin bayan an idar da Sallah ya yi ta sa, bayan ya idar ya kan yi addu'a, ya ce; ya Allah(swt) ka gafartamin, kasan ni babba ne, kar ka barni cikin tababbu. Sai na ce da shi; gaskiya fa ka tafka kuskure da ka kashe dan 'yar Annabi(saw)! Sai ya ce; ka bari kawai Abu Is-haq, da ba mu kashe Husain(as) ba; da sai mun fi jakuna walakanta.


Ibn Hajar Al-Askalani ya na cewa; wannan uzurin banza ne Shimr ya ke, tunda ana yiwa shugaba da'a ne a abinda ya ke daidai, [doriya akan walakantar Duniya da ya gujewa; ya yi ta, sannan ya garzaya cikin wulakanta madauwamiyya (Wata)]:


أخبرنا أبو بكر محمد بن عبد الباقي أنبأ الحسن بن علي أنبأ أبو عمر بن حيوية أنبأ أحمد بن معروف ثنا الحسين بن الفهم ثنا محمد بن سعد أنبأ منذر بن إسماعيل حدثني الهيثم بن الخطاب الهدي أنه سمع أبا إسحاق السبيعي يقول كان شمر بن ذي الجوشن يقول الضبابي لا يكاد أو لا يحضر الصلاة فيجئ بعد الصلاة فيصلي ثم يقول اللهم اغفر لي فإني كريم لم تلدني اللئام قال فقلت له إنك لسئ الرأي يسارع إلى قتل ابن بنت رسول الله(ص) فقال دعنا منك يا أبا إسحاق فلو كنا كما تقول وأصحابك كنا شرا من الحمراء السقات...


قال بن حجر العسقلاني: ان هذا لعذر قبيح فإنما الطاعة في المعروف.


- تاريخ مدينة دمشق : ابن عساكر، ج ٢٣، ص ١٨٩، ترجمة ٢٧٦٢. تاريخ الوفاة : ٥٧١. تحقيق : علي شيري. تاريخ النشر : ١٤١٥. دار الفكر للطباعة والنشر والتوزيع.


- لسان الميزان : ابن حجر، ج ٣، ص ١٥٢ - ١٥٣، ترجمة ٥٤٦. تاريخ الوفاة : ٨٥٢. الطبعة : الثانية. تاريخ النشر : ١٣٩٠ - ١٩٧١ م. بمطبعة مجلس دائرة المعارف النظامية الكائنة في الهند بمحروسة حيدر آباد الدكن عمرها الله إلى أقصى الزمن سنة (١٣٣٠) هجرية.


- ميزان الاعتدال : الذهبي، ج ٢، ص ٢٨٠، ترجمة ٣٧٤٢. تاريخ الوفاة : ٧٤٨. تحقيق : علي محمد البجاوي. الطبعة : الأولى. تاريخ النشر : ١٣٨٢ - ١٩٦٣ م. دار المعرفة للطباعة والنشر بيروت - لبنان.


- قتلة الإمام الحسين في ميزان أهل السنة : عابس الشاكري، ج ١ ص ٥٩ - ٦٢.


Allamah Al-Majalisi ya nakalto Imam Zainul-Abidin(as) ya na cewa: an ce da Ubaidullah; Umar Ibn Sa'ad fa ya ki ya kashe Husain(as); har ma ya kan je wajen sa su tattauna, sai Ubaidullah ya tura Shimr Ibn Zil Jaushan da runduna da sojoji 4,000, ya rubutawa Umar Ibn Sa'ad wasikar cewa; da zarar runduna ta zo, to ku gaggauta kashe Husain(as), kar ku bari ko ruwa ya sha:


أمالي الصدوق: محمد بن عمر البغدادي، الحافظ، عن الحسن بن عثمان بن زياد التستري من كتابه، عن إبراهيم بن عبيد الله بن موسى بن يونس ابن أبي إسحاق السبيعي قاضي بلخ قال: حدثتني مريسة بنت موسى بن يونس ابن أبي إسحاق وكانت عمتي قالت: حدثتني صفية بنت يونس بن أبي إسحاق الهمدانية وكانت عمتي قالت: حدثتني بهجة بنت الحارث بن عبد الله التغلبي، عن خالها عبد الله بن منصور، وكان رضيعا لبعض ولد زيد بن علي قال: سألت جعفر بن محمد بن علي ابن الحسين فقلت: حدثني عن مقتل ابن رسول الله(ص) فقال: حدثني أبي عن أبيه(ع) قال: ... فبلغ عبيد الله بن زياد أن عمر بن سعد يسامر الحسين(ع) ويحدثه، ويكره قتاله، فوجه إليه شمر بن ذي الجوشن في أربعة آلاف فارس، وكتب إلى عمر بن سعد إذا أتاك كتابي هذا فلا تمهلن الحسين بن علي وخذ بكظمه، وحل بين الماء وبينه...


- بحار الأنوار : العلامة المجلسي، ج ٤٤، ص ٣١٠ - ٣١٥. تاريخ الوفاة : ١١١١. تحقيق : محمد الباقر البهبودي. الطبعة : الثانية المصححة. تاريخ النشر : ١٤٠٣ - ١٩٨٣ م. مؤسسة الوفاء، بيروت لبنان.


Ibn Asakir, Az-Zahbi... sun tabbatar Shimr Ibn Zil Jaushan bai tsaya kan kashe Imam Husain(as) kai dai ba; hasalima shine ya jagoranci kai Iyala [da kan Husain(as)] zuwaga Yazid Ibn Mu'awiya:


قال بن عساكر:


شمر بن ذي الجوشن ... ووفد على يزيد بن معاوية مع أهل بيت الحسين...


- تاريخ مدينة دمشق : ابن عساكر، ج ٢٣، ص ١٨٦، ترجمة ٢٧٦٢. تاريخ الوفاة : ٥٧١. تحقيق : علي شيري. تاريخ النشر : ١٤١٥. دار الفكر للطباعة والنشر والتوزيع.


- ميزان الاعتدال : الذهبي، ج ٢، ص ٢٨٠، ترجمة ٣٧٤٢. تاريخ الوفاة : ٧٤٨. تحقيق : علي محمد البجاوي. الطبعة : الأولى. تاريخ النشر : ١٣٨٢ - ١٩٦٣ م. دار المعرفة للطباعة والنشر بيروت - لبنان.


Idan ba Yazid Ibn Mu'awiya ne ya sa aka kashe Husain(as) ba; me ya sa za'a kai masa Iyalai da kan Imam Husain(as)???


Ayatullah Al-Milani ya na cewa; tun kafin (waki'ar Ashura), Shimr Ibn Zil Jaushan babban yaron Ubaidullah Ibn Ziyad ne, abinda ke alamta hakan Shimr ya na cikin wadanda Ubaidullah ya tura Kufa (iraq) akan su hana mutane zuwa wajen Muslim Ibn Aqil(r), sannan su tsorata mutanen Kufa (Iraq) akan hadarin da ke cikin sabawa Sarki, da gagarumar ukubar da aka tanada akan hakan:


قال آية الله السيد علي الحسيني الميلاني:


وكان من أوّل أمره من أصحاب ابن زياد، وكان ممّن أمره بأنْ يخذّلوا الناس عن مسلم، ويخوّفوهم الحرب، ويحذّروهم عقوبة السلطان


- من هم قتلة الحسين(ع) : آية الله السيد علي الحسيني الميلاني، ص ٣٦٥.


Allamah Al-Majalisi ya nakalto riwayoyin da ke tabbatar da tun kafin (waki'ar Ashura), Shimr Ibn Zil Jaushan babban yaron Ubaidullah Ibn Ziyad ne, abinda ke alamta hakan Shimr ya na cikin wadanda Ubaidullah ya tura Kufa (iraq) akan su hana mutane zuwa wajen Muslim Ibn Aqil(r), sannan su tsorata mutanen Kufa (Iraq) akan hadarin da ke cikin sabawa Sarki, da gagaruwar ukubar da aka tanada akan hakan:


و قد نقل العلامة المجلسي:


فدعا ابن زياد كثير بن شهاب وأمره أن يخرج فيمن أطاعه في مذحج، فيسير في الكوفة ويخذل الناس عن ابن عقيل، ويخوفهم الحرب، ويحذرهم عقوبة السلطان وأمر محمد بن الأشعث أن يخرج فيمن أطاعه من كندة وحضرموت، فيرفع راية أمان لمن جاء من الناس، وقال مثل ذلك للقعقاع الذهلي وشبث بن ربعي التميمي وحجار بن أبجر السلمي وشمر بن ذي الجوشن العامري، وحبس باقي وجوه الناس عنده استيحاشا إليهم لقلة عدد من معه من الناس.


- بحار الأنوار : العلامة المجلسي، ج ٤٤، ص ٣٤٩. تاريخ الوفاة : ١١١١. تحقيق : محمد الباقر البهبودي. الطبعة : الثانية المصححة. تاريخ النشر : ١٤٠٣ - ١٩٨٣ م. مؤسسة الوفاء، بيروت لبنان.


ANNABI MUHAMMAD(SAW) YA GAYAWA IMAM HUSAIN(AS); SHIMR IBN ZIL JAUSHAN NE ZAI KASHE SHI. - INJI IBN ASAKIR


Ibn Asakir ya riwaito Amr Ibn Hasan ya na cewa; mun kasance tare da Husain(as) a ranar Karbala, sai Imam Husain(as) ya hangi Shimr Ibn Zil Jaushan, sai ya ce; tabbas Annabi(saw) ya yi gaskiya, daman ya ce; wata rana wani mai kama da Kare zai shekar da jin Ahlul-bayt(as), Shimr ya na da ciwon kuturta (ya yi kama da kare):


أنبأنا أبو محمد هبة الله بن أحمد بن طاوس أنبأ أبو الغنائم بن أبي عثمان أنبأ محمد بن أحمد بن محمد بن رزقويه أنبأ أبو بكر محمد بن عمر بن محمد بن الجعابي حدثني أبو بكر أحمد بن عبد العزيز ثنا عمر بن شبة ثنا أبو أحمد حدثني عمي فضيل بن الزبير عن عبد الرحيم بن ميمون عن محمد بن عمرو بن حسن قال كنا مع الحسين(ر) بنهري كربلاء فنظر إلى شمر بن ذي الجوشن فقال صدق الله ورسوله قال رسول الله(ص) كأني أنظر إلى كلب أبقع يلغ في دماء أهل بيتي فكان شمر أبرص...


- تاريخ مدينة دمشق : ابن عساكر، ج ٢٣، ص ١٩٠، ترجمة ٢٧٦٢. تاريخ الوفاة : ٥٧١. تحقيق : علي شيري. تاريخ النشر : ١٤١٥. دار الفكر للطباعة والنشر والتوزيع.


Ash-Shahrudi ya nakalto; Shimr Ibn Zil Jaushan dan Zina ne, tabbas ya halarci yakin Siffin cikin rundunar Imam Ali(as), sai dai kowa ya san aika-aikar da ya yi a Karbala. An riwaito wata rana Uwar Shimr ta yi tafiya, akan hanya kishin ruwa ya kamata, ta nemi wani makiya ya taimaka mata da ruwa; ya ce sai in ta yarda ya yi lalata da ita, bayan ya yi lalata da ita ne ta dauki cikin Shimr, wannan ne ya sa ranar Waki'ar Ashura; Imam Husain(as) ya kira Shimr da dan Makiyayi:


قال الشيخ علي النمازي الشاهرودي:


شمر بن ذي الجوشن: تولد من الزنا. وكان يوم صفين في جيش أمير المؤمنين(ع). و قضاياه في كربلاء معروفة. وعن كتاب المثالب لهشام بن محمد الكليني: إن امرأة ذي الجوشن خرجت من جبانة السبيع إلى جبانة كندة، فعطشت في طريق ولاقت راعيا يرعى الغنم فطلبت منه الماء فأبى أن يعطيها إلا بالإصابة منها. فمكنته فواقعها الراعي فحملت بشمر.... قول مولانا الحسين(ع) لشمر يوم عاشوراء: يا بن راعية المعزى، أنت أولى بها صليا.


- مستدركات علم رجال الحديث : الشيخ علي النمازي الشاهرودي، ج ٤، ص ٢٢٠، ترجمة ٦٨٩٩. تاريخ الوفاة : ١٤٠٥. الطبعة : الأولى. تاريخ النشر : محرم الحرام ١٤١٤. المطبعة: حيدرى - تهران.


IMAM HUSAIN(AS) YA TABBATAR SHIMR IBN ZIL JAUSHAN DAN WUTA NE, HASALIMA SHIMR DA KANSA YA TABBATAR DA SHI DAN WUTA NE. - INJI AT-TABARI...


At-tabari, Al-mufid(a)... sun riwaito; Imam Husain(as) ranar Ashura; ya kira Shimr da dan makiyayi, dan wuta, doriya akan Shimr da kansa ya tabbatar da shi dan wuta ne:


فحدثني عبد الله بن عاصم قال حدثني الضحاك المشرقي قال لما أقبلوا نحونا فنظروا إلى النار تضطرم في الحطب والقصب الذي كنا ألهبنا فيه النار من ورائنا لئلا يأتونا من خلفنا إذ أقبل إلينا منهم رجل يركض على فرس كامل الأداة فلم يكلمنا حتى مر على أبياتنا فنظر إلى أبياتنا فإذا هو لا يرى إلا حطبا تلتهب النار فيه فرجع راجعا فنادى بأعلى صوته يا حسين استعجلت النار في الدنيا قبل يوم القيامة فقال الحسين من هذا كأنه شمر بن ذي الجوشن فقالوا نعم أصلحك الله هو هو فقال يا ابن راعية المعزى أنت أولى بها صليا.


- تاريخ الطبري : الطبري، ج ٤، ص ٢٢١ - ٢٢٢. تاريخ الوفاة : ٣١٠. تحقيق : مراجعة وتصحيح وضبط : نخبة من العلماء الأجلاء. منشورات مؤسسته الأعلمي للمطبوعات، بيروت - لبنان.


- مقتل الحسين(ع) : أبو مخنف الأزدي، ص ١١٦. تاريخ الوفاة : ١٥٧. تحقيق : تعليق : حسين الغفاري.


 - الإرشاد : الشيخ المفيد، ج ٢، ص ٩٦.تاريخ الوفاة : ٤١٣. تحقيق : مؤسسة آل البيت(ع) لتحقيق التراث. الطبعة : الثانية. تاريخ النشر : ١٤١٤ - ١٩٩٣ م. دار المفيد طباعة - نشر - توزيع.


IDAN SHIMR IBN ZIL JAUSHAN (شمر بن ذي الجوشن) DAN SHIA NE; SABODA YA TABA KASANCEWA TARE DA IMAM ALI(AS) A YAKIN SIFFIN, KENAN AMMAR IBN YASIR, ABDULLAH IBN ABBAS, ABU MUSA AL-ASH'ARI... 'YAN SHIA NE? HAKAN YA NUF kiIN CIKIN SAHABBAI AKWAI 'YAN SHIA? KENAN ZANCEN DAN SABA'A NE YA KIRKIRI SHIA; KARYA NE???


KASANCEWA SHIMR IBN ZIL JAUSHAN CIKIN RUNDANAR IMAM ALI(AS) A YAKIN SIFFIN HAKAN BA YA ALAMTA SHIMR DAN SHIA NE, TUNDA CIKIN WADANDA SU KA TAIMAKAWA IMAM ALI(AS) A YAKIN SIFFIN HAR DA KWAWARIJ; WANDANDA DAGA BISANI SU KA YAKI IMAM ALI(AS) A NAHRAWAN, DORIYA AKAN IMAM ALI(AS) A LOKACIN KHALIFANCIN; DUKAN MUSULMAI (SHIA DA WANINSU) SU NA TARE DA SHI (IN KA CIRE 'YAN TAWAYE), HASALIMA HAR KIRISTOCI DA YAHUDAWAN DA SU KE KARKASHIN DAULAR MUSULUNCI; SU NA TARE DA IMAM ALI(AS).IDAN DUK WADANDA SU KAIMAKAWA IMAM ALI(AS) A YAKIN SIFFIN; 'YAN SHIA NE, KENAN AMMAR IBN YASIR, IBN ABBAS, ABU MUSA AL-ASH'ARI... 'YAN SHIA NE? HAKAN YA NUFIN CIKIN SAHABBAI AKWAI 'YAN SHIA? KENAN ZANCEN DAN SA'ABA NE YA KIRKIRI; KARYA NE???


➖➖➖➖➖➖➖➖➖

Abdulrahman Murtala - abdulrahmanyj@gmai


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post