ZAZZAFAN RADDI:- Idan Babu Taimakon Manzon Allah (S) Har Uwarka Da Ubanka Babu Mai Shiga Aljannah...Inji Ado Isah Guda




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


RADDI GA IDRIS ABDUL-AZEEZ DUTSIN TANSHI BAUCHI 


A duk lokacin da jahili ya bude baki yayi magana babu abinda ke biyo bayanta sai qasqanci. Wani na ganin shi mai ilimi ne don ganin ya tara wawaye a gabansa yana karantar dasu tatsuniyoyi suna yi masa kabbara. 


Maganar Idris Abdul-Aziz dutsin tanshi Bauchi wacce yayi cewa ba ya neman taimakon Manzon Allah (S. A. W. W) tasa nayi wannan rubutu don yi masa nasiha da mabiyansa ta hanyar magana ta ilimi.


Duk da cewa na san shi jahili ba ya yarda da gazawarsa kuma ba ya karbar nasiha, amma zanyi wannan nasiha ta hanyar kawo masa abinda bai sani ba a Ilimance, idan akwai mai rabo cikin mabiyansa wani zai fahimta. 


Imam Ali (A. S) na cewa :


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


قال الإمام علي بن أبي طالب(ع):


" الْجَاهِلُ لَا يَعْرِفُ تَقْصِيرَهُ وَلَا يَقْبَلُ مِنَ النَّصِيحِ لَهُ."


" SHI JAHILI BA YA SANIN GAZAWARSA, KUMA BA YA KARBA DAGA MAI YIN NASIHA GARE SHI. "


المصدر : غرر الحكم ودرر الكلم


Wannan dalili yasa bayan maganar da Idris dutsen tanshi yayi sai ya qara fitowa ya jaddada maganar tasa don ya ji martanin da yake samu daga masana masoyan Manzon Allah (S. A. W. W). 


Abinda ba ka sani ba shine, ko ka qi neman taimakon Manzon Allah (S. A. W. W) anan duniya saboda ka raina shi, to, dole ka nemi taimakonsa a ranar alqiyama, in ba haka ba har Uwarka da Ubanka babu mai shiga Aljannah, domin ayyukan mutum ba sa kai shi Aljannah sai da lullubewar rahmar Ubangiji. Shi kuma Ubangiji ba zai yi maka rahma ba har sai ta hanyar ceton Manzon Allah (S. A. W. W) a ranar da babu mai ceto in ba shi ba. 


Wannan rana ita ce ranar da Allah (T) ke cewa :


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


  " يَا أَيُّهَا النَّاسُ اتَّقُوا رَبَّكُمْ إِنَّ زَلْزَلَةَ السَّاعَةِ شَيْءٌ عَظِيمٌ (1) 


" YAA KU MUTANE  ! KUJI TSORON UBANGIJINKU, LALLE GIRGIZAR QASA RANAR TASHIN ALQIYAMA WANI ABU NE MAI GIRMA. "



" يَوْمَ تَرَوْنَهَا تَذْهَلُ كُلُّ مُرْضِعَةٍ عَمَّا أَرْضَعَتْ وَتَضَعُ كُلُّ ذَاتِ حَمْلٍ حَمْلَهَا وَتَرَى النَّاسَ سُكَارَى وَمَا هُمْ بِسُكَارَى وَلَكِنَّ عَذَابَ اللَّهِ شَدِيدٌ." (2)


" RANAR DA KAKE GANINTA KOWACCE MAI SHAYARWA ZA TAYI JIFA DA ABINDA TAKE SHAYARWA, KUMA MA'ABOCIYAR CIKI TA HAIFAR DA (abinda ke) CIKINTA, KUMA KUGA MUTANE CIKIN MAYE ALHALI BA MAYE SUKE YI BA, SAI DAI AZABAR ALLAH MAI TSANANI. "


(Suratul-Hajj, aya ta 1-2)


To, idan kai jahili ne wanda bai san ana neman taimakon Manzon Allah (S. A. W. W) sai ka biyo mu cikin wannan riwaya wacce muka cirota daga Sunan na Tirmidhi kamar haka :


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


«2621» أَخْبَرَنَا سُوَيْدُ بْنُ نَصْرٍ أَخْبَرَنَا عَبْدُ اللَّهِ بْنُ الْمُبَارَكِ أَخْبَرَنَا أَبُو حَيَّانَ التَّيْمِيُّ عَنْ أَبِي زُرْعَةَ بْنِ عَمْرِو بْنِ جَرِيرٍ عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ قَالَ أُتِيَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِلَحْمٍ فَرُفِعَ إِلَيْهِ الذِّرَاعُ فَأَكَلَهُ وَكَانَتْ تُعْجِبُهُ فَنَهَسَ مِنْهَا نَهْسَةً ثُمَّ قَالَ: ((أَنَا سَيِّدُ النَّاسِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ هَلْ تَدْرُونَ لِمَ ذَاكَ يَجْمَعُ اللَّهُ النَّاسَ الأَوَّلِينَ وَالآخِرِينَ فِي صَعِيدٍ وَاحِدٍ فَيُسْمِعُهُمُ الدَّاعِي وَيَنْفُذُهُمُ الْبَصَرُ وَتَدْنُو الشَّمْسُ مِنْهُمْ فَيَبْلُغُ النَّاسُ مِنَ الْغَمِّ وَالْكَرْبِ مَا لاَ يُطِيقُونَ وَلاَ يَحْتَمِلُونَ فَيَقُولُ النَّاسُ بَعْضُهُمْ لِبَعْضٍ أَلاَ تَرَوْنَ مَا قَدْ بَلَغَكُمْ أَلاَ تَنْظُرُونَ مَنْ يَشْفَعُ لَكُمْ إِلَى رَبِّكُمْ فَيَقُولُ النَّاسُ بَعْضُهُمْ لِبَعْضٍ عَلَيْكُمْ بِآدَمَ. فَيَأْتُونَ آدَمَ فَيَقُولُونَ أَنْتَ أَبُو الْبَشَرِ خَلَقَكَ اللَّهُ بِيَدِهِ وَنَفَخَ فِيكَ مِنْ رُوحِهِ وَأَمَرَ الْمَلاَئِكَةَ فَسَجَدُوا لَكَ اشْفَعْ لَنَا إِلَى رَبِّكَ أَلاَ تَرَى مَا نَحْنُ فِيهِ أَلاَ تَرَى مَا قَدْ بَلَغَنَا فَيَقُولُ لَهُمْ آدَمُ إِنَّ رَبِّي قَدْ غَضِبَ الْيَوْمَ غَضَبًا لَمْ يَغْضَبْ قَبْلَهُ مِثْلَهُ وَلَنْ يَغْضَبَ بَعْدَهُ مِثْلَهُ وَإِنَّهُ قَدْ نَهَانِي عَنِ الشَّجَرَةِ فَعَصَيْتُ نَفْسِي نَفْسِي نَفْسِي اذْهَبُوا إِلَى غَيْرِي اذْهَبُوا إِلَى نُوحٍ.

فَيَأْتُونَ نُوحًا فَيَقُولُونَ يَا نُوحُ أَنْتَ أَوَّلُ الرُّسُلِ إِلَى أَهْلِ الأَرْضِ وَقَدْ سَمَّاكَ اللَّهُ عَبْدًا شَكُورًا اشْفَعْ لَنَا إِلَى رَبِّكَ أَلاَ تَرَى مَا نَحْنُ فِيهِ أَلاَ تَرَى مَا قَدْ بَلَغَنَا فَيَقُولُ لَهُمْ نُوحٌ إِنَّ رَبِّي قَدْ غَضِبَ الْيَوْمَ غَضَبًا لَمْ يَغْضَبْ قَبْلَهُ مِثْلَهُ وَلَنْ يَغْضَبَ بَعْدَهُ مِثْلَهُ وَإِنَّهُ قَدْ كَانَ لِي دَعْوَةٌ دَعَوْتُهَا عَلَى قَوْمِي نَفْسِي نَفْسِي نَفْسِي اذْهَبُوا إِلَى غَيْرِي اذْهَبُوا إِلَى إِبْرَاهِيمَ. فَيَأْتُونَ إِبْرَاهِيمَ فَيَقُولُونَ يَا إِبْرَاهِيمُ أَنْتَ نَبِيُّ اللَّهِ وَخَلِيلُهُ مِنْ أَهْلِ الأَرْضِ اشْفَعْ لَنَا إِلَى رَبِّكَ أَلاَ تَرَى مَا نَحْنُ فِيهِ فَيَقُولُ إِنَّ رَبِّي قَدْ غَضِبَ الْيَوْمَ غَضَبًا لَمْ يَغْضَبْ قَبْلَهُ مِثْلَهُ وَلَنْ يَغْضَبَ بَعْدَهُ مِثْلَهُ وَإِنِّي قَدْ كَذَبْتُ ثَلاَثَ كَذَبَاتٍ فَذَكَرَهُنَّ أَبُو حَيَّانَ فِي الْحَدِيثِ نَفْسِي نَفْسِي نَفْسِي اذْهَبُوا إِلَى غَيْرِي اذْهَبُوا إِلَى مُوسَى. فَيَأْتُونَ مُوسَى فَيَقُولُونَ يَا مُوسَى أَنْتَ رَسُولُ اللَّهِ فَضَّلَكَ اللَّهُ بِرِسَالَتِهِ وَبِكَلاَمِهِ عَلَى الْبَشَرِ اشْفَعْ لَنَا إِلَى رَبِّكَ أَلاَ تَرَى مَا نَحْنُ فِيهِ فَيَقُولُ إِنَّ رَبِّي قَدْ غَضِبَ الْيَوْمَ غَضَبًا لَمْ يَغْضَبْ قَبْلَهُ مِثْلَهُ وَلَنْ يَغْضَبَ بَعْدَهُ مِثْلَهُ وَإِنِّي قَدْ قَتَلْتُ نَفْسًا لَمْ أُومَرْ بِقَتْلِهَا نَفْسِي نَفْسِي نَفْسِي اذْهَبُوا إِلَى غَيْرِي اذْهَبُوا إِلَى عِيسَى. فَيَأْتُونَ عِيسَى فَيَقُولُونَ يَا عِيسَى أَنْتَ رَسُولُ اللَّهِ وَكَلِمَتُهُ أَلْقَاهَا إِلَى مَرْيَمَ وَرُوحٌ مِنْهُ وَكَلَّمْتَ النَّاسَ فِي الْمَهْدِ اشْفَعْ لَنَا إِلَى رَبِّكَ أَلاَ تَرَى مَا نَحْنُ فِيهِ فَيَقُولُ عِيسَى إِنَّ رَبِّي قَدْ غَضِبَ الْيَوْمَ غَضَبًا لَمْ يَغْضَبْ قَبْلَهُ مِثْلَهُ وَلَنْ يَغْضَبَ بَعْدَهُ مِثْلَهُ وَلَمْ يَذْكُرْ ذَنْبًا نَفْسِي نَفْسِي نَفْسِي اذْهَبُوا إِلَى غَيْرِي اذْهَبُوا إِلَى مُحَمَّدٍ. قَالَ فَيَأْتُونَ مُحَمَّدًا فَيَقُولُونَ يَا مُحَمَّدُ أَنْتَ رَسُولُ اللَّهِ وَخَاتَمُ الأَنْبِيَاءِ وَقَدْ غُفِرَ لَكَ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِكَ وَمَا تَأَخَّرَ اشْفَعْ لَنَا إِلَى رَبِّكَ أَلاَ تَرَى مَا نَحْنُ فِيهِ فَأَنْطَلِقُ فَآتِي تَحْتَ الْعَرْشِ فَأَخِرُّ سَاجِدًا لِرَبِّي ثُمَّ يَفْتَحُ اللَّهُ عَلَيَّ مِنْ مَحَامِدِهِ وَحُسْنِ الثَّنَاءِ عَلَيْهِ شَيْئًا لَمْ يَفْتَحْهُ عَلَى أَحَدٍ قَبْلِي ثُمَّ يُقَالُ يَا مُحَمَّدُ ارْفَعْ رَأْسَكَ سَلْ تُعْطَهُ وَاشْفَعْ تُشَفَّعْ. فَأَرْفَعُ رَأْسِي فَأَقُولُ يَا رَبِّ أُمَّتِي يَا رَبِّ أُمَّتِي يَا رَبِّ أُمَّتِي. فَيَقُولُ يَا مُحَمَّدُ أَدْخِلْ مِنْ أُمَّتِكَ مَنْ لاَ حِسَابَ عَلَيْهِ مِنَ الْبَابِ الأَيْمَنِ مِنْ أَبْوَابِ الْجَنَّةِ وَهُمْ شُرَكَاءُ النَّاسِ فِيمَا سِوَى ذَلِكَ مِنَ الأَبْوَابِ ثُمَّ قَالَ وَالَّذِي نَفْسِي بِيَدِهِ إِنَّ مَا بَيْنَ الْمِصْرَاعَيْنِ مِنْ مَصَارِيعِ الْجَنَّةِ كَمَا بَيْنَ مَكَّةَ وَهَجَرَ وَكَمَا بَيْنَ مَكَّةَ وَبُصْرَى)). 


وَفِي الْبَابِ عَنْ أَبِي بَكْرٍ الصِّدِّيقِ وَأَنَسٍ وَعُقْبَةَ بْنِ عَامِرٍ وَأَبِي سَعِيدٍ.قَالَ أَبُو عِيسَى: هَذَا حَدِيثٌ حَسَنٌ صَحِيحٌ. وَأَبُو حَيَّانَ التَّيْمِيُّ اسْمُهُ يَحْيَى بْنُ سَعِيدِ بْنِ حَيَّانَ كُوفِيٌّ وَهُوَ ثِقَةٌ وَأَبُو زُرْعَةَ بْنُ عَمْرِو بْنِ جَرِيرٍ اسْمُهُ هَرِمٌ.


Tirmidhi yace, Suwaidu Bn Nasrin ya bamu, Abdullahi Bn Mubaraki ya bamu labari, Abu Hayyan Al-Taimiy ya bamu labari daga baban Zur'ata Bn Amruu Bn Jareer, daga Abu Hurairata yace :

Manzon Allah (S. A. W. W) ya zo da Nama, sai Zuraa'a ya miqa masa, sai yaci yana mai mamaki, sai wani saura ya saura daga gare shi, sa'an nan yace : 


" NINE SHUGABAN MUTANE RANAR ALQIYAMA. SHIN, KUN SAN DALILIN DA YASA ALLAH ZAI MUTANE TUN DAGA NA FARKO HAR NA QARSHE A GURI GUDA (1) KUMA MAI KIRA YA JIYAR DASU, IDANUWA SU FISGE SU KUMA A KUSANTO DA RANA ☀ KUSA DASU, KUMA MUTANE SU KAI MATUQA DAGA DAMUWA DA BAQIN CIKI, BASU DA WANI IKO KUMA BA ZA SU IYA 'DAUKAR (wannan tashin hankali da damuwa ba)  ? KUMA SASHEN MUTANE YA FADAWA SASHE : " Shin, ba ku ga abinda ya same ku ba  ? Shin, ba za ku nemi wanda zai nema muku ceto wajen Ubangujinku ba? "


Sai sashen mutane su cewa sashe : " Ku tafi wajen Adamu  ." Sai su jewa Adamu suce :


" Kaine baban 'yan Adam, Allah ya halicceka da hannunSa kuma ya hura maka ruhinSa, kuma ya umarci Mala'iku da suyi maka Sujadah. Ka cecemu wajen Ubangijinka. Ko ba ka ganin halin da muke ciki  ? Shin, ko ba kaga abinda ya same mu (na tashin hankali) ba? " Sai Adamu yace musu :


" LALLE UBANGIJINA YAYI FUSHI A YAU IRIN FUSHIN DA BAI TABA YIN FUSHI IRINSA, KUMA BA ZAI TABA YIN FUSHI KAMARSA YA BAYANSA BA. KUMA LALLE NI YA HANENI GAME DA CIN ('ya'yan wata) BISHIYA, SAI NA SABA. NIMA TA KAINA TA KAINA TA KAINA NAKE YI  ! KU TAFI ZUWA GA WANINA, KU TAFI ZUWA GA NUHU  ."


Sai su jewa Nuhu suce :


" Yaa Nuhu  ! Kaine farkon Manzanni zuwa ga mutanen doron qasa, kuma haqiqa Allah ya ambace ka da : " BAWA MAI YAWAN GODIYA  ." ka nema mana ceto wajen Ubangijinka. Ko ba ka ganin halin da muke ciki, ko ba kaga abinda ya same mu ba  ?" Sai Nuhu yace musu :


" LALLE UBANGIJINA YAYI FUSHI YAU FUSHIN DA BAI TABA YIN IRINSA BA, KUMA BA ZAIYI FUSHI MISALINSA A BAYANSA BA. HAQIQA NI INA DA WATA ADDU'AH WACCE NA YIWA JAMA'ATA (na neman halakar dasu). TA KAINA NAKE TA KAINA NAKE TA KAINA NAKE. KU TAFI ZUWA GA WANINA, KU TAFI ZUWA GA IBRAHIM. "

Sai su jewa Ibrahim suce :


" Yaa Ibrahim  ! aine Annabin Allah kuma kaine badadaninsa daga mutanen doron qasa, ka nema mana ceto zuwa wajen Ubangijinka. Shin, ba kaga halin da muke ciki ba ?" Sai yace :


" LALLE UBANGIJINA YAYI FUSHI YAU FUSHIN DA BAI TABA YIN MISALINSA KAFINSA, KUMA BA ZAIYI MISALINSA BAYANSA BA. LALLE NI NA TABA YIN QARYA SAU UKU. " Abu Hayyan ya ambace su cikin hadisi. NIMA TA KAINA NAKE TA KAINA NAKE TA KAINA NAKE. KU TAFI ZUWA GA WANINA, KU TAFI ZUWA GA MUSA. "


Sai su jewa Musa suce masa :


" Yaa Musa  ! Kaine Manzon Allah wanda Allah ya fifita ka da saqonSa da kuma maganarSa akan 'ya'yan Adam. Ka nema mana ceton Ubangijinka. Ba ka ganin halin da muke ciki, ba kaga abinda ya same mu ba  ?" Sai yace :


" LALLE UBANGIJINA YAYI FUSHI A YAU FUSHIN DA BAI TABA YIN IRINSA BA KUMA BA ZAIYI IRINSA BA A BAYA. LALLE NI NA KASHE RAI (Bakibde) WACCE BA A UMARCENI DANA KASHETA BA. TA KAINA NAKE TA KAINA NAKE TA KAINA NAKE. KU TAFI ZUWA WAJEN WANINA, KU TAFI ZUWA GA ISAH. "


Sai su tafi zuwa ga Isah suce :


" Yaa Isah  ! Kai Manzon Allah ne kuma kalma daga gare Shi, kuma ka yi magana da mutane tun kana shimfidar goyo. Ka nema mana ceto zuwa ga Ubangijinka. Ko ba ka ganin halin da muke ciki, ko ba kaga abinda ya same mu ba  ?" Sai Isah yace :


" LALLE UBANGIJINA YAYI FUSHI YAU FUSHIN DA BAI TABA YIN IRINSA BA KUMA BA ZAIYI KAMARSA A BAYANSA BA. " Sai dai shi (Isah) bai fadi kaifinsa ba (tunda ba shi dashi, sai dai yace). TA KAINA NAKE TA KAINA NAKE TA KAINA NAKE. KU TAFI ZUWA GA WANINA, KU TAFI ZUWA GA MUHAMMAD. "


Yace, sai su jewa Muhammad suce :


" Yaa Muhammad  ! Kai Manzon Allah ne kuma cikamakin Annabawa, kuma haqiqa an gafarta maka abinda abinda ya gabata na daga zunubanka dama wadanda aka jinkintar. Ka nema mana ceto zuwa ga Ubangijinka. Ko ba ka ganin halin da muke ciki  ? Ko ba kaga abinda ya same mu ba  ?"


" SAI NA TASHI NA TAFI QARQASHIN AL'ARSHI NA FADI INA MAI SUJADAH GA UBANGIJINA, SANNAN ALLAH YA BUDE MIN QOFOFIN GODIYANSA DA KUMA KYAWUN YABO GARE SHI WANDA BAI TABA BUDE SU GA WANI BA GABANINA. SA'ANNAN YACE : " YAA MUHAMMAD  ! KA 'DAGO KANKA (daga Sujadah) KA ROQI DUKKAN ABINDA KAKE SO ZAN BAKA, KA NEMI CETO ZAN BA KA CETON. "


" SAI NA 'DAGO KAINA NACE, YAA UBANGIJI  ! AL'UMMATA!  YAA UBANGIJI AL'UMMATA !! YAA UBANGIJI AL'UMMATA  !!!


SAI YACE : " YAA MUHAMMAD  ! KA SHIGAR DAGA CIKIN AL'UMMARKA WADANDA BABU HISABI A KANSU TA QOFAR DAMA DAGA QOFAR ALJANNAH, SUNE MUTANEN DA ZA SUYI TARAYYA CIKIN KOMA-BAYAN HAKA NA DAGA QOFOFI. "


Sa'annan yace : " NA RANTSE DA WANDA RAINA KE HANNUNSA, LALLE ABINDA KE TSAKANIN BIRANE NA DAGA BIRANEN ALJANNAH KAMAR ABINDA KE TSAKANIN MAKKAH DA HAJARA NE, KUMA KAMAR ABINDA KE TSAKANIN MAKKAH DA BUSRAH NE. "


A cikin Babin daga Abubakar Siddiq da Anas da Uqbata Bn Ameer da Abu Sa'eed. Abu Isah (Al-Turmidhi yace : Wannan Hadisi mai kyau ne kuma ingantacce. 


(SUNAN TIRMIDHI, KITABUN SIFFATIL-QIYAAMAH, BABUN MAA JAA'AH  FIS-SHAFAA'ATA, HADISI MAI LAMBA 2621).


Maganar da za mu qarqare da ita ita ce ayar nan da Allah (T) ke cewa :


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


{وَمَا أَرْسَلْنَا مِنْ رَسُولٍ إِلَّا لِيُطَاعَ بِإِذْنِ اللَّهِ وَلَوْ أَنَّهُمْ إِذْ ظَلَمُوا أَنْفُسَهُمْ جَاءُوكَ فَاسْتَغْفَرُوا اللَّهَ وَاسْتَغْفَرَ لَهُمُ الرَّسُولُ لَوَجَدُوا اللَّهَ تَوَّابًا رَحِيمًا (64)} ﴾ 


" KUMA BAMU AIKA DA WANI MANZO BA FACE DOMIN AYI MASA 'DA'A/BIYAYYA DA IZNIN ALLAH. DA DAI ACE A LOKACIN DA SUKA ZALUNCI KANSU SUN ZO  MAKA, SUN NEMI GAFARAR ALLAH KUMA MANZO YA NEMA MUSU GAFARA, TO, HAQIQA DA SUN SAMI ALLAH MAI KARBAR TUBA MAI JIN QAI. "


       (NISA'I, AYA TA 64)


Anan Allah ya kafa sharadi da cewa kuma Manzo ya nema musu gafara. Ashe kuwa in har sai Manzo ya nema maka gafara wajen Allah sannan ka same Shi mai karbar tubanka da yi maka rahma, to, ashe kuwa ya taimake ka. 


SABODA HAKA IDAN AKA CE BA KA BUQATAR TAIMAKON MANZON ALLAH HAR UWARKA DA UBANKA BABU MAI TAFIYA ALJANNAH DOMIN BABU WANDA AIKINSA ZAI KAI SHI. SANNAN KUMA RANAR ALQIYAMA BA KA ISA KAJE KAI-TSAYE ZUWA GA UBANGIJINKA BA DOLE SAI TA HANYAR MANZON ALLAH. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda. 


       (08137925034)


9th Afril, 2023/  18th Ramadan, 1444.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post