Shin Nawa ne Kudin Kofi Daya Na kiyayya. ?



Fassarar Abubakar Musa


Ban taba sanin yana da tsada haka ba. Ina son sanin nawa ne kudin KIYAYYA, don haka sai na yanke shawarar ziyartar shagon da ake saidawa. 


A matsayinsa na dan kasuwa mai neman kwastoma, mai saidawar sai ya rugo domin ya tambayi me nake so. Sai na ce masa ina son kofi daya ne kawai na kiyayya. Sai ya yi murmushi ya tambaya, ko zan iya saye?


"Nawa ne kofi daya?" Na tambaya "Hmmmmm!" Ya ja dogon lumfashi, sai ya ce:


👉🏻 Daga farko dai zai dauke farin cikin ka. 


👉🏻 Zai haifar maka da damuwa mara karewa. 


👉🏻 Zai zaizaye zuciyarka. 


👉🏻 Za ka kasance kana jin haushin wanda kake kiyayya da shi a duk lokacin da ka kalle shi. 


👉🏻 A duk lokacin da wasu suke taya shi murna, za ka rinka neman dalilin da zai sa a ce bai dace ba. 


👉🏻 Za ka kasance karfinka ya tafi kuma ka gaji da ganin mutumin. 


👉🏻 A duk lokacin da ya yi dariya, za ka yi kuka. 


👉🏻 A yayin da sauran mutane suka shagaltu da tsara yadda rayuwarsu za ta kasance, kai kuma ka damu da yadda za ka jawo shi kasa. 


👉🏻 Halaye masu kyau za su bar ka, za ka zamanto mazaunar shaidanu. 


👉🏻 Za ka fara samun matsaloli daban-daban na lafiya kamar hawan jini, ciwon siga, shanyewar barin jiki, kansa, ciwon hanta, ciwon koda da dai sauransu. In har ka sha  daga kofin kiyayya, tsangwama, kyama, rashin yafiya, yunkurin cutarwa, haushi, hassada da duk makamantanta. Babbar matsalar ma ita ce addu'o'i ko magunguna ba su cika yin taimako ba a irin wannan yanayi   saboda ka karya dokokin da suke sanannu shimfidaddu. 


👉🏻 Za ka mutu kafin lokacinka. 


Mai saidawar zai ci gaba da lissafo nawa kofin kiyyya yake, sai na tsayar da shi, domin jin irin tsadarsa. 


Sai na bar wajen domin na san ba zan iya saye ba. 

Ba zan biya hakan ba bayan na san zan iya SO cikin sauki kuma ba tare da tsada ba. 


Ya ku 'yan uwa, kada ku bari wani ya dauke farin cikinku, ya kuma sayar maku da kiyayya. 


Ku guji gulma, tsangwama, fushi da sauransu domin mafi yawanci abin da kuka ji ne dangane da wasu yake haifar da kiyayyar. 


Kada ku mutu kafin lokacinku!

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post